Sin Ta Kausasa Murya Wajen Yin Tir Da Matakin Da Amurka Ta Dauka A Venezuela
[ad_1]
Mataimakin wakilin Sin na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Sun Lei, ya yi tsokaci a taron gaggawa na kwamitin sulhun MDD, kan halin da ake ciki a kasar Venezuela, inda ya bayyana cewa, Sin ta yi matukar kaduwa, kuma ta kausasa murya wajen yin tir da haramtaccen matakin babakeren da Amurka ta dauka na kashin kanta.
Sun Lei ya bayyana cewa, Amurka ta sanya muradunta sama da tsarin kasa da kasa, ta kuma sanya matakan sojanta a gaban kokarin diflomasiya, wanda hakan ya yi barazana sosai ga zaman lafiya da tsaro a yankin Latin Amurka da Caribbean har ma da na kasa da kasa. Ya ce, ko kadan Sin ba ta amince da hakan ba, kuma al’ummar kasa da kasa gaba daya sun yi Allaha wadai, da nuna matukar damuwa tare da suka mai tsanani.
Sun Lei ya jaddada cewa, Sin ta gargadi Amurka da ta saurari muryoyin al’ummun kasa da kasa, kuma ta bi dokokin kasa da kasa, da manufa da ka’idojin yarjejeniyar MDD, ta daina keta ikon mallakar yankunan wasu kasashe, da daina tsoma hannu cikin harkokin gwamnatin Venezuela, da koma kan hanyar warware batun ta hanyar tattaunawa da shawarwari na siyasa. Har ila yau, kasar Sin na goyon bayan gwamnatin Venezuela, da al’ummarta wajen kare ikon tsaron yankunan kasar, da kuma hakkin su na doka, kana Sin tana fatan hadin gwiwa da kasashen yankin, da kuma al’ummar kasa da kasa wajen karfafa hadin kai, da kare adalci da gaskiya, domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Latin Amurka da Caribbean. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link