Yanzu zan yi barci ido rufe — Barau
[ad_1]
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Kano su ba da cikakken goyon baya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya sauya shekar gwamnan daga NNPP zuwa APC.
Barau ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Kano ranar Talata, inda ya ce Tinubu ya jaddada muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyya domin tabbatar da ingantacce mulki.
Sanatan ya ce dawowar gwamnan babbar nasara ce ga APC, musamman a jihar Kano wadda ke da muhimmanci a siyasar ƙasar. “Ranar farin ciki ce a gare ni, domin jam’iyyarmu ta samu gwamna mai ci,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne a mara wa Gwamna Abba baya, a daina rikici da takaddama, tare da ba shi damar gudanar da mulki ba tare da matsin lamba ba.
Barau ya bayyana cewa ya janye wasu daga cikin burinsa na siyasa domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.
Ya bayyan cewa lokaci ya yi na ’yan siyasa a Kano su jingine batun takara da burin mulki, su maida hankali kan goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf a jam’iyyar.
Barau ya kara da cewa shi ma ya janye nasa burin takara domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.
A cewarsa, idan aka hana gwamnan damar yin wa’adi na biyu, hakan zai iya kawo cikas ga ayyukan ci gaba da kuma lalata tafiyar mulki a Kano.

Sanatan ya tuna wasu lokuta da ya yi sadaukarwa a siyasa domin haɗin kan jam’iyya, ciki har da lokacin da ya janye takara a shugabancin Majalisar Dattawa da kuma a zaben gwamna a Kano.
Ya ce: “Na dade ina ganin sadaukarwa don al’umma shi ne mafi muhimmanci. Idan gwamnan tun farko yana cikin APC, da ba ma na magana kan takara. Yanzu da yake cikin jam’iyyarmu, dole mu mara masa cikakken baya.”
A cewarsa, gwamnan zai yi aiki cikin ’yanci wajen zaben kwamishinoni da sauran mukarrabai, ba tare da tsoma bakin shugabannin jam’iyya ba. “Za mu ba shi damar yin aikinsa yadda yake so, ba za mu takura masa ba,” in ji shi.
Barau ya danganta dawowar gwamnan zuwa APC da manufofin Renewed Hope Agenda na Tinubu, wanda ya ce ke jawo hankalin ’yan siyasa daga sauran jam’iyyu.
Haka kuma, ya sanar da sauya sunan ƙungiyar goyon bayansa daga Tinubu/Barau Organisation zuwa Tinubu, Abba, Barau Organisation, domin nuna sabon haɗin kai.
Sanatan ya jaddada cewa burinsa na tsawon shekaru a siyasa shi ne hidima ga al’umma, tare da tabbatar da cewa Kano da Najeriya sun ci gaba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link