Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?
[ad_1]
Duk da cewa kasar Sin tana fuskantar karin matsin lamba daga waje da kalubalen cikin gida tun daga farkon wannan shekara, tattalin arzikinta ya samu nasarori a cikin wannan mawuyacin hali. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, alkaluman yawan kudin da aka samu daga samar da kayayyaki da hidimomi a cikin kasa wato GDP a takaice, a cikin watanni 9 na farkon bana sun karu da 5.2%. Adadin da ya nuna wasu halaye na musamman na tattalin arzikin kasar.
Da farko, an tabbatar karfin tattalin arzikin kasar ta Sin. Watau har yanzu, saurin karuwar tattalin arzikin kasar yana kan gaba a cikin manyan kasashe da yankuna masu karfin tattalin arziki na duniya, kuma yana ci gaba da kasancewa a matsayin tushe mai karko na inganta karuwar tattalin arzikin duniya.
Baya ga haka, ya kara nuna alamar ci gaban tattalin arzikin kasar. Tun daga farkon wannan shekara, kasar Sin take kokarin raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ta hanya mai dacewa da yanayi, wanda hakan ya ba da sabon kuzari ga tattalin arzikinta, kuma ya hanzarta yunkurin yin kirkire-kirkire na duniya.
Har ma abun da ba kasafai ake gani ba, tattalin arzikin Sin yana cike da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai. Ba sabunta kayayyaki kirar kasar da kara musu inganci kadai aka samu ba, har ma abokan cinikin kasar a ketare suna ta kara yawa.
A jiya Litinin ne aka bude cikakken zama na 4 na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a nan Beijing, inda za a tattauna da kuma ba da shawarwari kan shirin shekaru biyar-biyar na 15 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin. Kasashen duniya na sa ran cewa, kasar Sin za ta ba da sababbin damammarkin neman samun ci gaba ga duniya, bisa ga tsayayyun manufofinta da ci gaba da bude kofarta ga duk duniya baki daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link