’Yan sanda sun kama amarya kan zargin kashe mijinta da guba a Jigawa
[ad_1]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, ta kama wata sabuwar amarya bisa zargin kashe mijinta har lahira ta hanyar zuba guba a abincinsa a garin Gauza da ke Ƙaramar Hukumar Jahun.
Rundunar ta bayyana cewa lamarin ya faru a ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 5 na yamma.
Bincike ya nuna cewa mamacin ya ci abincin da matarsa ta dafa masa, daga bisani ya kamu da rashin lafiya mai tsanani.
An garzaya da shi asibiti amma ya rasu a can.
’Yan sandan Jahun sun fara aikin bincike nan da nan, inda suka kama matar a matsayin wadda ake zargi da hannu a mutuwar angon.
A yayin bincike, matar ta amsa cewa ta sanya guba a abincin mijin nata.
Ta kuma bayyana yadda ta aika ƙawarta ta je ta sayo maga gubar da ta yi amfani da ita.
Matar ta shaida wa ’yan sanda cewa iyayenta ne suka tilasta mata auren mijin, wanda a cewarta hakan ne ya sa ta aikata laifin.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya umarci a miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) da ke Dutse, domin zurfafa bincike.
Za a gurfanar da matar a kotu bayan kammala bincike.
’Yan sandan sun shawarci al’umma da su kasance masu bin doka, da warware matsalolin iyali cikin lumana.
Sun yi gargaɗin cewa ɗaukar doka a hannu na iya haifar da mummunan sakamako.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da zage damtse wajen kare rayuka da tabbatar da adalci a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link