Ruwan sama mai ƙarfi ya raba mutum 612 da gidajensu a Yobe

[ad_1]



Ruwan sama mai ƙarfi ya yi ɓarna a garin Potiskum, Jihar Yobe, inda ambaliya ta mamaye yankuna da dama, ta lalata gidaje da dama a cikin garin.

Ruwan saman da ya fara sauka a daren Juma’a ya bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba, bayan gidajensu sun rushe ko kuma sun samu mummunan lahani.

Musa Adamu, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, ya shaida wa Aminiya cewa: “Gidaje da dama sun lalace, amma ba a rasa rai ba. Yawancin waɗanda abin ya shafa sun koma sansanonin ’yan gudun hijira, yayin da wasu ke zaune a gidajen ‘yan uwansu.”

Yankunan da abin ya fi  shafa su ne waɗanda ke kusa da magudanan ruwa, inda gine-gine da dama suka rushe.

Waɗannan sun hada da Arikime, Ramin Kasa, Tandari, Nahuta, Boriya, Rugar Fulani, da Unguwar Kuwait.

Sauran yankunan da ambaliya ta shafa sun haɗa da Old Prison, Filin Nashe, Unguwar Makafi/Majema, Unguwar Jaji Bakin Kwari, Afghanistan, Tsangaya Bakin Kwari, Karofi, Bayan Garejin Danjuma, da yankunan da ke bayan Fudiyya Potiskum.

Mazauna waɗannan yankuna suna fuskantar ambaliya akai-akai saboda rashin ingantattun magudanan ruwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *