Manyan Ƙalubale 5 Da Janar Christopher Musa Dole Ya Fuskanta Don Yin Nasara
[ad_1]
A matsayinsa na ministan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa mai ritaya yana riƙe da muƙami mai matuƙar nauyi a tsarin tsaron ƙasa. Yayin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na Nijeriya, nasararsa za ta ta’allaka ne kan yadda zai tunkari manyan ƙalubale masu zurfi da suka daɗe suna damun rundunonin tsaro.
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen shi ne yaƙi da matsalolin tsaro masu yawa a lokaci guda. A Arewa maso Gabas akwai Boko Haram da ISWAP, a Arewa maso Yamma ana fama da ƴan bindiga da satar mutane, a Arewa ta tsakiya rikicin manoma da makiyaya na ƙara ta’azzara, yayin da a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu ake fama da tashe-tashen hankula na ƴan aware da kuma fasa bututun mai. Wannan yanayi na sa Sojoji su bazu a fannoni da dama, lamarin da ke buƙatar tsari, da daidaito da dabaru na musamman domin kada a rasa nasarorin da aka samu a wasu yankuna.
- ’Yan Majalisa Sun Roƙi Tinubu Ya Sake Duba Lamarin Janye Musu ’Yansanda
- Shugaba Xi Ya Saurari Rahoton Aiki Daga Kantoman Yankin Musamman Na Macao
Wani babban ƙalubale shi ne dawo da amincewar jama’a ga rundunonin soji. A tsawon shekaru, zarge-zargen tauye haƙƙin ɗan Adam da asarar rayukan fararen hula sun raunana dangantaka tsakanin Sojoji da al’umma musamman bayan ƙarin kuskure kai harin ta sama. Samun sahihin bayanan sirri daga jama’a na da muhimmanci wajen yaƙi da ta’addanci, amma hakan ba zai yiwu ba idan babu amincewa. Don haka, Janar Musa na da alhaƙin ƙarfafa ladabi, da bin doka, da hulɗa mai kyau tsakanin rundunar Sojojin ƙasar da al’umma.
Yawaitar makamai ba bisa ƙa’ida ba da raunin tsaron iyakoki ma na daga cikin manyan barazana. Iyakokin Nijeriya masu faɗi da rikice-rikice a yankin Sahel sun sa makamai na shiga hannun ƴan ta’adda da masu laifi cikin sauƙi. Janar Musa dole ne ya ƙarfafa haɗin gwuiwa tsakanin hukumomin tsaro, da leƙen asiri, da ƙasashe makwabta domin toshe hanyoyin shigo da makamai da kuma inganta sa ido a kan iyakoki. Shi da kansa ya taɓa cewa; yin katanga a iyakar hanya ce babba wajen tabbatar da tsaro.
A ƙarshe, tabbatar da walwala da jin daɗin dakarun soji, da haɗin gwuiwar hukumomin tsaro, da cikakken goyon bayan siyasa su ma manyan ƙalubale ne. Gajiya da rashin isassun kayan aiki, da jinkirin alawus na iya raunana ƙwarin gwuiwar sojoji. Haka kuma, rashin daidaito tsakanin sojoji, da ƴansanda da sauran hukumomi kan rage tasirin yaƙin tabbatar da tsaro.
Nasarar Janar Christopher Musa za ta dogara ne kan yadda zai gyara waɗannan matsaloli, ya ƙarfafa rundunoni sama da na ƙasa tare da tabbatar da cewa matakan tsaro sun yi daidai da manufofin zaman lafiya da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
[ad_2]
Source link