Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti
[ad_1]
Kwamandan Ƙungiyar sa kai ta Vigilante gungun Najeriya (VGN) reshen Jihar Kaduna, Abdulwahab Muhammed ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta amince da Ƙungiyar a matakin ƙasa ta hanyar sanya hannu a kan ƙudurin da aka gabatar.
A cewar ƙungiyar bisa la’akari da irin rawar da take takawa wajen daƙile ayyukan miyagu da samar da tsaro a sassan ƙasar nan.
Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta sa hannu kan kudurin amincewa da kungiyar domin kasancewa cikin jerin hukumomin tsaro na kasa, la’akari da irin jajircewar da suke nunawa musamman a Jihar Kaduna.
Abdulwahab ya bayyana hakan ne yayin taron ƙarin girma da ƙungiyar ta shirya ga wasu jami’anta a Ƙaramar hukumar Jama’a, inda kuma aka karrama wasu fitattun mutane da ke ba da gudunmawa wajen tallafa wa ayyukan tsaro.
Kwamandan ya ce, suna da kyakkyawar fahimta da haɗin kai da sauran jami’an tsaro, inda suke miƙa waɗanda suka kama ga ’yan sanda don gudanar da bincike da yin hukunci bisa doka. Ya roƙi gwamnatin jihar Kaduna da ta ƙara tallafa musu da kayan aiki domin sauƙaƙa gudanar da ayyukansu.
Shi ma Shugaban karamar hukumar Jama’a Peter Tanko Dogara wanda sakataren Ƙaramar hukumar Jama’a, Dakta Shehu Usman Danbala ya wakilta, ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar wajen tabbatar da tsaro a matakin sa kai, tare da kiran al’umma da su riƙa basu cikakken goyon baya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link