Sin Ta Yi Kira Ga Dukkan Kasashen Da Ke Son Zaman Lafiya Su Dakile Burin Japan Na Sake Shan Damarar Soji
[ad_1]
A yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, wajibi ne kasar Sin ta yi aiki kafada da kafada da dukkan kasashen da ke son zaman lafiya don dakile yunkurin masu tsattsauran ra’ayin kasar Japan na karfafa sake shan damarar soji, tare kuma da hada karfi da karfe wajen kare sakamakon nasarar da aka samu a yakin duniya na biyu, da kuma zaman lafiyar duniya da aka samar da kyar.
Ya ce matakin da Japan ta dauka na gaggauta yunkurinta na shan damarar soji na barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin, wanda kasashen yankin da ma sauran kasashen duniya suka yi matukar nuna taka-tsantsan a kai. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link