Kashe-kashe da garkuwa da mutane sun dawo a Katsina

[ad_1]



’Yan bindiga a daren Litinin sun kai hari a kan wasu al’ummomi na Karamar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, inda suka kashe mutane takwas tare da yin garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba.

A cewar mazauna yankin, maharan sun kutsa Unguwar Alhaji Barau, Gidan Dan Mai-gizo da Gidan Hazo a gundumar Na’alma a karamar hukumar, inda suka yi ta barna tsawon sa’o’i.

Shaidu sun ce ’yan bindigar sun kuma toshe hanyar Dayi-Na-Alma, inda suka kwace babura tare da karɓe wayoyi da kuɗin jama’a.

Mutane 8 sun mutu, da dama sun gudu

Mazauna yankin sun bayyana cewa mutum uku aka kashe a Gidan Naino karkashin gundumar Na-Alma, mutum ɗaya a Unguwar Alhaji Barau, sannan mutum biyu-biyu a Unguwar Maigizo da Unguwar Hazo.

An kuma gano cewa an sace tumaki a Unguwar Galadima, lamarin ya tilasta wa mazauna da dama guduwa cikin firgici.

Yarjejeniyar zaman lafiya ta wargaje

An ɗauki wannan lamari a matsayin gazawar yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka kulla da ‘yan bindiga a wasu kananan hukumomi na jihar domin dakatar da hare-hare a kan al’ummomi masu rauni.

An rawaito cewa al’ummomin da aka rufe cikin yarjejeniyar sun ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga ba tare da turjiya ba, lamarin da ya ƙara tsoratar da jama’a.

A watan Nuwamban bara, kananan hukumomi 18 daga cikin 34 na jihar sun shiga yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga.

Duk da cewa wasu yankuna sun samu ’yar natsuwa, wasu kuma har yanzu suna fuskantar hare-hare, abin da ya haifar da shakku kan ingancin yarjejeniyar.

Kananan hukumomi 18 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar

A watan Agustan 2025, sarakunan gargajiya da wakilan al’umma sun yi hoto tare da shugabannin ’yan bindiga a taron yarjejeniyar zaman lafiya a Karamar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina.

Kananan hukumomin da suka shiga yarjejeniyar sun haɗa da: Kankara, Kafur, Malumfashi, Funtua, Batagarawa, Charanchi, Sabuwa, Dandume, Faskari, Matazu, Musawa, Safana, Kurfi, Dutsinma, Jibia, Batsari, Danmusa da Bakori.

A karkashin yarjejeniyoyin da aka cimma, shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya sun yi alkawarin bin sharuddan, yayin da ’yan bindiga suka amince da dakatar da hare-hare da sakin fursunoni.

Shakku kan ingancin yarjejeniyar

Masu suka sun sha ƙakubalantar ingancin yarjejeniyoyin, inda da dama daga cikinsu aka kulla ta hannun shugabannin al’umma ba kai tsaye daga gwamnati ba, wacce ta sha bayyana cewa ba za ta tattauna da ‘yan ta’adda ba.

Mazauna yankin da suka yi magana da Aminiya sun nuna damuwa cewa ‘yan bindiga na kai hare-hare a yankin gabashin Malumfashi a kullum, musamman a gundomomin Dayi da Na-Alma.

Ɗaya daga cikinsu, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce jama’a yanzu na rayuwa cikin tsoro, ya kuma yi kira da a tura jami’an tsaro da yawa zuwa yankunan da abin ya shafa.

A cewarsa, ya kamata a ayyana cikakken yaƙi da ‘yan bindiga da abokan huldarsu.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta Katsina, Abubakar Sadiq, jiya, bai ɗaga kira ba kuma bai amsa rubutaccen saƙon da wakilinmu ya tura masa ba.

Ɗaya daga cikin shugabannin Dattawan Katsina, Bashir Kurfi, ya soki kan yarjejeniyar, yana mai cewa barin ’yan bindiga su tsara sharuddan da suke so a bi ba zai haifar da ɗa mai ido ga tsaron al’umma ba.

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sha nanata cewa ba zai shiga kowace irin yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga ba.

“Ina matsayin gwamna, ba zan tattauna da ’yan bindiga a lokacin rauni ba, ba zan fara roƙon ‘yan bindiga su zo su tattauna da ni ba,” in ji Dikko a wata hira da aka yi da shi kwanan nan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *