Yawaitar Garkuwa Da Mutane Ya Sa Ba Ma Iya Barci da Ido Biyu — Hakimin Gundale
[ad_1]
Yawaitar Garkuwa Da Mutane Ya Sa Ba Ma Iya Barci Da Ido Biyu – Hakimin Gundale
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Al’ummar garin Gundale da ke kan iyakar Jihar Taraba a Kudancin Jihar Gombe, cikin Karamar Hukumar Shongom, na ci gaba da rayuwa cikin fargaba da tashin hankali sakamakon yawaitar satar mutane da ke addabar yankin.
Hakimin Gundale, Alhaji Aliyu Ibrahim, ya bayyana cewa, mazauna garin ba sa iya kwanciya lafiya saboda yadda ‘yan bindiga ke shiga gari ba tare da wata tangarda ba suna yin garkuwa da mutane a fili.
“Gaskiya ba ma iya barci da ido biyu a rufe. ‘Yan bindiga na shigowa garinmu ana kallo za su dauki mutane. A makon jiya kadai an sace mutum bakwai,” in ji hakimin.
Ya ce, duk da kokarin ‘yan banga da mafarauta, matsalar ta fi karfinsu, ganin cewa, garin yana kusa da duwatsu kuma yana kan iyaka da Jihar Taraba, inda masu laifi ke amfani da dazuka wajen tserewa da wadanda suka sace.
Hakimin ya kara da cewa, mutane masu hali da ‘yan kasuwa da dama sun daina kwana a Gundale saboda tsoron a sace su, domin a kowane lokaci ‘yan bindiga kan shiga gari suna farautar mutane.
Alhaji Aliyu ya roki gwamnatin jihar da ta taimaka musu ta hanyar kafa sansanin sojoji ko jami’an tsaro a yankin, tare da hadin gwiwar mafarauta domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wasu mazauna garin da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa, rayuwarsu na cikin hatsari, domin ‘yan bindiga na iya shiga gari a kowanne lokaci ba sai da dare ba saboda babu isassun jami’an tsaro a yankin.
Sun roki gwamnati da kada ta manta da su, inda suka ce su ma ‘yan kasa ne kamar kowa da ya kamata a kare musu rayuwa da dukiyoyinsu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link