Bataliyar sojoji na musamman sun sauka a Filato don daƙile ’yan bindiga
[ad_1]
Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta tura sabuwar runduna ta musamman domin yaƙi da matsalar ta’addanci a Jihar Filato.
Tuni dakardun, ƙarƙashin Bataliya ta Musamman ta Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, suka isa jihar domin aikin kawo ƙarshen matsalolin garkuwa da mutane da kuma ayyukan ’yan bindiga da tsaro ƙarƙashin rundunar.
Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya tura Rundunar Sojoji na Musamman ƙarƙashin Bataliya ta Musamman sake ƙarƙashin ofishinsa domin shawo kan matsalar hare-haren ’yan bindiga da kuma satar mutane da ta sake ƙara kamari a jihar.
Da yake tarbar su a Hedikwatar Runduna ta 3, Babban Kwamandan Runduna ta 3 kuma Jagoran Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Enduring Peace, Manjo Janar Folusho Oyinlola, wanda Babban Hafsan Ayyuka, Birgediya Janar Senlong Sule ya wakilta, ya ja kunnen sojojin da su kasance masu ƙarfi da tsauri wajen kai farmaki ga ’yan bindiga.
Ya yaba da jagorancin Babban Hafsan rundunar Ƙasa bisa samar da kayan yaƙi da sauran kayan aiki da za su taimaka wajen cika manufar rundunar yadda ya kamata.
Manjo Janar Oyinlola ya kuma roƙi jama’ar jihar da kada su firgita idan suka ga motsin sojoji da manyan kayan yaƙi a tituna.
Ya gode musu bisa goyon bayan da suke bai wa rundunar, tare da kira da su ƙara bayar da sahihan bayanai kan inda ’yan ta’adda ke ɓuya domin taimaka wa sojoji wajen samun nasarar kawo zaman lafiya a jihar.
A cewar Babban Hafsan Ayyuka, wannan matakin zai zama babban sauyi wajen magance matsalar rashin tsaro a Filato.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link