Sojoji Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
[ad_1]
Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da nasarar ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su a yankin Kajuru/Kujama na Jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 6 ga Janairu, wacce Laftanar Kanar Shuaib Umar, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojan ya sanya wa hannu, ya ce, an gudanar da aikin ne a ranar Litinin, 5 ga Janairu, 2026.
“An mika wadanda aka ceto lafiya ga wakilan Karamar Hukumar Kajuru da Majalisar Masarautar Kajuru don hada su da iyalansu,” in ji sanarwar.
[ad_2]
Source link