Shugabar Kasar Dominica: Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Domin Tabbatar Da Moriyar Daukacin Bil Adama
[ad_1]
Shugabar kasar Dominica, Madam Sylvanie Burton, ta zanta da wakiliyar CMG a kwanan baya, yayin da take ziyara a kasar Sin, inda ta yi tsokaci kan wasu shawarwarin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, na neman tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da cudanyar wayewar kai, da kulawa da al’amura yadda ya kamata a duniya. A cewarta, wadannan shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar suna da nufin tabbatar da moriyar bai daya ta daukacin bil Adama, gami da makomarsu mai haske, wadda ta shafi manya da kananan kasashe baki daya.
Shugaba Burton ta kara da cewa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin yana kokarin kulla huldar hadin gwiwa tsakanin kasarsa da kananan kasashe. Wannan mataki, a ganinta, yana da matukar ma’ana, saboda ya sa kananan kasashe samun damar bayyana ra’ayoyinsu domin sauran kasashe su ji. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link