Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makon

[ad_1]



Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa jihohi 11 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa ambaliya daga ranar Lahadi zuwa Alhamis.

A cikin sanarwar da Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli, ta fitar, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Benuwe, Nasarawa, Taraba da Delta.

Sauran sun haɗa da Neja, Kebbi, Kano, Katsina, Sakkwato da Zamfara.

Sanarwar ta bayyana cewa cikar kogunan Gongola, Benuwe da Neja na ƙara barazana ga al’ummar da ke zaune a gefen kogunan.

Gwamnati ta shawarci al’ummar da ke yankunan da abin ya shafa, musamman waɗanda ke kusa da Numan da Lokoja, da su bar wuraren nan take don guje wa afka wa hatsari.

Haka kuma ta buƙaci gwamnatocin jihohi da hukumomin agaji su gaggauta ɗaukar matakan kariya da bayar da taimako domin rage illar ambaliyar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *