Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13 a Borno

[ad_1]



Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce, sun kashe mayaƙan Boko Haram 13 bayan da suka yi nasarar daƙile wani harin kwantan ɓauna da ‘yan mayaƙan suka shirya da wasu bama-bamai a kan ayarin sojojin da ke kusa da garin Kareto na Jihar Borno, a ranar Laraba.

Harin dai ya faru ne a yayin da sojoji da ke rakiyar manyan motocin da ke ɗauke da kayan jin ƙai a kan hanyar Gubio zuwa Damasak suka yi ta luguden wuta kan ’yan Boko Haram, bayan tarwatsewar wasu bama-bamai guda biyu.

“Sojoji sun ɗauki matsaya cikin gaggawa tare da murƙushe ‘yan tada ƙayar baya da ƙarfin wuta, inda suka kashe 13 nan take,” in ji rundunar OPHK a cikin wata sanarwa.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da: Bindigogi ƙirar AK-47 guda takwas da akwatunan albarusai guda 10 da alburusai masu yawa da kuma bama-bamai.

Wani soja ya samu rauni kaɗan, yayin da tayoyin motoci masu sulke huɗu suka lalace sannan wasu manyan motoci biyu suka ƙone.

Sojojin sun ce, an ƙara ƙaimi domin hana masu tada ƙayar baya ’yancin kai hari da kuma tabbatar da kayayyakin jin ƙai sun isa Damasak.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *