Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

[ad_1]


An yi zargin kisan wani dalibi a Jami’ar Jos, mai suna Peter Mafuyai, da cewa dan uwansa dalibi ne ya kashe shi, wanda aka bayyana mai kisan da Nanpon Timnan, a gidan da suke zaune a wajen harabar jami’ar da ke kauyen Rusau, a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Jihar Filato.

Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito daga wani bidiyo da Happy Londi ta wallafa a Facebook cewa mamacin dalibi ne a shekarar karshe ta mataki na uku (300 lebel) a Sashen Banki da Kudi.

Londi ta kara da cewa Nanpon Timnan dalibi ne na mataki na biyu (200 lebel) a Sashen Kimiyyar Noma.

Ta rubuta cewa: “Wani dalibi da ake kira Nanpon Timnan, dalibi ne na 200 lebel a Sashen Kimiyyar Noma, ana zargin ya kashe wani dalibi, Peter Mafuyai, dalibi na 300 lebel a Sashen Banki da Kudi a Jami’ar Jos.”

A cikin wani bidiyo da aka hada da wannan rubutu, an ga gawar marigayin a cikin motar asibiti, likitoci suna rufe ta da wani kyalle mai launin Faful.

A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru.

A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi.

Ya ce: “Nanpon ya riga ya yanke Peter a kumatunsa yayin da yake rokon a bar shi. Lokacin da muka shiga tsakani muka ce ya daina, sai ya yi barazanar yanka duk wanda ya kusanto shi.

“Da Peter ya ga ba ya sauraron rokonsa, sai ya rungume shi yana rokonsa da kuka.

“Mun fita neman taimako amma babu wanda ya amsa mana. Da Peter ya yi kokarin tserewa sai ya fadi, Nanpon ya kamo shi ya ci gaba da saransa da adda.”

Wani kwararren masanin tsaro da yaki da ta’addanci ya wallafa a dandalin D a ranar Lahadi cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Filato sun kama wanda ake zargin.

Ya kuma ambaci majiyoyi da suka tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar rahoton da aka samu daga Babban Jami’in Tsaro na jami’ar.

Ya rubuta cewa, “Rundunar ‘Yansanda ta Filato ta kama wani dalibi mai shekaru 23 na Jami’ar Jos bisa zargin kashe abokinsa sannan ya binne shi a rami mara zurfi a cikin dakinsa da ke kauyen Rusau a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

“Majiyoyi sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi a Jos, inda suka danganta da rahoton da aka samu daga Babban Jami’in Tsaron jami’ar.

“A cewar majiyoyin, wanda ake zargin mai suna Dabid Nanpon Timmap, dalibi a matakin shekara ta uku a jami’ar, ya kai wa Peter Mata Mafurai, mai shekaru 22, hari da adda, ya kashe shi a gidansa.”

Zagazola ya kara da cewa, bayan samun kiran gaggawa da misalin karfe 9:30 na safiya, DPO na sashin Laranto ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa wurin, inda aka kama wanda ake zargin.

“Majiyoyin sun ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya binne mamacin a cikin rami mara zurfi da ya haka a cikin dakinsa. An tono gawar kuma an kai ta dakin ajiye gawarwaki na Asibitin koyarwa na Jami’ar Bingham domin yin binciken gawar (autopsy),” in ji shi.

Ya kara da cewa, an tsare wanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike domin gano hakikanin dalilin kashe abokin nasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *