’Yan Najeriya kada su zaɓi ADC, ba ta da abun bayarwa — Shettima
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya shawarci ‘yan Najeriya kada su goyi bayan jam’iyyar ADC, inda ya ce babu wani abu da za ta iya bayarwa. Ya yi wannan magana ne a ranar Laraba a filin baje koli na Gusau da ke Jihar Zamfara, yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyarsa….