Category: Latest News

  • Mun Ceto Nijeriya Yayin Da Take Gab Da Dilmiyewa – Tinubu

    [ad_1]

    Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin duba harajin da aka ɗora wa gidan jaridu da Rediyo da talabijin domin ƙarfafa masana’antar watsa labarai da kuma inganta rawar da take takawa a kundin tsarin mulki.

    Shugaban ya yi wannan alkawari ne a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin wani taron buda baki da ya yi tare da shugabannin kafafen yaɗa labarai.

    • Nijar Ta Haramta Fitar Da Dabbobi Ketare Don Takaita Karancinsu A Cikin Gida
    • Ministan Wajen Sin Ya Zanta Da Takwarorinsa Na Afghanistan Da Holland

    Tinubu ya yaba wa masu gidajen jarida, editoci da ‘yan jarida bisa rawar da suke takawa wajen sanar da al’umma bayanai, halin da kasa ke ciki, samar da guraben aiki da kuma tabbatar da dimokuraɗiyya ta gaske.

    A cewarsa, shugabanci na gari yana buƙatar ɗaukar matakai masu wahala a lokacin da ya dace, yana mai cewa gazawar shugabanni wajen ɗaukar mataki a lokutan da suka dace na iya zama kamar guje wa nauyin da ke kansu.

    Ya bayyana cewa wasu sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun kasance masu wahala, amma matakai ne da suka zama dole domin daidaita tattalin arziki da kuma hana Nijeriya dilmiyewa cikin matsalar kuɗi mai tsanani.

    Ya ce: “Dole ne mu ceci ƙasar nan mu dawo da ita yayin da take gab da dilmiyewa.

    “A yau zan iya tsayawa, in yi alfahari a gabanku cewa, Nijeriya ta farfaɗo daga wancan mawuyacin lokacin.”

    [ad_2]

    Source link

  • Hukumomin Gabatar Da Kararraki Na Sin Sun Dukufa Wajen Yakar Laifukan Sayar Da Kayayyakin Jabu

    [ad_1]

    Wata sanarwar da hukumar koli ta gabatar da kararraki ta kasar Sin ko SPP a takaice, ta raba wa manema labarai a Asabar din nan, ta ce a shekarar 2025 da ta gabata, hukumomin gabatar da kararraki na kasar Sin, sun gurfanar da mutane 18,376 gaban kuliya, kan laifukan da suka shafi samarwa, da kuma sayar da kayayyakin jabu da marasa inganci.

    Kazalika, SPP ta ce hukumomin a dukkanin fadin kasar Sin, sun ci gaba da matsa kaimin shawo kan laifukan dake barazana ga nagartar abinci, da magunguna, da nufin kare lafiyar jama’a.

    SPP ta kara da cewa, a shekarar ta 2025, masu gabatar da kararraki sun gurfanar da mutane 9,595 gaban kotu kan zargin aikata laifuka 5,026 masu nasaba da abinci, da kuwa wasu mutanen 4,043 kan laifuka 2,135 masu alaka da magunguna. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

    [ad_2]

    Source link

  • Nijar Ta Haramta Fitar Da Dabbobi Ketare Don Takaita Karancinsu A Cikin Gida

    [ad_1]

    Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sanar da hana fitar da dabbobi zuwa kasashen ketare a wani yunkuri na samar da wadatuwar dabbobin a cikin gida, wannan mataki dai shi ne irinsa na biyu da aka dauka a ‘yan shekarun nan cikin wannan kasa dimbin jama’arta ke harkokin kiwon dabbobi don sayarwa.

    Sai dai tuni wannan mataki ya gamu da suka daga ‘yan kasuwa da masu turkar dabbobin domin sayarwa bayan da suka bayyana cewa kai tsaye matakin zai iya haifar musu da asara mai yawa musamman a lokacin sallar layya.

    • Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Aikin Noma Domin Samar Da Wadataccen Abinci
    • Ministan Wajen Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Kawo Karshen Matakan Soji A Gabas Ta Tsakiya

    Nepal: Mawakin Gambara Na Dab Da Lashe Zaben Shugabancin Kasar

    Tsohon mawakin gambara Balendra Shah yana gab da samun gagarumar nasara a babban zaben Nepal, inda jam’iyyarsa ta Rastriya Swatantra ke kan gaba.

    Sakamakon farko na nuna yadda matasa suka yi watsi da tsofaffin ‘yan siyasa, wanda hakan ke zama babban sauyi a tsarin mulkin kasar. A halin yanzu, Shah na ba wa tsohon Firayim Minista KP Sharma Oli rata mai nisa, lamarin da masu nazari ke kallo a matsayin sakamakon zanga-zangar yaki da cin hanci da rashawa da ta gudana a kasar.

    Ana ganin wannan nasara a matsayin bukatar jama’a ta samun sabon jini da sauyi na gaske a siyasar Nepal. Yayin da ake ci gaba da kirga kuri’u, magoya baya na murna a Kathmandu, ana kuma sa ran bayyana sakamakon karshe nan da 9 ga watan Maris.

    Nasarar ka iya bai wa jam’iyyar RSP damar kafa gwamnati mai karfi don aiwatar da sauye-sauyen da aka yi alkawari.

    [ad_2]

    Source link

  • Mutum 6 sun rasu, 9 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi

    [ad_1]



    Aƙalla mutum shida ne suka riga mu gidan gaskiya, yayin da wasu tara suka ji jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Jihar Kogi.

    Hatsarin ya auku ne a daren ranar Alhamis a kan hanyar Lokoja zuwa Obajana, inda wata motar haya ƙirar Toyota Hiace ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota.

    Shaidu sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne a yankin Apata, lokacin da motar hayar mai lamba XW 142 ENU ta yi karo gaba-da-gaba da wata tirela mai lamba KAB 575 XA wadda ta taho daga ɗaya hannun.

    Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar hatsarin a ranar Asabar.

    Kwamandan hukumar na shiyyar Jihar Kogi, Tenimu Yusuf Etuku, ya bayyana hatsarin a matsayin abun tausayi, yana mai cewa gudun wuce ƙima ne ya haddasa shi.

    Ya bayyana cewa jimillar mutane 17 ne hatsarin ya rutsa da su; maza 14 da mata uku.

    A cewarsa, mutane tara (maza takwas da mace ɗaya) sun jikkata, yayin da mutum shida (maza biyar da mace ɗaya) suka rasa rayukansu.

    Sauran mutum biyu kuma an ceto su ba tare da sun ji rauni ba.

    Etuku, ya ƙara da cewa an kai waɗanda suka jikkata Asibitin Fisayo da ke Obajana domin kula da su, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka rasu ɗakin ajiye gawarwaki na Ankuri da ke Lokoja.

    Kayayyakin da aka samu bayan aukuwar hatsarin sun haɗa da kuɗi Naira 20,800, jakunkuna biyu, wayoyin hannu guda biyu, da wasu buhunhuna guda uku.

    An kuma miƙa motocin da suka yi hatsarin ga rundunar ’yan sanda da ke Obajana.

    Daga ƙarshe, kwamandan ya shawarci direbobi da su guji gudun wuce ƙima a manyan hanyoyi domin rage aukuwar hatsari da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.


    [ad_2]

    Source link

  • Shawarar GGI Ta Sin Na Ingiza Daidaito Ga Duniya Mai Fama Da Tangal-Tangal

    [ad_1]

    Mahalarta taron karawa juna sani na kasa da kasa, na dandalin Baku karo na 13, sun bayyana gamsuwa game da tasirin shawarar inganta jagorancin duniya ko GGI, wadda kasar Sin ta gabatar, suna masu bayyana shawarar a matsayin wadda ke samar da daidaito ga yanayin duniya mai cike da sauye-sauye da tangal-tangal.

    Da yake tsokaci game da hakan a taron na jiya Juma’a, tsohon wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin game da harkokin Turai Wu Hongbo, ya ce shawarar GGI, na yayata manufar martaba ikon kasashe na mulkin kai bisa daidaito, da nacewa biyayya ga dokokin kasa da kasa, da ingiza cudanyar mabanbantan sassa, da sanya bukatun bil’adama gaban komai, da manufar daura aniyar aiwatar da matakai a zahiri.

    Wu ya kara da cewa, yayin da ake ganin karuwar manufofin daukar matsayar kashin kai da kariyar cinikayya, kana ake ganin fadadar rikice-rikice tsakanin mabanbantan yankunan duniya, da karin koma baya a tsarin jagorancin duniya, shawarar GGI ba kawai tana karfafa dalilai da ka’idojin kafuwar MDD ba ne, har ma ta zamo amsa ga burikan al’ummun kasa da kasa.

    A nasa tsokacin kuwa, ministan raya tattalin arziki na kasar Azerbaijan Mikayil Jabbarov, bayyana goyon bayan kasarsa ya yi ga shawarar ta GGI. Yana mai cewa, tsarin gudanar duniya na yanzu na fuskantar tarin kalubale masu haifar da sauyi, amma duk da haka, kasar Sin ta samar da hanyar warware hakan, don wanzar da daidaito tsakanin sassan kasa da kasa.

    Shi kuwa tsohon shugaban kasar Slovenia Borut Pahor, cewa ya yi kasar Sin ba ta shiga duk wasu nau’ikan tashe-tashen hankula, kuma ta nunawa duniya matakanta na koli, a fannin wanzar da daidaito, da tsayawa kan yanayi na tabbas, wanda hakan ya sanya ta zama muhimmin ginshiki na samar da daidaito a duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

    [ad_2]

    Source link

  • NFF Na Duba Yiwuwar Soke Wasan Sada Zumunci Da Kasar Iran

    [ad_1]

    Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta ce tana sa ido sosai kan rikicin da ke kara tabarbarewa tsakanin kasashen Iran, Amurka da Israila, yayin da rashin tabbas ke karuwa game da shirye-shiryen wasannin sada zumunta na kasa da kasa da tawagar kwallon kafa ta Nijeriya da takwararta ta kasar Iran, in ji wani rahoton da jaridar PUNCH Sports Edtra ta ruwaito.

    Tun da farko an shirya Nijeriya za ta shiga gasar hadaka ta kasashe hudu da za a buga a Amman, inda Super Eagles za ta fafata da Iran a ranar 27 ga watan Maris kafin ta hadu da tawagar kwallon kafa ta Jordan mai masaukin baki a ranar 31 ga watan na Maris.

    • Za a Gudanar Da Tattaunawa Kan Batun Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka a Faransa Daga Ranar 14 Zuwa 17 Ga Watan Maris
    • Duniya Ta Shaida Kokarin Sin Bisa Shirin Ci Gaban Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’Umma Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15

    Hakazalika kuma ana sa ran tawagar kwallon kafa ta Costa Rica na cikin kasashen da za su buga karamar gasar, duk da haka an jefa shakku kan shirin bayan da Iran ta janye daga gasar a daidai lokacin da rikicin siyasa da na soja ke karuwa a Gabas ta Tsakiya, dan jaridar ESPN Colin Udoh ya ruwaito a karshen mako cewa masu shirya gasar suna binciken yiwuwar mayar da wasannin daga Gabas ta Tsakiya zuwa Turai saboda dalilai na tsaro.

    Da yake magana da PUNCH Sports Edtra, daraktan sadarwa na NFF Ademola Olajire ya ce ana ci gaba da tattaunawa yayin da hukumomi ke ci gaba da sa ido kan lamarin, lokacin da aka tambaye su ko akwai wata kasa ta Turai da ake ganin za a iya mayar da gasar zuwa can, Olajire ya ce alhakin hakan yana kan masu shirya gasar.

    Rikicin ya karu ne bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da wani hari na hadin gwiwa akan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya haifar da daukar fansa a duk fadin yankin, kasashe da dama tun daga lokacin sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka, wanda ya tilasta rufe sararin samaniya da kuma haifar da fargabar tsaro da suka fara shafar ayyukan wasanni.

    Sakamakon janyewar Iran, shirin da aka yi na kasashen hudu tun da farko ba shi da tabbas, masu shirya gasar suna tunanin shirya wani wasa na sada zumunci tsakanin Nijeriya da Jordan a wani wuri mai tsaro a nahiyar Turai idan gasar ba za ta ci gaba kamar yadda aka tsara ba.

    Shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijeriya Ibrahim Gusau ya nuna cewa hukumar har yanzu tana da lokaci domin tantance matakin da za a dauka, buga akalla wasa daya na sada zumunci a lokacin a watan Maris ya kasance babban abin da Super Eagles ke sa ido a kai, yayin da zakarun na gasar cin kofin Afirka sau uku ke ci gaba da kokarin ganin sun farfado ta tawagar.

    [ad_2]

    Source link

  • Trump Zai Yi Maraba Da Tawagar Kasar Iran A Gasar Kofin Duniya —Infantino

    [ad_1]

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasar za ta yi maraba da tawagar kasar Iran yayin da za ta karbi bakuncin gasar Kofin Duniya da za a buga a wannan shekarar a kasashen Amurka, Medico da Canada duk da cewa kasashen suna cikin yaki, a cewar shugaban FIFA Gianni Infantino.

    A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Instagram, Infantino ya ce ya gana da Trump a ranar Talata domin tattauna shirye-shiryen gasar, wadda Amurka, Canada da Medico za su karbi bakunci, kuma za a fara a ranar 11 ga Yuni.

    • Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Aikin Noma Domin Samar Da Wadataccen Abinci
    • Duniya Ta Shaida Kokarin Sin Bisa Shirin Ci Gaban Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’Umma Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15

    Infantino ya ce shi da Trump sun yi magana game da halin da ake ciki a Iran, an shirya Iran za ta buga wasanni uku a Amurka, amma yanzu ana shakku kan halartarsu kasar, tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka fara yaki a tsakaninsu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaban Addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei.

    Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki zuwa Isra’ila da kasashe hudu na yankin Gulf wadanda ke karbar bakuncin sansanonin sojin Amurka da suka hada da Bahrain, Kuwait, Katar da Hadaddiyar Daular Larabawa.

    A yayin tattaunawar, shugaba Trump ya sake nanata cewa, “Ba shakka, kasar Amurka tana maraba da tawagar Iran” in ji Infantino, Iran za ta fafata da New Zealand da Belgium a Los Angeles a ranakun 15 da 21 ga watan Yuni kafin ta buga da kasar Masar a Seattle a ranar 26 ga watan na Yuni.

    A makon da ya gabata Trump ya shaida wa jaridar Politico, cewa “Gaskiya ban damu ba idan Iran ta buga gasar cin kofin duniya a kasar nan” bayan fara yaki tsakanin kasashen, an ambato shugaban hukumar kwallon kafa ta Iran Mehdi Taj yana cewa “Abin da ya tabbata shi ne bayan wadannan hare-haren, yana da wuya muyi marmarin zuwa Amurka”.

    [ad_2]

    Source link

  • Jarumin Kannywood Umar Ascon ya rasu a Kano

    [ad_1]



    Allah Ya yi wa jarumin fina-finan Hausa Umar Ascon, wanda aka fi sani da Alhaji Lado Mai Barkono a cikin shirin nan mai dogon zango Garwashi, rasuwa.

    Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a Asibitin Koyarwa ma Malam Aminu Kano, bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.

    Wani furodusa a masana’antar Kannywood, Abubakar Yahaya Matinko, wanda suke unguwa ɗaya da marigayin, ya tabbatar da rasuwar jarumin.

    Ya ce ko da yake marigayin bai daɗe a masana’antar ba, amma cikin ƙanƙanin lokaci ya samu karɓuwa sosai a wajen masu kallo.

    Ya ƙara da cewa marigayin ya rasu ya bar mata ɗaya mai juna biyu da kuma ’ya’ya mata biyu.

    Kafin shigarsa harkar fina-finan Hausa, marigayin yana kasuwancin man fetur a Hotoro Depot a Kano.

    Daga baya ne ya shiga harkar fim inda ya zama ɗaya daga cikin jaruman da suka yi fice a cikin shirin Garwashi a matsayin Alhaji Lado Mai Barkono.

    Baya ga haka, ya fito a wasu fina-finan Hausa kamar Wata Shida, Manyan Mata da sauran su.

    An gudanar da jana’izarsa a Masallacin Al‑Masjlisul Islami da ke unguwar Hotoro Ring Road a Kano, kusa da gidan man Gade-Gade, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

    Tuni jarumai da masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood suka fara miƙa saƙon ta’aziyya tare da nuna alhininsu kan rasuwar jarumin.


    [ad_2]

    Source link

  • An Samu Karuwar Tafiye-Tafiye Tsakanin Yankunan Sin Yayin Bikin Bazara Na Bana

    [ad_1]

    Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce an samu karin yawan tafiye-tafiye tsakanin yankuna daban daban na Sin, yayin balaguron lokacin bikin bazara na bana, wanda a kan kira “Chunyun” da harshen Sinanci.

    Alkaluman da ma’aikatar ta fitar a Asabar din nan, sun nuna cewa, a kwanaki 40 na karuwar balaguro da Sinawa ke ki tsakanin sassan kasar, a bana irin wadannan tafiye-tafiye sun kai biliyan 9.41. Adadin da ya karu da kaso 4.3 bisa dari kan na lokacin bikin bazarar shekarar 2025. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

    [ad_2]

    Source link

  • Manyan Kamfanonin Sin Suna Zuba Karin Jari A Jihar Xinjiang Ta Kasar

    [ad_1]

    A jiya Juma’a, kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati, na majalisar gudanarwar kasar Sin, da gwamnatin jihar Xinjiang ta kasar, suka gabatar da alkaluman zuba jari da manyan kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin suka samar a jihar ta Xinjiang, cikin shekaru 5 da suka gabata.

    Alkaluman sun nuna cewa, a shekarar 2025 kadai, manyan kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin sun zuba jarin da yawansa ya kai Yuan biliyan 265.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 38.5 a jihar Xinjiang, tare da samar da guraben aikin yi dubu 107 a jihar. Ban da haka, kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin, sun zuba jarin kudi da ya kai dala biliyan 159.5 a jihar Xinjiang, cikin shekaru 5 da suka gabata, lamarin da ya kasance babban taimako ga jihar, a kokarinta na raya tattalin arziki da zaman al’umma.

    Haka zalika, duk a jiya Juma’a, wasu manyan kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin 18, sun kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa da gwamnatin jihar Xinjiang, na neman kaddamar da sabbin ayyuka 92, wadanda suka shafi bangarorin makamashi, da sarrafa ma’adinai, da samar da na’urorin aiki na zamani, da dai sauransu.

    A cewar darektan kwamitin sanya ido kan kadarorin mallakar gwamnati na majalisar gudanarwar kasar Sin, Zhang Yuzhuo, ana zuba karin jari a jihar Xinjiang ne domin neman damar samar da guraben aikin yi, da damar wadatar da kai ga jama’ar wurin, da karfafa cudanya tsakanin mutane ‘yan kabilu daban daban, tare da ba da cikakkiyar kulawa ga dukkan al’ummun jihar ta Xinjiang. (Bello Wang)

    [ad_2]

    Source link