Category: Latest News

  • Mazauna Yankin Sun Tsere Bayan Gano Wasiƙar Kawo Hare-haren Ta’addanci a FCT

    [ad_1]

    Mazauna da dama na al’ummomin Kungaboku da Paze a cikin Babban Birnin Tarayya (FCT) sun tsere daga gidajensu bayan wata wasiƙa da ake zargin ‘yan bindiga ne suka rubuta ta bayyana, wadda ke barazanar kai hare-hare a yankin.

    A cikin wasiƙar da aka ce an samu a cikin littafin wani ɗalibi a wata makaranta mai zaman kanta, ‘yan bindigar sun yi rantsuwa cewa za su kai hari Kungaboku da makwabciyarta Paze domin ramuwar gayya kan kashe kwamandansu.

    • Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Birnin Paris
    • Ƙarin Farashin Fetur: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Nemi A Dakatar Da Karɓar Haraji

    Za a iya tuna cewa a ranar 7 ga Maris, sojojin Bataliya ta 7, tare da ‘yansanda da ‘yan sa-kai, sun ceto mutane 19 da aka sace.

    Wadanda aka ceto, mafi yawansu mazauna Paze da Kungaboku ne, sun samu ‘yanci ne yayin wani hadin gwiwar bincike da aikin ceto da aka gudanar a yankin Gidan Dogo da ke Karamar Hukumar Bwari.

    A yayin wannan aiki, an ruwaito cewa sojojin sun kashe wani ɗan bindiga, yayin da sauran suka tsere daga wurin da raunukan harbin bindiga da ake zargin sun samu.

    An kuma ruwaito cewa an gano wasiƙar barazanar ne a cikin littafin rubutun wani ɗalibi a wata makaranta mai zaman kanta da ke Paze, bayan da wani malami ya gano ta yayin da yake duba aikin gida na ɗalibin.

    Bayan sanarwa mahukunta makarantar, ‘yansanda sun kama ɗalibin, iyayensa, malamin da kuma shugabannin makarantar domin yi musu tambayoyi da bincike, kafin daga bisani aka sake su.

    Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa Kungaboku da Paze, wadanda ke kusa da Byazhin, dake cikin Kubwa a Karamar Hukumar Bwari, sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan.

    [ad_2]

    Source link

  • Trump na yi wa ƙasashe da NATO matsin lambar su taimaka masa a buɗe Mashigar Hormuz

    [ad_1]



    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya buƙaci ƙasashe da dama da kuma ƙungiyar tsaro ta NATO da su aike da jiragen ruwan yaƙi domin taimakawa wajen tabbatar da tsaron Mashigar Hormuz, a yayin da Iran ke ci gaba da barazanar kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa sakamakon yaƙin da take yi da ƙawancen Isra’ila da Amurka.

    Trump ya ce sojojin Amurka sun “lalata gaba ɗaya” garkuwar sojojin Iran a Tsibirin Kharg, tsibirin da ke kusan kilomita 30 daga gaɓar Tekun Fasha, wanda shi ne babbar tashar fitar da ɗanyen man Iran.

    Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa yana fatan ƙasashe kamar China, Faransa, Japan, Koriya ta Kudu da Birtaniya za su tura jiragen ruwa domin tabbatar da cewa Iran ba ta hana jiragen ruwa wucewa ta mashigar ba.

    Rahotanni sun ce an ji fashewar abubuwa kusan 15 a Tsibin Kharg a ranar Asabar, sai dai kamfanin dillancin labaran Iran na Fars ya ruwaito cewa ba a lalata tsarin samar da man ƙasar ba.

    Matsin lamba ga NATO da ƙasashen duniya

    Trump ya ce yana tattaunawa da ƙasashe da dama domin taimakawa wajen buɗe Mashigar Hormuz, wadda rufewarta ta janyo tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

    Ya kuma yi gargaɗi cewa idan NATO ba ta taimaka wa Amurka ba, ƙungiyar za ta fuskanci “mummunar makoma”, kamar yadda ya faɗa a wata hira da jaridar Financial Times.

    A halin yanzu, Japan da Australia sun bayyana cewa ba za su tura jiragen ruwan yaƙi ba, duk da cewa Japan ta ce za ta fitar da rarar man da take da shi domin rage tasirin ƙarancin man da rikicin ya haifar.

    Rikicin dai na ci gaba da tayar da hankali a kasuwar makamashi ta duniya, yayin da farashin ɗanyen mai ke ci gaba da tashi sakamakon fargabar rufe Mashigar Hormuz, wadda guda ce daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai a duniya.

    EU na duba yiwuwar buɗe Mashigar Hormuz

    Babbar jami’ar kula da harkokin tsare-tsare na Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), Kaia Kallas ta ce ƙasashen Tarayyar Turai na shirin fara tattaunawa kan matakan da tarayyar za ta ɗauka wajen tabbatar da buɗe Mashigar Hormuz.

    “Yana daga cikin muradanmu tabbatar da cewa Mashigar Hormuz ta kasance a buɗe,” in ji Kallas, gabanin taron ministocin harkokin waje na tarayyar a Brussels, kamar yadda Reuters ya ruwaito.

    Wannan dai ba ya rasa nasaba da kiran da Trump ya yi wa ƙasashen na Turai da ma na ƙungiyar tsaro ta NATO da su taimaka wajen tabbatar da cewa mashigar ta kasance a buɗe.

    Ofishin firaiministan Birtaniya ya sanar a ranar Lahadi cewa Mista Trump ya tattauna da Firaiminista Keir Starmer dangane da muhimmancin buɗe mashigar ta Hormuz domin daƙile yanayin da sufurin makamashi ke fuskanta a duniya.

    Barazanar Iran ga Netanyahu

    A gefe guda kuma, rundunar dakarun juyin-juya hali ta Iran (IRGC) sun yi barazanar “farauta da kashe” Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya shiga mako na uku.

    A cikin wani saƙo da suka wallafa a shafin su na Sepah News, rundunar ta ce idan Netanyahu na raye, za su ci gaba da farautarsa domin ya fuskanci sakamakon abin da suka kira aikata laifuka.

    A daidai wannan lokaci Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya a yankin Tekun Fasha, inda aka ji ƙarar fashe-fashe a Manama, babban birnin Bahrain.

    Haka kuma Saudiyya ta ce ta lalata jiragen yaƙi marasa matuƙa guda 10 da suka nufi Riyadh, sai dai Iran ta musanta hannu a harin.


    [ad_2]

    Source link

  • Ƙarin Farashin Fetur: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Nemi A Dakatar Da Karɓar Haraji

    [ad_1]

    Ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya, NLC, ta buƙaci gwamnati ta ba ma’aikata ƙarin alawus na tsadar rayuwa, ƙarin albashi na wucin gadi da kuma rangwamen haraji domin rage wahalar da karin farashin fetur ya jawo.
    A wata sanarwa da shugaban NLC, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu mai taken “Ce to ‘yan Nijeriya daga wannan firgici: taimakon gaggawa ya zama dole”, ƙungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta gaggauta farfaɗo da matatun man fetur na Nijeriya.
    • Boko Haram Sun Sake Kai Hari Kan Wani Sansanin Sojoji A Borno
    • Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Birnin Paris
    NLC ta bayyana cewa ƙarin farashin man fetur ya ƙara tsananta wahalar tattalin arziki ga ma’aikata da sauran ‘yan Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu.
    Kungiyar ta jaddada cewa ba daidai ba ne gwamnati ta jingina matsalar kawai da rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, tare da cewa hakkin gwamnati ne ta ɗauki matakan gaggawa domin kare jama’a daga wahala.
    NLC ta kara da cewa, bai da ce gwamnati ta ki ɗaukar matakan da za su sauƙaƙa wa jama’a ba, musamman a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa.

    [ad_2]

    Source link

  • Boko Haram Sun Sake Kai Hari Kan Wani Sansanin Sojoji A Borno

    [ad_1]

    Wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan wani sansanin sojoji da ke Ajilari, wanda yake a wajen birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
    Rahotanni sun ce harin na Ajilari ya faru ne a lokaci guda da wani hari a garin Baga, inda majiyoyi suka bayyana cewa ‘yan ta’addan sun gwabza yaki da sojoji a sansanin sojojin Baga.
    1. Binciken CGTN: Shawarar Inganta Wayewar Kai A Duniya Ta Kasar Sin Na Kawo Zaman Lumana Ga Duniya Mai Cike Da Hargitsi
    • Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Birnin Paris
    Majiyoyi sun shaida wa wakilin jaridar Daily Trust cewa, maharan sun kutsa cikin yankin ne da misalin karfe 12:30 na dare.
    Sai dai kuma, martani cikin gaggawa daga rundunar haɗin gwiwa ta sojoji, ‘yansanda, rundunar sa-kai ta CJTF, da kuma sojojin sama ya tilasta wa maharan ja da baya.
    Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun riga sun ɗauki matakan da suka dace domin shawo kan lamarin.

    [ad_2]

    Source link

  • An yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu da Iran a Birtaniya

    [ad_1]

    Ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a birnin Landan na Birtaniya, duk da cewa gwamnati ta haramta gudanar da gangamin jama’a saboda dalilan tsaro.

    ’Yan sanda sun ce an kama mutum 12 yayin zanga-zangar, tare da buɗe bincike kan wasu kalaman adawa da Isra’ila da aka yi a wajen gangamin.

    Ministar harkokin cikin gida ta Birtaniya, Shabana Mahmood, ta ce an haramta gangamin jama’ar ne domin kauce wa tarzoma, musamman a lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta bayan hare-haren da Iran ke kaiwa a matsayin martani ga farmakin Amurka da Isra’ila.

    Hukumar ’yan sanda ta Metropolitan Police ta ce wannan shi ne karon farko da aka haramta irin wannan zanga-zanga a Landan tun shekara ta 2012, sai dai an ba da damar gudanar da taro a wuri guda ba tare da yin gangami ba.

    ’Yan sanda sun shiga tsakanin masu zanga-zangar kashi biyu masu adawa da juna ta hanyar barin kowanne ɓangare ya yi nasa gangamin a gefuna biyu na Kogin Thames da ke daura da majalisar dokokin ƙasar.

    Masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu sun ɗaga tutoci da alluna da ke ɗauke da rubutun kalamai kamar “A dakatar da laifukan yaƙin Isra’ila”, suna mai nuni da farmakin da Isra’ila ke yi a Zirin Gaza tun bayan harin da aka kai ranar 7 ga Oktoba, 2023.

    Wata mata mai shekaru 81, Jean Apps, ta ce ta halarci zanga-zangar ne saboda abin da ta kira rashin adalcin da ake yi wa Falasɗinawa, da kuma hare-haren da ake kai wa Iran.

    A gefe guda kuma, masu zanga-zangar adawa da su sun ɗaga tutocin Amurka da Isra’ila tare da tuta mai tambarin “Zaki da Rana” ta Iran, suna jaddada goyon baya ga Reza Pahlavi, ɗan tsohon sarkin ƙarshe na Iran da ke zaman gudun hijira tun bayan juyin juya halin 1979.

    Waɗanda suka shirya zanga-zangar ta Ranar Al-Qudus, wato ƙungiyar Islamic Human Rights Commission, sun soki matakin hana zanga-zanga, suna mai cewa matakin na da alaƙa da siyasa.

    [ad_2]

    Source link

  • ’Yan Boko Haram sun sake kai hari sansanin soji a Borno

    [ad_1]



    Ana fargabar cewa wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari wani sansanin soja da ke Ajilari, wajen birnin Maiduguri a Jihar Borno.

    Rahotanni sun ce harin ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare, wanda ya kuma ya faru a lokaci guda da wani hari da ’yan ta’addan suka kai wamo a sansanin soji da ke Baga, inda suka yi artabu da dakarun soji.

    Sai dai Aminiya ta ruwaito cewa, wata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro da ta haɗa da sojoji, ’yan sanda, ’yan sa-kai da kuma rundunar sojin sama ta kai ɗauki cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa.

    Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa jami’an tsaro sun tari hanzari maharan.

    Wasu mazauna yankin sun ce sun tsinci kansu cikin tsananin firgici yayin da ƙarar harbe-harbe ta karaɗe ko’ina, da daidai lokacin da jiragen sama masu saukar ungulu ke shawagi a sama.

    “Mun ji tsorata sosai. Saboda ƙarar harbe-harbe ta karaɗe ko’ina. Amma AlhamdulilLah yanzu lamarin ya lafa, an kuma ci gaba da sallar dare,” in ji wani mazaunin Gomari, Bashir Yusuf.

    A ‘yan kwanakin nan dai ‘yan ta’addan na ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojoji a yankin.

    A makon da ya gabata ne Ministan Tsaro, Christopher Musa ya gayyaci hafsoshin tsaron Najeriya zuwa wani taron gaggawa, inda daga bisani suka gana da Shugaba Bola Tinubu tare da manyan jami’an tsaro.

    Bayan taron, Minstan ya bayyana cewa shugabannin tsaron sun yanke shawarar sauya dabarun yaƙi, yayin da shugaban ƙasar ya ba da umarnin a gaggauta samar da sabbin kayan aiki domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci.


    [ad_2]

    Source link

  • An kama mai shekaru 74 da hodar iblis a filin jirgin saman Abuja

    [ad_1]



    Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), sun kama wani mutum mai shekaru 74 a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bisa zargin yunƙurin safarar hodar iblis.

    An kama mutumin, mai suna Ikwuakalom Nwakoro Emeka ne, a ranar Asabar yayin da ake binciken fasinjoji kafin hawa jirgin kamfanin British Airways da yake shirin zuwa Landan.

    Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa mutumin ya yi iƙirarin cewa zai tafi Landan ne domin yin hutu.

    Sai dai yayin binciken kayayyakinsa, jami’ai sun gano hodar iblis da aka ɓoye a cikin kayan abinci.

    Hukumar ta ce nauyin ƙwayar ya kai kilo 11, kuma an ɓoye ta ne a cikin niƙaƙƙen busasshen barkono, sannan aka naɗe ta da takarda.

    Babafemi ya ƙara da cewa wannan kamun na daga cikin jerin samamen da NDLEA ke gudanarwa a faɗin ƙasar nan domin daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi.

    A wani samame na daban kuma a birnin Legas, jami’an NDLEA sun kama wata mata mai suna Maryam Olalowo a wani otal da ke Victoria Island, inda ake zarginta da yunƙurin sayar da giram 89 na hodar iblis da giram 20 na wiwi.

    An kama ta ne tare da ‘ya’yanta guda uku, har da jiri.

    Yayin da ake yi mata tambayoyi, ta shaida cewa ƙwayoyin na mijinta ne, Ibrahim Olatunji.

    Daga bisani, jami’an NDLEA sun yi nasarar kama Olatunji bisani.

    Hukumar ta bayyana cewa ya amsa laifinsa na mallakar ƙwayoyin, sannan bincike ya nuna cewa an taɓa kama shi a shekarar 2015 inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu da rabi kan irin wannan laifi.


    [ad_2]

    Source link

  • Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Birnin Paris

    [ad_1]

    Da safiyar yau Lahadi, tawagogin Sin da Amurka sun gudanar da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya.

    Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumma’a cewa, bisa jagorancin muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a birnin Busan da kuma dukkan tattaunawa ta wayar tarho da aka yi a baya, bangarorin biyu za su yi shawarwari kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da suke ci masu tuwo a kwarya.

    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ne ya jagoranci tawagar kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • Za A Wallafa Makalar Xi Kan Karfafa Samun Ingantaccen Ci Gaban Tattalin Arzikin Teku

    [ad_1]

    Za a wallafa makalar da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya rubuta, game da karfafa samun ingantaccen ci gaban tattalin arzikin teku a mujallar Qiushi, fitowa ta shida a wannan shekara, wadda mujalla ce ta kwamitin kolin JKS.

    Domin ciyar da zamanantar da kasar Sin gaba, yana da muhimmanci a yi amfani da albarkatun teku yadda ya kamata, da karfafa samun ingantaccen ci gaban tattalin arzikin teku, da samar da hanyar da kasar Sin za ta yi amfani da albarkatun teku wajen samun karfin da take muradi, kamar yadda makalar ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • Binciken CGTN: Shawarar Inganta Wayewar Kai A Duniya Ta Kasar Sin Na Kawo Zaman Lumana Ga Duniya Mai Cike Da Hargitsi

    [ad_1]

    Yayin da al’ummomin kasa da kasa, a yanayi mai sarkakiya da hargitsi ke cikin wani hali na sauye-sauye masu zurfi da ba za a iya hasashe a kai ba, shawarar inganta wayewar kai a duniya da kasar Sin ta gabatar tana kawo zaman lumana ga duniya mai cike da tashin-tashina.

    Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN tare da Jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar ta hannun Cibiyar Nazarin Sadarwa ta kasa da kasa ta New Era, wanda ya kunshi mutane 12,302 daga kasashe 41 na duniya, ya nuna cewa, wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi magana mai kyau game da shawarar inganta wayewar kai a duniya da kasar Sin ta gabatar.

    Gaba daya sun yi amannar cewa ainihin ra’ayoyin da shawarar ta kunsa, kamar mutunta bambancin wayewar kai da inganta kyawawan dabi’un dan’adam na gama-gari, suna da ma’ana mai matukar muhimmanci a yanayin kasa da kasa da ake ciki yanzu.

    Kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen sakin mara ga mu’amalar al’adu ta yadda za ta kawar da bakonta, da yadda koyo daga juna zai maye fadace-fadace, kana da yadda zaman tare zai maye jiji-da-kai ko ganin fifiko a kan wasu. A cikin binciken, kashi 90.8% na masu bayyana ra’ayoyi sun yi amannar cewa mutunta bambance-bambancen wayewar kai, muhimmiyar ka’ida ce da ta kamata kasashen duniya su bi.

    Haka nan kashi 77.2% na masu bayyana ra’ayoyin sun yarda cewa babu wata wayewar kai da ta fi wata. Sannan kashi 87.7% sun ce ya kamata a rika tafiyar da duk wayewar kai bisa daidaito, kana daga cikin wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu daga Afirka da yankin Amurka ta Kudu sun nuna amincewa sosai da daidaiton dukkanin wayewar kai, inda wadanda suka amince da hakan suka kai yawan kashi 93.1% da 90.3%, bi-da-bi.

    A ko da yaushe kasar Sin ta yi amannar cewa, zaman lafiya, da ci gaba, da adalci, da dimokuradiyya da ‘yanci, su ne burika na bai-daya ga dukkan al’ummomi. A cikin binciken, kashi 91.8% na masu bayyana ra’ayoyin sun yarda da wannan ra’ayi sosai kuma suka ce ya kamata al’ummomi daban-daban su ba da fifiko ga hadin gwiwar samun nasara ga ko wane bangare a maimakon fito-na-fito da juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link