Category: Latest News

  • Madrid Da PSG Na Shirin Sayen Osimhen

    [ad_1]

    Kungiyoyin Real Madrid da PSG na sa ido kan Victor Osimhen, yayin da ake hasashen yiwuwar sayensa a kasuwar bazara.

    A cewar dan jaridar Turkiyya Ali Naci Küçük, Real Madrid ta sanya Osimhen da Erling Haaland na Manchester City cikin jerin zabin ‘yan wasan da take son dauka a kakar wasa mai zuwa.

    Küçük ya kara da cewa wakilan Real Madrid da PSG sun halarci filin wasa na Rams Park a ranar Talata da ta gabata domin kallon Osimhen yayin wasan Galatasaray a gasar UEFA da Liverpool FC.

    Real Madrid ta dade tana bibiyar Osimhen, kuma a halin da kwangilar wasu ‘yan wasanta ke ciki—musamman Vinícius Júnior—na kara yiwuwar tabbatar wannan ciniki.

    [ad_2]

    Source link

  • Mutum 23 Sun Mutu, 146 Sun Jikkata A Fashewar Bama-bamai A Maiduguri

    [ad_1]

    Aƙalla mutane 23 sun mutu yayin da wasu 146 suka samu raunuka sakamakon jerin fashewar bama-bamai da suka girgiza birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a daren Litinin.

    Fashe-fashen sun faru ne a ƙofar shiga ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), Kasuwar Litinin da kuma yankin Ofishin Wasiku na tsohon birnin.

    • Ko Za A Ga Sauyi Bayan Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka?
    • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 26

    Surajo Abdullahi, mai kula da shiyyar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), wanda ya tabbatar da alkaluman, ya ce an kwashe mutane 169 zuwa asibitoci uku a Maiduguri.

    “Mutane 108 na karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), 20 a Asibitin Umaru Shehu, sannan 17 a Asibitin Kwararru na Maiduguri,” in ji shi.

    [ad_2]

    Source link

  • Kasashen Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Dangane Da Ziyarar Shugaba Trump

    [ad_1]

    Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce kasashen Sin da Amurka na tuntubar juna dangane da ziyarar da shugaban Amurka Donald Trump zai kawo kasar Sin.

    Kakakin ma’aikatar Lin Jian ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Litinin, a lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da batun, inda ya ce hulda tsakanin shugabannin kasashen biyu na da matukar muhimmanci wajen jangorantar dangantakar kasashensu.

    Da aka nemi jin ta bakinsa game da furucin shugaban Amurka kan kasar Sin, game da mashingin Hormuz, Lin Jian ya ce karuwar tashin hankali a mashigin da kewayensa, ya katse hanyoyin jigilar kayayyaki da na cinikin makamashi na kasa da kasa, tare da kawo tsaiko ga zaman lafiya a yankin da ma duniya.

    Kakakin ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da su dakatar da aiwatar da matakan soji nan take, su kaucewa kara ta’azzara rikicin, da kare tashin hankali a yankin daga yin mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (FMM)

    [ad_2]

    Source link

  • Zulum Ya Yi Allah-Wadai Da Fashewar Bam A Maiduguri, Ya Buƙaci A Ƙara Tsaro A Wuraren Ibada

    [ad_1]

    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi Allah-wadai da fashewar bam da ya auku a wasu sassan birnin Maiduguri a yammacin ranar Litinin.

    Zulum, wanda ke ƙasar Saudi Arabia domin gudanar da Umrah, ya bayyana harin a matsayin abin takaici, da rashin imani da kuma zalunci kan fararen hula a cikin watan Ramadan.

    • Borno Ta Kashe Naira Biliyan 100 Kan Samar Da Tsaro A 2025 – Gwamna Zulum
    • Boko Haram Sun Sake Kai Hari Kan Wani Sansanin Sojoji A Borno

    A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya fitar, gwamnan ya buƙaci jama’a su ƙara sanya ido musamman a wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a yayin da ake cikin wannan lokaci na bukukuwa.

    Ya ce zuciyarsa na tare da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka jikkata sakamakon fashewar, yana mai jaddada cewa wannan hari abin Allah-wadai ne kuma ba za a lamunci irin sa ba.

    Gwamnan ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa Sojoji da sauran jami’an tsaro suna kan lamarin, tare da buƙatar mutanen gari su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin nutsuwa tare da sanar da jami’an tsaro duk wani abu da suka ga yana da alamar haɗari.

    [ad_2]

    Source link

  • Fashewar Bam Ta Girgiza Maiduguri, Ana Fargabar Mutane Sun Mutu

    [ad_1]

    An shiga fargaba a birnin Maiduguri bayan wasu fashewar bama-bamai da suka auku a kusa da kasuwar Monday Market Maiduguri da kuma wani wurin tsaro a  Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

    Rahotanni sun ce bama-baman sun fashe kusan lokaci guda da misalin karfe 7:02 na yammacin ranar Litinin, lamarin da ya janyo fargaba a tsakanin mazauna yankin. Ana fargabar cewa wasu mutane sun mutu yayin da da dama suka jikkata sakamakon fashewar.

    • Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Zulum Kan Faɗaɗa Ilimin Fasaha Da Sana’o’i A Borno
    • Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri

    Shugaban sashin ayyuka na Hukumar Kashe Gobara na jihar Borno, Mohammed Kafaran, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun tura jami’ansu zuwa wurin domin tantance halin da ake ciki.

    Shaidu sun ce an garzaya da wasu daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na birnin Maiduguri domin samun kulawar likitoci, yayin da wasu suka ce sun ga gawarwaki a wurin abin fashewar.

    Jami’an agaji da na tsaro na ci gaba da aikin ceto da tantance ɓarnar da fashewar ta janyo, yayin da ake sa ran ƙarin bayani kan lamarin nan gaba.

    [ad_2]

    Source link

  • An ji ƙarar tashin bama-bamai a Maiduguri

    [ad_1]



    Mazauna Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun shiga cikin firgici a yammacin wannan Litinin ɗin sakamakon ƙarar fashewar wasu abubuwa da ake zargin bama-bamai ne.

    Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka tayar da bama-bamai a wasu sassan birnin.

    Rahotanni sun ce mashigar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da shatale-talen Kasuwar Monday da Elkanemi ne wuraren da fashewar ta shafa.

    An samu rahoton cewa an ji ƙarar fashewa ta farko da misalin ƙarfe 7 na yammacin nan, jim kaɗan bayan da aka yi buɗa-baki.

    Kawo yanzu dai babu tabbacin ko an samu asarar rayuka a lamarin wanda ya faru sa’o’i bayan da ’yan ta’adda suka kai hari a wani sansanin soji a Ajilari da ke wajen birnin Maiduguri, inda aka ƙona wata motar sintiri ta sojoji.

    Sai dai sojojin sun yi nasarar daƙile harin tare da kashe wasu daga cikin ’yan ta’addan, yayin da da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.


    [ad_2]

    Source link

  • Tinubu zai tafi ziyarar aiki Birtaniya ranar Talata

    [ad_1]



    A gobe Talata ce ake sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu, zai bar birnin Abuja domin kai wata ziyarar aiki Birtaniya bisa gayyatar Sarkin Ingila, Charles III da matarsa Sarauniya Camilla.

    Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

    Ya ce Tinubu zai tafi tare da uwargidansa, Oluremi Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnati domin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Birtaniya, musamman a fannoni kamar kasuwanci, zuba jari, ƙaura, da musayar al’adu.

    A cewar sanarwar, Sarkin Charles III zai karɓi baƙuncin shugaban Najeriya da matarsa a Windsor Castle daga ranar 18 zuwa 19 ga Maris, inda za su halarci wani baje kolin kayayyakin al’adun sarauta da ke da alaƙa da Najeriya.

    Sanarwar ta ce wannan ita ce ziyarar farko da wani shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37, kuma Tinubu ne shugaban Najeriya na farko da Sarkin Ingila zai karɓa a Windsor Castle.

    Haka kuma, shugaban zai halarci wani zaman rattaba hannu kan yarjejeniyar tallafin kuɗi ta fam miliyan 746 tsakanin Hukumar Kula da Fitar Kudi Ketare ta Birtaniya da Hukumar Tashoshin Ruwan Najeriya da kuma Maaikatar Kudi ta Najeriya, domin gyara manyan tashoshin jiragen ruwa guda biyu a Najeriya, duk a Jihar Legas.

    A yayin ziyarar, Tinubu zai gana da Firaministan Birtaniya Keir Starmer a Fadar Downing Street, inda ake sa ran za su tattauna kan faɗaɗa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

    Ana kuma sa ran ziyarar shugaban na Najeriya za ta ƙare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama da suka shafi kasuwanci, zuba jari, tsaro da haɗin gwiwar al’adu.

    Daga cikin tawagar da za ta rakiyar shugaban ƙasar akwai Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Ministan Shari’a Lateef Fagbemi, Ministan Ma’adanai Dele Alake, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris, da Ministan Kuɗi Wale Edun, da sauran manyan jami’an gwamnati.


    [ad_2]

    Source link

  • Ko Za A Ga Sauyi Bayan Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka?

    [ad_1]

    Tawagogin Sin da Amurka sun fara gudanar da tattaunawa a karo na 6, kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya, jiya Lahadi a birnin a Paris na Faransa, a wani lokaci da harkokin cinikayya a duniya ke cikin yanayi na hargitse saboda matakan son kai da Amurka ke dauka.

    Yayin da kasar Sin ke fadada bude kofarta da kara gyara manufofi ta yadda za ta samar da kyakkyawan muhallin kasuwanci da na ci gaba ga ’yan kasuwa da masu zuba jari na kasashen waje, a daya bangaren, Amurka na ci gaba da bullo da matakan kariyar cinikayya.

    A baya-bayan nan, an ji yadda Amurka ta sanar da kaddamar da bincike mai lamba 301 kan kasashe da yankuna 60, ciki har da kasar Sin, bisa hujjojin rashin daukar mataki kan “Tilasta Kwadago” da “Fitar da Kayayyaki Fiye da Kima”.

    Irin wadannan matakai da Amurka ke ci gaba da bullowa da su daya bayan daya, suna mayar da hannun agogo baya kan irin ci gaban da ake samu da kuma kara hargitsa tsarin cinikayya da haifar da rashin tabbas a duniya.

    Abun da ya kamata ta yi la’akari da shi shi ne, yayin da take kokarin durkusarwa ko dakile abokan cinikayyarta, to tana kara durkusar da kamfanoninta na ci gida, kuma hakan ba zai kai ta ga cimma burinta ba. Misali, wani sakamakon bincike na babban bankin Amurka ya ce, masu sayayya da masu harkokin kasuwanci ne suka biya kaso 90 na haraje-harajen da Amurka ta kakkaba bara. Har ila yau, wani rahoto na cibiyar JP Morgan ya ruwaito cewa, masu matsakaitan kamfanoni a Amurka ne suka fi jin jiki sanadiyyar matakan haraji na kasar.

    Babban misali da ya yi hannun riga da Amurka shi ne manufofin kasar Sin. Tana kara bude kofa da saukaka matakan cinikayya ga baki, amma kuma wannan bai sa ta ragu da komai ba, sai ma karin ci gaba da tagomashi da take samu. Wasu alkaluma da hukumar kididdga ta Sin ta fitar yau Litinin sun nuna yadda harkokin tattalin arziki suka samu tagomashi a farkon bana tsakanin Junairu da Fabrairu, inda karuwar manyan masana’antun kasa ya kai kaso 6.3 bisa dari, ma’aunin samar da sana’ar bayar da hidima ya karu da kaso 5.2, yawan kayayyakin yau da kullum da aka sayar ya kai kudin Sin yuan biliyan 8607.9, karuwar kaso 2.8 bisa dari, dukkansu idan aka kwatanta da makamancin lokaci a bara.

    Ya zama wajibi Amurka ta lura cewa, babu inda rikici zai kai ta. Ya kamata kamar yadda ake da kyakkyawan fata game da tattaunawar karo na 6, a ga sauyi daga gare ta bayan kammaluwarsa. Sauyi mai aminci da dorewa da bangarorin biyu za su kara cin gajiyarsa, har ma da sauran sassan duniya. (Fa’iza Mustapha)

    [ad_2]

    Source link

  • Wakilin Sin Ya Gana Da Manema Labarai Bayan Tattaunawar Tattalin Arziki Da Ciniki Tsakanin Tawagogin Sin Da Amurka

    [ad_1]

    Wakilin tattauna harkokin cinikayya na kasar Sin Li Chenggang, ya gana da manema labarai bayan tattaunawar da aka yi game da tattalin arziki da ciniki tsakanin tawagogin Sin da Amurka a birnin Paris. Inda ya ce tawagogin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi, ta hakika kuma mai ma’ana.

    Ya ce Sin da Amurka sun tattauna game da samar da wani tsarin aiki a tsakaninsu, domin inganta hadin gwiwar ciniki da zuba jari, kuma sun amince cewa kyakkyawar dangantakar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu, za ta amfani kasashen biyu da ma duniya.

    Ya nanata cewa, matsayar kasar Sin kan bincike na Sashe 301, ba ta taba sauya ba, kuma kasar na adawa da irin wannan bincike daga bangare guda. (FMM)

    [ad_2]

    Source link

  • Ba Mu Yi Takamaiman Shiri Don Fuskantar Real Madrid Ba — Guardiola

    [ad_1]

    Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa har yanzu babu wani takamaiman shiri da ƙungiyarsa ta yi dangane da wasan da za ta buga da Real Madrid a gasar UEFA Champions League.

    Manchester City za ta karɓi baƙuncin Real Madrid a filin wasan Etihad da ke birnin Manchester domin buga wasan zagaye na biyu na zagaye na 16 na gasar Zakarun Turai ta bana.

    • Shugabar ALGON Ta Kano Ta Buƙaci Dakatar Da Aiyukan Siyasar Ado Doguwa
    • Real Madrid Ta Shiga Halin Damuwa Bayan Wasanni Uku Ba Tare Da Nasara Ba

    A wasan farko da aka buga a filin Santiago Bernabéu, Manchester City ta sha kashi da ci 3–0 a hannun Real Madrid. Duk da haka, Guardiola ya ce ƙungiyarsa za ta yi iya ƙoƙarinta domin ta rama a gidanta.

    Guardiola ya shaida wa manema labarai cewa, “Har yanzu ban da wani takamaiman shiri kan yadda za mu tunkari wasan da Real Madrid.”

    Tsohon kocin Bayern Munich ya ƙara da cewa ’yan wasansa sun san abin da ya kamata su yi domin kare martabar gida, yana mai cewa City na buƙatar cin kwallaye huɗu ba tare da an zura mata ko ɗaya ba domin ta kai zagayen kwata-fainal na gasar.

    [ad_2]

    Source link