Category: Latest News

  • Zaɓen 2027: A raba wa ’yan Najeriya shinkafa — Tinubu

    [ad_1]



    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ƙungiyar da ke mara masa baya domin sake tsayawa takara a zaɓen 2027 mai suna, ‘Renewed Hope Ambassadors’ da ta raba wa ’yan Najeriya shinkafa a wannan lokaci da Musulmi ke azumin watan Ramadana da kuma azumin mabiya addinin Kirista na Lenten.

    RFI ya ambato Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma wanda ke jagorancin ƙungiyar yana bayyana hakan tare da sanar da cewar ’ya’yan ƙungiyar za su aiwatar da shirin a kowane sashe na ƙasar.

    Uzodinma ya ce umarnin ya nuna irin tausayin da shugaban ƙasa ke da shi da kuma karamci ga ’yan ƙasa tare da neman haɗin kan jama’a, a daidai lokacin da su ke sadaukar da rayukan su wajen ibada da taimako da kuma kula da juna.

    Sai dai wasu na kallon wannan yunƙuri a matsayin wani shirin kamfe na zaɓe mai zuwa gabanin kaɗa gangar siyasa, la’akari da cewar wannan rabon ana yin sa a tsakanin magoya bayan jam’iyya.

    Raba shinkafa ga talakawa ya zama ruwan dare a ƙarƙashin gwamnatin APC tun da ta karɓi mulkin Najeriya a shekarar 2015.

    Yanzu haka ’yan siyasa daga jam’iyyu daban daban na can su na raba wa jama’a shinkafar domin rage musu raɗadin halin ƙunci da suka samu kansu da zummar samun goyan bayan su lokacin zaɓuɓɓuka.

    A baya gwamnatin Tinubu ta sha sanar da shirye-shiryen tallafa wa jama’a domin rage tasirin tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da ke addabar ƙasar, ciki har da rabon hatsi daga rumbun ajiyar gwamnati da kuma wasu shirye-shiryen tallafin jin ƙai.

    Sai dai masu sukar gwamnati na cewa irin waɗannan rabon kayan abinci na ɗan lokaci ne kawai, kuma ba su magance matsalolin tattalin arziki da talauci da yawancin ’yan Najeriya ke fuskanta ba.


    [ad_2]

    Source link

  • Inshorar Lafiya A Matakin Farko Ta Sin Ta Karade Mutane Biliyan 1.33

    [ad_1]

    Ya zuwa karshen shekarar 2025, sama da mutane biliyan 1.33 ne aka shigar da su cikin tsarin inshorar kiwon lafiya a matakin farko ta kasar Sin, yayin da adadin kason da aka karade ya kiyaye matsayinsa ba tare da tangarda ba da kusan kashi 95 cikin dari.

    Hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta kasar Sin ta ce, a shekarar 2025, asusun inshora na matakin farko, ciki har da inshorar haihuwa, ya samu makudan kudin shiga kimanin yuan triliyan 3.59, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 520, kana an kashe tiriliyan uku daga cikin asusun. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • Dangote Da GCL Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Masana’antar Taki A Habasha

    [ad_1]

    Kamfanin Dangote da kamfanin makamashi na ƙasar China mai suna GCL Group sun ƙulla wata yarjejeniya ta shekaru 25 wadda kuɗinta ya kai dala biliyan 4.2 domin samar da iskar gas ga wani babban aikin masana’antar taki da za a gina a Ethiopia.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar, kamfanin GCL zai riƙa samar da iskar gas ga sabuwar masana’antar urea mai ƙarfin samar da tan miliyan uku a duk shekara da Dangote ke shirin ginawa. Ana sa ran masana’antar wadda kuɗinta ya kai dala biliyan 2.5 za ta fara aiki a shekarar 2029, inda aka tsara mallakar kashi 60 ga Dangote da kuma kashi 40 ga Ethiopian Investment Holdings.

    • Matatar Man Fetur Ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Da Dizal
    • Matatar Dangote Ta Sake Ƙara Farashin Fetur Zuwa ₦1,175

    Da zarar an kammala aikin, masana’antar za ta zama mafi girma a yankin Gabashin Afirka wajen samar da taki, inda za ta wadatar da buƙatar taki ta ƙasar Habasha tare da samar da shi ga ƙasashe maƙwabta.

    Rahotanni sun ce za a samo iskar gas din ne daga filin gas na Calub Gas Field a yankin Ogaden, sannan a riƙa kai shi ta bututun mai mai tsawon kilomita 108 zuwa sabuwar masana’antar taki da za a gina a garin Gode.

    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce wannan haɗin gwuiwa zai taimaka wajen samar da tsarin haɗa masana’antar makamashi da samar da abinci a Afirka, tare da rage dogaro da shigo da taki daga ƙasashen waje.

    [ad_2]

    Source link

  • Sin: Bincike Mai Lamba 301 Da Amurka Ta Yi Ya Bata Tsarin Tattalin Arzikin Duniya

    [ad_1]

    Kwanan baya, wani kakakin ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ya amsa tambayar da dan jarida ya yi masa game da sanarwar da ofishin wakilin harkokin cinikayyar kasar Amurka ya fidda, cewar zai kaddamar da bincike mai lamba 301 kan kasashe da yankuna guda 60, ciki har da kasar Sin, bisa hujjar “Ba su daina fitar da hajojin da aka samar ta hanyar tilasta wa wasu yin aiki ba.”

    Kakakin ya ce, kafin haka, kasar Amurka ta taba daukar matakan hana cinikayyar kasar Sin sau da dama, bisa karyar da ta yi game da “tilasta wa wasu yin aiki”, kasar Sin ta kuma bayyana matsayinta kan batun sau da dama, tana kuma adawa da tilasta wa wani ko wasu yin aiki a ko da yaushe, kana ta zartas da yarjejeniyoyin ’yan kwadago na duniya guda 28, tare da kafa cikakken tsari na dokar kwadago.

    Har zuwa yanzu, kasar Amurka ba ta zartas da kulla yarjejeniyar hana tilasta wa wani ko wasu yin aiki ta shekarar 1930 ba, kuma ta ki bin manufofin duniya. A sai daya kuma, sau da dama ta siyasantar da batun tilasta wa wani ko wasu yin aiki. A wannan karo kuma, kasar Amurka ta kaddamar da bincike mai lamba 301 domin kafa kariyar ciniki.

    A halin yanzu, kasar Sin da kasar Amurka suna gudanar da tattaunawar cinikayya ta sabon zagaye a birnin Paris na kasar Faransa, kasar Sin tana son yin shawarwari da kasar Amurka kan batun, domin sa-kaimi ga kasar don ta gyara kuskurenta. Haka kuma, kasar Sin za ta mai da hankali kan binciken da kasar Amurka ta kaddamar, tare da daukar matakai da suka dace domin kare ikonta yadda ya kamata. (Mai Fassara: Maryam Yang)

    [ad_2]

    Source link

  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 26

    [ad_1]

    Mota Sahur (Fajr/Imsak) Iftar (Maghrib)
    Abuja 05:07 AM 07:04 PM
    Idan 05:02 AM 06:58 PM
    Kano 05:03 AM 07:03 PM
    Kaduna 05:07 AM 07:06 PM
    Legas 05:21 AM 07:23 PM
    Maiduguri 04:58 AM 06:43 PM
    Sokoto 05:20 na safe 07:16 PM
    Fatakwal 05:12 AM 07:05 PM

    [ad_2]

    Source link

  • Manyan Ma’aunan Tattalin Arzikin Sin Sun Karu Daga Janairu Zuwa Fabrairu

    [ad_1]

    Yau Litinin, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai, inda ya yi bayani game da yanayin gudanarwar harkokin tattalin arzikin kasa daga watan Janairu zuwa Fabrairun bana.

    A yayin taron, kakakin hukumar kididdigar kasar Sin ya ce, daga watan Janairu zuwa Fabrairun bana, yanayin samar da guraben ayyukan yi da farashin kayayyaki sun kiyaye samun ci gaba ba tare da tangarda ba, a sa’i daya kuma, sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ya bunkasa kamar yadda aka yi fata, hakan ya sa, aka bude wani babi mai kyau ta fuskar tattalin arziki a farkon bana.

    Haka zalika, daga watan Janairu zuwa watan Fabrairu, yawan karuwar manyan masana’antun kasa ya kai kaso 6.3 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kana, ya karu da kaso 1.1 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Disambar bara. Game da sana’ar ba da hidima kuma, ma’aunin samarwa na sana’ar ya karu da kaso 5.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, wanda ya karu da kaso 0.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Disambar bara.

    Ban da haka kuma, daga watan Janairu zuwa watan Fabrairu, yawan kayayyakin yau da kullum da aka sayar ya kai zunzurutun kudi Yuan biliyan 8607.9, adadin da ya karu da kaso 2.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, wanda ya karu da kaso 1.9 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Disambar bara. (Mai Fassara: Maryam Yang)

    [ad_2]

    Source link

  • Tinubu Ya Rantsar Da Taiwo Oyedele A Matsayin Ƙaramin Ministan Kuɗi

    [ad_1]

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin Karamin Ministan Kudi a ranar Litinin a Abuja.

    Oyedele, wanda ya taɓa zama shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan sauye-sauyen haraji, ya karbi rantsuwar ne bayan naɗa shi a wannan muƙami. Ya maye gurbin Doris Uzoka-Anite, wacce aka mayar da ita Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi.

    • Mun Ceto Nijeriya Yayin Da Take Gab Da Dilmiyewa – Tinubu
    • Tinubu Da Shettima Sun Yi Buɗa-Baki Da Sarakuna Da Malaman Addini A Villa

    A baya dai shugaban ƙasa Tinubu ya aikewa da majalisar dattawa sunan Oyedele domin tantancewa da tabbatar da naɗin nasa, bayan majalisar dokoki ta amince da wasu dokokin gyaran tsarin haraji da kwamitinsa ya jagoranta.

    Taiwo Oyedele, ɗan asalin garin Ikaram-Akoko a Jihar Ondo State, masanin tattalin arziƙi ne mai shekaru 50 da ƙwarewa a fannin kuɗi, da haraji da manufofin tattalin arziƙi. Ya fara karatunsa a Yaba College of Technology inda ya samu HND a fannin lissafi da kuɗi, sannan daga baya ya samu digiri a Applied Accounting daga Oxford Brookes University a United Kingdom.

    Kafin shiga aikin gwamnati, Oyedele ya shafe shekaru 22 yana aiki da kamfanin PricewaterhouseCoopers inda ya fara aiki a 2001 har ya zama jagoran harkokin haraji na Afirka. Haka kuma yana koyarwa a Babcock University a Jihar Ogun State, sannan yana matsayin baƙo mai bincike a Lagos Business School.

    [ad_2]

    Source link

  • Jama’ar gari sun kashe ’yan bindiga 3 a Sakkwato

    [ad_1]



    Wasu mazauna da ke aikin sa-kai a ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, sun kashe wasu ’yan bindiga uku a wani artabu da ya faru a ranar Lahadi.

    Rahotanni daga yankin sun ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka kurɗo ta wasu hanyoyi da ke wajen gari domin yi wa al’ummar shigar ba-zata.

    Wani jagoran al’umma a ƙauyen wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun ɓuya a kan bishiyoyi da ke kusa da maƙabartar ƙauyen, yayin da wasu suka shiga wani gida a wajen gari, inda suka yi karo da ’yan sa-kai da ke sintiri a yankin.

    A cewarsa, ’yan bindigar sun kashe wani ɗan sa-kai guda ɗaya, lamarin da ya fusata kafin sauran ’yan sa-kan mayar da martani suka kashe uku daga cikin maharan a yayin musayar wuta.

    Ya ƙara da cewa daga bisani maharan sun kashe wani ɗan sa-kai da ya ɓuya a cikin wani gida.

    “Sun kashe ’yan sa-kai biyu, Umar Ibrahim da Abubakar Abdullahi na Mumini. Mu kuma mun kashe ’yan bindiga uku a yayin artabun,” in ji shi.

    Wasu mazauna yankin sun ce maharan sun zo ne a ƙafa cikin sanɗa, bayan sun ajiye baburansu a wajen gari, sannan bayan artabun sun yi amfani da jaki wajen ɗaukar gawarwakin ’yan uwansu da aka kashe kafin su tsere.

    Aminiya ta ruwaito cewa wannan lamarin dai ya jefa mazauna ƙauyen cikin fargabar dawowar ’yan bindigar domin ɗaukan fansa, inda wasu suka yi yunƙurin barin garin, sai dai shugabannin al’umma da kwamitin tsaron ƙauyen sun shawo kansu da su zauna.

    Mazauna sun koka kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga a yankin, da suka yi zargin cewa Bargaja na daga cikin ƙauyukan da ba su da jami’an tsaro duk da irin barazanar da suke fuskanta.

    Sun yi kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su tura jami’an tsaro zuwa ƙauyen domin daƙile hare-haren da ke aukuwa akai-akai.

    Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato, Ahmad Rufai, ya ce rundunar na da masaniya kan harin da kuma asarar rayukan da aka yi.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Sin Ta Aika Da Sakon Taya Murna Ga ‘Yan Wasan Kasar Da Suka Halarci Gasar Paralimpics Karo Na 14

    [ad_1]

    Kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta Sin, sun aika da sakon taya murna ga tawagar ‘yan wasa masu bukata ta musamman ta Sin da suka halarci gasar wasannin Paralimpics ta lokacin hunturu karo na 14.

    Sakon wanda aka aika jiya Lahadi ya bayyana cewa, a gasar wasannin Paralimpics na lokacin hunturu karo na 14 da aka kammala, ‘yan wasa masu bukata ta musamman na Sin sun lashe lambobin yabo 44, ciki har da zinare 15, azurfa 13 da tagulla 16, inda suka zo na farko a yawan lambobin zinare da kuma yawan lambobin yabo gaba daya. Sun samu nasara a fagen wasanni da kuma nuna sadaukarwa, kuma sun samar wa kasar Sin da al’ummarta karin daraja da daukaka a fagen wasanni.

    A cikin sakon nasu, kwamitin tsakiyar JKS da majalisar gudanarwa ta Sin sun yaba wa ‘yan wasan masu bukata ta musamman na Sin da suka nuna kyakkyawan hali na jajircewa da dogaro da kai da kuma kyakkyawan fatansu na samun ci gaba a sabon zamani, wanda ya kara ingiza kishin kasa da ruhin gwagwarmaya na ‘yan uwantakar Sin a cikin gida da wajen kasar. Matakin da ya karfafa musu gwiwar kara kokarin hidima ga kasa, da kuma samar da karin nasarorin wasanni.(Amina Xu)

    [ad_2]

    Source link

  • Fasinjoji sun jikkata a hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

    [ad_1]



    Fasinjoji da dama sun jikkata bayan wani jirgin ƙasa da ke jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga layin dogo sakamakon karo da wani abu a kan hanyarsa.

    Lamarin ya faru ne yau Litinin a kusa da Asham a kan layin dogon da ke haɗa Abuja da Kaduna, lamarin da ya jefa fasinjojin cikin fargaba.

    Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa (NRC), Kayode Opeifa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura tawagar agajin gaggawa nan take bayan samun rahoton hatsarin.

    Binciken farko ya nuna cewa jirgin ya kauce daga hanyarsa ne bayan ya yi karo da wani abu a kan layin dogon, sai dai har yanzu jami’ai ba su fitar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ba.

    Rahotanni sun ce wasu daga cikin fasinjojin sun samu raunuka daban-daban, kuma an kwashe su zuwa cibiyar lafiya da ke tashar jirgin ƙasa ta Idu da ke Abuja domin samun kulawar mahukuntan lafiya.

    Hukumar NRC wadda ta tabbatar da faruwar hatsarin da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar wannan Litinin, ta ce babu wanda ya rasa ransa a hatsarin.

    Wasu hotuna da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna wasu daga cikin taragon jirgin da suka lalace, yayin da ma’aikatan jirgin ke duba inda abin ya faru, tare da fasinjojin da suka sauka daga jirgin suna jiran a kai su wuri mai aminci.

    Hukumar NRC ta ce injin ɗaya daga cikin taragon jirgin da kuma mai ɗaukar fasinja ne suka samu matsala sakamakon tangardar haɗin sassan jirgin.

    Opeifa ya ce an gaggauta aiwatar da matakan ceto tare da tura ƙwararrun jami’an fasaha zuwa wurin, yayin da Hukumar Tabbatar da Aminci (SIB) ke gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

    Ya kuma tabbatar da cewa jirgin ya isa tashar Idu da misalin ƙarfe 10:39 na safe, inda ya samu jinkiri na mintuna 38 saboda cire sassan jirgin da hatsarin ya shafa.

    Hukumar ta jaddada cewa tsaron fasinjoji shi ne babban abin da ta sa a gaba, tare da tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan jirgin cikin aminci.


    [ad_2]

    Source link