Category: Latest News

  • Kungiyar Nazarin Ci Gaban Hakkokin Dan Adam Ta Kasar Sin Ta Kira Taro Mai Taken “Kawar Da Rashin Adalci Don Neman Samun Hakkin Ci Gaba” A Geneva

    [ad_1]

    A yayin taro na 61 na majalisar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHRC), kungiyar nazarin ci gaban hakkokin dan Adam ta kasar Sin ta kira wani taro mai lakabin “kawar da rashin adalci don neman samun hakkin ci gaba” a ranar 13 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda kwararru da masana na kasar Sin da na sauran kasashe suka tattauna kan yadda za a bai wa kowane dan Adam hakkin ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkiren dabaru, yayin da duniyarmu ke fuskantar matsaloli da dama da suka shafi tattalin arziki da zaman rayuwar dan Adam da muhalli da sauransu.

    Mahalarta taron sun ce, bai wa kowane dan Adam hakkin ci gaba shi ne muhimmin ginshikin samun hakkin ci gaba na dan Adam. Shawarar samar da ci gaba ga duk duniya da kasar Sin ta gabatar, mai kunshe da ka’idar amfanar da kowa tare da nuna hakuri, ta kara zurfafa ma’anar akidar tabbatar da adalci wajen samun hakkin ci gaba. Taron ya kuma yi kira ga sassan kasa da kasa, su inganta hadin gwiwa, da kawar da rashin adalci a bangaren tsari, da kokarin raya tsarin jagorancin duniya mai adalci da kuma dorewa. (Murtala Zhang)

    [ad_2]

    Source link

  • Dalilin da ya sa ban ɗaga hankalina ba lokacin da na rasa muƙamai — Sanusi II

    [ad_1]



    Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa bai ɗaga hankalinsa ba bayan rasa manyan muƙamai biyu a rayuwarsa.

    Sanusi II, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron lakcar azumi ta shekara-shekara ta Fola Adeola (Fola Adeola Annual Ramadan Lecture).

    A wajen taron, ya yi magana kan muhimmancin haƙuri da kuma yadda dogaro da Allah Ya taimaka masa wajen shawo kan ƙalubalen da ya fuskanta.

    Ya ce mutane da dama suna kuskuren danganta nasara da iko ga ’yan adam, maimakon su gane cewa Allah ne kaɗai ke juya al’amuran yadda Ya so.

    “Sau da yawa a rayuwarmu muna danganta abubuwa ga mutane, alhali su ma halittu ne kawai,” in ji Sanusi.

    “Idan ka tuna cewa yanayin rayuwa ba ya dawwama, kuma Allah ne ke sauya al’amura, hakan zai taimaka maka ka jure kuma ka daidaita halayenka.”

    Ya gargaɗi mutane da kada su ƙasƙantar da kansu domin neman yardar masu iko.

    A cewarsa, wasu mutanen kan ƙasƙantar da kansu ne saboda tunanin cewa wani mutum ne ke da iko a kan makomarsu.

    Sanusi II, ya kafa misali da rayuwarsa domin nuna yadda al’amura ke sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci.

    Ya ce: “An dakatar da ni daga muƙamin Gwamnan Babban Banki, bayan watanni uku kuma na zama Sarki. Bayan wasu shekaru aka sauke ni daga sarauta, amma bayan shekaru huɗu na sake dawowa.

    “Yanzu ina cikin fada, a kan karagar mulkina… A ƙarshe dai, dogaro ga Allah ne ke yin komai. Kada ka firgita.”

    Ya ƙara da cewa lokacin da yake rayuwa bayan fitar da shi daga Kano, ya ba shi damar mayar da hankali kan karatu da kuma bunƙasa ci gaban gobensa.

    Sanusi II, ya riƙe muƙamin Gwamnan CBN daga shekarar 2009 zuwa 2014.

    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne, ya tsige shi daga karagar mulki a shekarar 2020.

    Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da shi kan Sarautar Kano a shekarar 2024.


    [ad_2]

    Source link

  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 25

    [ad_1]

    Mota Sahur (Fajr/Imsak) Iftar (Maghrib)
    Abuja 05:08 na safe 07:03 PM
    Idan 05:03 AM 06:57 PM
    Kano 05:04 AM 07:02 PM
    Kaduna 05:08 na safe 07:05 PM
    Legas 05:22 AM 07:22 PM
    Maiduguri 04:59 AM 06:42 PM
    Sokoto 05:21 AM 07:15 PM
    Fatakwal 05:13 AM 07:04 PM

    [ad_2]

    Source link

  • Masanin Zimbabwe: Manufar Soke Harajin Kasar Sin Ga Afirka Za Ta Kara Habaka Fitar Da Kayayyaki Zuwa Ketare

    [ad_1]

    Wani masani na kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, manufar soke harajin kwastam ta kasar Sin ga kasashen Afirka 53, za ta bayar da damammaki ga ‘yan Afirka masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare.

    Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ranar Jumma’ar da ta gabata, mai fashin baki kan harkokin tattalin arziki na kasar Zimbabwe, kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Dereck Goto, ya ce, manufar tana nuna gagarumin sauyin tsarin dangantakar cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka.

    A watan Fabrairun da ya gabata, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta fara cikakkiyar aiwatar da manufar soke harajin kwastam ga kasashen Afirka 53 masu huldar jakadanci da ita daga ranar 1 ga watan Mayun bana.

    Goto ya ce sabon matakin da kasar Sin ta dauka na da matukar muhimmanci a fannin siyasar yankuna. Ta hanyar bayar da damar soke biyan harajin kwastam a sassan nahiyar Afirka, kasar Sin tana kara karfafa matsayinta na abokiyar kasashe masu tasowa, tare da bude hanyoyin samun ci gaba masu tushe na cinikayya.

    Ya kara da cewa, “A takaice dai, ga kasar Zimbabwe da sauran abokan hulda na Afirka, manufar soke harajin kwastam ta zarce wata alama ta karamci. Gayyata ce ta zurfafa karfin masana’antu, da fadada fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da kuma tabbatar da hadewa da daya daga cikin manyan kasuwannin tattalin arzikin duniya. Babban abin da ya fi zama mai muhimmanci a yanzu shi ne yadda masu samar da kayayyaki na Afirka kimtsa kansu yadda ya kamata domin cin gajiyar damar da aka samu.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Kano Ta Rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Ta Haɗe Ta Da Ma’aikatar Ilimi

    [ad_1]

    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi a wani mataki na sake fasalin tsarin gudanar da ilimi a jihar.

    Sanarwar wacce mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu ranar Lahadi ta bayyana cewa bayan wannan sauyi, sabuwar ma’aikatar za ta ci gaba da aiki da sunan Ma’aikatar Ilimi, inda za a kafa wani sashen kula da Ilimi Mai Zurfi a cikinta domin sa ido kan jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare.

    • Kwankwaso Bai Taɓa Neman Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa Ba – NNPP
    • Shugabar ALGON Ta Kano Ta Buƙaci Dakatar Da Aiyukan Siyasar Ado Doguwa

    Sanarwar ta kara da cewa dukkan hukumomi da ke ƙarƙashin tsohuwar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, ciki har da Kano State Scholarship Board, za su koma ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi, yayin da jami’o’in gwamnati da sauran manyan cibiyoyin ilimi za su kasance ƙarƙashin sabon sashin kula da Ilimi Mai Zurfi.

    Gwamnatin jihar ta ce wannan mataki na daga cikin shirin gyaran ɓangaren ilimi domin rage maimaituwar ayyuka, da inganta haɗin kai wajen tsara manufofi da kuma rage kashe kuɗin gudanar da gwamnati.

    Gwamna Yusuf ya jaddada cewa sauyin zai taimaka wajen ƙara inganci da gaskiya a tafiyar da ɓangaren ilimi tare da tabbatar da cewa ana aiwatar da manyan sauye-sauye da za su farfado da ilimi a jihar domin amfanin matasa na gaba.

    [ad_2]

    Source link

  • Tsohon ministan sufuri ya sauya sheƙa daga PDP zuwa ADC a Sakkwato

    [ad_1]



    Tsohon Ministan Sufuri, Alhaji Yusuf Suleiman, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa ADC.

    Ya bayyana hakan ne cikin wata takarda da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓarsa ta Isa ta Arewa a Ƙaramar Hukumar Isa, a Jihar Sakkwato.

    Alhaji Yusuf Suleiman, ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Matasa da Wasanni a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

    Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne saboda rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar PDP.

    Ya ce: “Na yanke shawarar barin PDP ne saboda rikice-rikicen shugabanci da jam’iyyar ke fama da su, waɗanda har yanzu ba a samu mafita a kansu ba.”

    Ya ƙara da cewa bayan shekaru da dama yana cikin jam’iyyar kuma yana bayar da gudunmawa ga ci gabanta, ya ga cewa lokaci ya yi da zai fice.

    Suleiman, ya ce ya koma jam’iyyar ADC ne domin ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa da kuma taimakawa wajen magance matsalolin rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi.


    [ad_2]

    Source link

  • Togo Na Neman Ƙarin Wutar Lantarki Da Take Siya Daga Nijeriya

    [ad_1]

    Togo ta bayyana sha’awarta na ƙara yawan wutar lantarki da take saya daga Nigeria ta hannun ‘Niger Delta Power Holding Company’ (NDPHC), domin samar da wutar ga sabbin wuraren da ake buƙatar wutar lantarkin a kasar.

    An bayyana wannan buƙatar ne yayin wani muhimmin taro tsakanin shugabannin NDPHC da wata tawaga daga kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Togo mai suna ‘Compagnie Énergie Électrique du Togo (CEET)’.

    • Nijar Ta Haramta Fitar Da Dabbobi Ketare Don Takaita Karancinsu A Cikin Gida
    • Wane Irin Tanadi Kuka Yi Wa Sallah Karama A Wannan Lokacin?

    Tawagar ta samu jagoranci daga babban daraktan kamfanin, Débo-K’mba Barandao, wanda ya kai ziyara ga shugabannin NDPHC domin ƙarfafa haɗin gwiwar dake tsakaninsu tare da duba yiwuwar faɗaɗa kasuwancin wutar lantarki tsakanin ƙasashen.

    Kamfanin CEET, wanda hedikwatarsa ke Lomé, a halin yanzu yana sayen kusan megawatt-hours 75 (MWh) na wutar lantarki daga NDPHC. Wannan tsarin samar da wutar ya taimaka wa Togo wajen tabbatar da daidaiton samar da lantarki da kuma tallafawa harkokin tattalin arziƙin ƙasar.

    Wutar lantarkin da ake shigowa da ita daga Nijeriya tana taimakawa wajen samar da ingantacciyar wuta mai araha ga gidaje, kasuwanni da kuma cibiyoyin gwamnati a Togo.

    [ad_2]

    Source link

  • IRGC ta sha alwashin kashe Netanyahu yayin da yaƙin Iran ya tsananta

    [ad_1]



    Rundunar dakarun juyin juya hali ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta Iran ta yi barazanar kashe Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yayin da yaƙi ya tsananta a Gabas ta Tsakiya.

    Barazanar ta fito ne a wata sanarwa da rundunar ta fitar a safiyar Lahadi, inda ta ce za ta ci gaba da bibiyar Netanyahu har sai ta “ga bayansa” kafin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a yankin.

    A daren Asabar zuwa safiyar Lahadi, Iran ta harba makamai masu linzami zuwa tsakiyar Isra’ila, lamarin da ya haddasa fashe-fashe masu ƙarfi a Tel Aviv, kamar yadda wasu bidiyoyi da suka yaɗu a kafafen sada zumunta suka nuna.

    Sai dai Isra’ila ta ce tsarin yi wa sararin samaniyarta garkuwa ya yi nasarar tare yawancin makaman da Iran ta harba, duk da cewa wasu rahotanni sun nuna an samu ɓarna a wasu sassan ƙasar.

    Sabbin hare-haren na zuwa ne bayan Amurka ta kai farmaki a birnin Isfahan na Iran da kuma tsibirin Kharg, inda rahotanni suka ce mutum 16 da ke aiki a matatar mai suka mutu.

    Tsibirin Kharg na ɗaya daga cikin muhimman wuraren da Iran ke fitar da man fetur, kuma ana kallonsa a matsayin muhimmin ginshiƙi ga tattalin arzikin ƙasar.

    Iran ta yi iƙirarin cewa Amurkan ta yi amfani da sararin samaniyar Haɗɗdiyar Daular Larabawa wajen kai mata harin a Kharg, sai dai har kawo yanzu Washington da Abu Dhabi ba su ce komai game da zargin ba, yayin da aka ga yadda Tehran ta kai hari wasu sassa na Dubai a jiyan.


    [ad_2]

    Source link

  • NDLEA Ta Kama Tsoho Da Yunƙurin Safarar Hodar Iblis A Filin Jirgin Sama Na Abuja

    [ad_1]

    Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun kama wani dattijo mai shekaru 74, Ikwuakalom Emeka, a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bisa zargin yunƙurin safarar kilo 11 na hodar iblis da aka ɓoye cikin kayan abinci yayin da yake shirin tafiya zuwa Ingilla.

    An kama tsohon mutumin ne a sashen bincike na filin jirgin yayin da yake kokarin hawa jirgin ‘British Airways’ mai lamba BA082 wanda zai nufi Heathrow Airport a Landan, ranar Asabar, 14 ga Maris, 2026.

    A cewar sanarwar da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, binciken jakunkunan Emeka ya nuna an ɓoye hodar iblis ne acikin barkono.

    [ad_2]

    Source link

  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 20 a Filato

    [ad_1]



    Aƙalla mutum 20 ne suka mutu a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani ƙauye a Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, kamar yadda wata ƙungiyar raya yankin ta bayyana.

    Ƙungiyar Kanam Development Association (KADA) ta ce harin ya faru ne ranar Juma’a lokacin da maharan suka yi wa sojojin da ke sintiri a yankin kwanton ɓauna.

    Sanarwar ta ce a yayin musayar wuta da ta biyo bayan harin, mutum 12 daga cikin jami’an tsaro sun rasa rayukansu, tare da wasu mutum takwas daga cikin mazauna yankin da suka haɗa kai da su domin kare al’ummarsu.

    Kazalika, ’yan bindigar sun afka wa wata al’umma da ke kusa, inda suka kwashe dukiya ciki har da shanu.

    KADA ta ce hare-haren sun ƙara jefa mazauna karkara cikin mawuyacin hali, domin a baya ma yankunan sun sha fama da hare-hare da sace-sacen mutane domin neman kuɗin fansa.

    A Najeriya dai, ƙungiyoyin ’yan bindiga na yawan kai hare-hare a yankunan karkara, inda suke sace mutane da kwasar dukiya.


    [ad_2]

    Source link