NDLEA Ta Kama Tsoho Da Yunƙurin Safarar Hodar Iblis A Filin Jirgin Sama Na Abuja
[ad_1]
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun kama wani dattijo mai shekaru 74, Ikwuakalom Emeka, a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bisa zargin yunƙurin safarar kilo 11 na hodar iblis da aka ɓoye cikin kayan abinci yayin da yake shirin tafiya zuwa Ingilla.
An kama tsohon mutumin ne a sashen bincike na filin jirgin yayin da yake kokarin hawa jirgin ‘British Airways’ mai lamba BA082 wanda zai nufi Heathrow Airport a Landan, ranar Asabar, 14 ga Maris, 2026.
A cewar sanarwar da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, binciken jakunkunan Emeka ya nuna an ɓoye hodar iblis ne acikin barkono.
[ad_2]
Source link