Category: Latest News

  • Gwamnatin Trump ta caccaki CNN kan rahotannin yaƙin Iran

    [ad_1]



    Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta caccaki kafar yaɗa labarai ta CNN kan yadda take kawo rahotanni dangane da yaƙin da ƙasar ke fafatawa da Iran, lamarin da ke ƙara buɗe sabon babi a rikici tsakanin Fadar White House da kafafen yaɗa labarai.

    Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth ya yi kakkausar suka kan wani rahoton CNN da ya ce Washington ba ta yi tsammanin Iran tana da ƙarfin kawo cikas a zirga-zirgar man fetur a Mashigar Hormuz ba.

    Hegseth ya bayyana rahoton a matsayin wanda “ba shi da tushe”, yana mai cewa yana fatan shugaban kamfanin Paramount Skydance, David Ellison, zai kammala saye kafar domin samun abin da ya kira “kafofin watsa labarai masu kishin ƙasa”.

    Kamfanin Paramount Skydance na shirin karɓe ikon kamfanin Warner Bros. Discovery, wanda a halin yanzu shi ne mai CNN, bayan ya sha gaban Netflix a takarar sayen kamfanin.

    A nata ɓangaren, kakakin Fadar White House Karoline Leavitt ta ce rahoton CNN game da yiwuwar rufe Mashigar Hormuz “ƙarya ce ɗari bisa ɗari”, tana mai cewa Ma’aikatar Tsaron Amurka ta daɗe tana shirya wa irin wannan barazana.

    Sai dai shugaban CNN Mark Thompson ya mayar da martani da cewa tashar za ta ci gaba da faɗar gaskiya ga masu kallonta, duk da matsin lamba ko suka daga ɓangaren ’yan siyasa.

    Rikicin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da kai hare-haren soja kan Iran a wani farmaki da ake kira Operation Epic Fury, wanda ya ƙara dagula rikicin a Gabas ta Tsakiya.


    [ad_2]

    Source link

  • An kashe sojoji biyu yayin rikicin matasa a Kuros Riba

    [ad_1]



    Wasu sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin da suke ƙoƙarin raba rikicin da ya ɓarke tsakanin matasan ƙauyukan Isabang da Alesi da ke Ƙaramar Hukumar Obubra a Jihar Kuros Riba.

    Rahotanni sun ce rikicin ya faru ne a ranar Asabar, bayan wata takaddama da ta fara tun makon da ya gabata tsakanin matasan ƙauyukan biyu.

    An ce lamarin ya samo asali ne bayan da wasu matasa suka lakaɗa wa wani mutum mai suna Ibrahim Musa duka a wani wurin binciken ababen hawa da jami’an tsaro ke aiki.

    Wani jami’in tsaro mai suna Joshua Erin ya sanar da sojojin Bataliya ta 245 da ke barikin Ejor game da rikicin, inda aka tura sojoji domin kwantar da tarzomar.

    Sai dai yayin ƙoƙarin da suke yi na sasanta rikicin, matasan da ke faɗa suka kai hari kan sojojin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji biyun nan take.

    Mutuwar sojojin ta haddasa tashin hankali a yankin, inda aka ce wasu sojoji sun mayar da martani, abin da ya janyo ƙarin asarar rayuka da jikkatar wasu.

    Rahotanni sun ce wasu matasa biyu — Christopher Agara da Ogobi Egbe — sun mutu a artabun, yayin da wasu da dama suka jikkata aka kai su asibiti domin samun kulawa.

    Lamarin ya tilasta wasu mazauna yankin tserewa daga gidajensu domin fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo.

    Sai dai rahotanni sun ce zuwa yanzu hankula sun fara kwanciya, yayin da al’ummar yankin suka koma gudanar da harkokinsu bayan lafawar rikicin.


    [ad_2]

    Source link

  • Illolin Tsarki Da Sabulu Ga Mace (2)

    [ad_1]

    A gaskiya, wasu daga cikinsu na amfani da hannayensu wajen cusa wadannan magungunan cikin jikinau , abin da ba su sani ba shine, idan su ka dauki tsawon lokaci su na aikata hakan, sai ya haifar mu su da matsewar jikinsu fiye da kima. Mun sha samun matsalolinan.

    “Idan mace ta samu kanta cikin wannan matsala, don warkar da ita akwai bukatar a yi ma ta aikin tiyata nau’i daban-daban ko kuma ayi kokarin samar ma ta da wata saban waje. Kafin a samu nasarar hakan kuma dole matar ta zauna a asibiti tsawon watanni ma su yawa.

    • Arsenal Na Tattaunawa Da Declan Rice Kan Tsawaita Kwantiraginsa A Ƙungiyar
    • An Yi Musayar Kwarewa Game Da Ayyukan Rage Talauci Ga Masu Bukatar Musamman Na Sin a Dandalin FAO

    “Saboda haka, abin da ya fi dacewa ga mace don tsaftace jikinta shine ruwa mai tsabta kawai. Idan ta yi amfani da duk wani abu da yake dauke da wani sanadari kamar sabulu ko turare, zai iya kashe kwayoyin halittar da Ubangiji ya halitta mata don jikinta ya zauna lafiya.

    Amma yayin da ta lahanta kwayoyin halittar da Ubangiji ya yi mata, sai kwayoyin cuta su samu damar shiga jikinta. A karshe irin wadannan mata za su fara fitar da gurbataccen ruwa, “inji shi.

    Ya ci gaba da bai wa mata shawarar cewa, kama ta ya yi su ke wanke jikinsu da ruwa mai tsafta kadai, kuma “kar mata su damu da wani wari da ke fita daga jikinsu saboda wannan warin dabi’ar da Allah Ya halicci wajen ne, matukar ba wari ne na cuta ba, wanda shi kuma warin cuta ya na kasancewa mai yawa ne”.

    [ad_2]

    Source link

  • Amurka Ta Yi Watsi Da Nadin Mojtaba Khamenei’ Sabon Shugaban Iran

    [ad_1]

    Kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ba da rahoton cewa; a ranar Litinin da ta gabata ne, kasar Iran ta nada Mojtaba Khamenei, a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa, Ali Khamenei, a matsayin shugaban koli.

    Hakan na nuni da cewa, masu tsattsauran ra’ayi za su ci gaba da rike madafun iko a Tehran, a rikicin da suke yi da Amurka da Isra’ila.

    • Za a Gudanar Da Tattaunawa Kan Batun Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka a Faransa Daga Ranar 14 Zuwa 17 Ga Watan Maris
    • Arsenal Na Tattaunawa Da Declan Rice Kan Tsawaita Kwantiraginsa A Ƙungiyar

    Mojtaba, malami ne mai matsakaicin matsayi tare da tasiri a cikin jami’an tsaron kasar Iran da kuma manyan hanyoyin kasuwanci a karkashin mahaifinsa, ana kallonsa a matsayin wanda ke kan gaba a zaben da majalisar ta yi, kungiyar malamai 88 da suka aiwatar da zaben sabon shugaban, bayan Ali Khamenei.

    A cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar bayan tsakar daren ranar Litinin a birnin Tehran na kasar Iran ta ce; ta hanyar kuri’ar da aka kada, majalisar kwararru ta nada Ayatollah Sayyid Mojtaba Hosseini Khamenei a matsayin shugaban tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na uku.

    Matsayin ya bai wa Mojtaba matsayi na koli a dukkan lamurran da suka shafi tsarin Jamhuriyar Musulunci.

    Nadin na Mojtaba, zai iya jawo fushin shugaban Amurka Donald Trump, wanda a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa; ya kamata Washington ta sanya baki a zaben. “Idan bai samu amincewa daga gare mu ba, ba za mu bari zaben ya je ko’ina ba,” kamar yadda ya fada wa kafar yada labarai ta ABC.

    Kafin wannan mataki, Isra’ila ta yi barazanar kashe mahaifin Mojtaba, Jagoran Addini Ali Khamenei, a daya daga cikin hare-haren farko da aka kaddamar kan Iran fiye da mako guda da ya gabata.

    Rundunar sojin Amurka a ranar Lahadin da ta gabata ta ba da rahoton cewa, wani Ba’amurke wanda shi ne na bakwai, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a harin farko na Iran mako guda da ya wuce, kwana guda bayan da Trump ya jagoranci komawa da gawarwakin wasu shida da suka mutu Amurka.

    Hare-haren na Amurka da Isra’ila, sun yi sanadiyyar kashe fararen hula akalla 1,332 na Iran tare da raunata dubban wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, a cewar jakadan Iran na Majalisar Dinkin Duniya.

    Yayin da Trump ya matsa lamba kan mika wuya ba tare da wani sharadi ba, Mohammad Bagher Kalibaf, kakakin majalisar dokokin Iran, ya ce; Tehran ba ta neman tsagaita bude wuta a yakin, sannan kuma za ta hukunta masu tada kayar baya.

    Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kan wasu manyan jami’an Iran, ciki har da Abolkasem Babaian, wanda aka nada kwanan nan a ofishin soji na babban jagoran, yana mai cewa; an kashe shi ne a wani harin da ta kai ranar Asabar. (Reuters)

    Wasu sabbin hare-hare guda biyu da Isra’ila ta kai cikin dare, sun shafi wuraren da ake jibge man fetur a ciki da wajen Tehran da kuma wani harin da aka kai a wani otal da ke tsakiyar Beirut babban birnin kasar Lebanon, wanda aka kai kan wasu da ake zargin kwamandojin Iran ne.

    Jiragen saman yakin, sun kai harin ne kan wasu cibiyoyin man fetur guda biyar a ciki da wajen babban birnin Iran, inda suka kashe akalla mutum hudu, a cewar wani jami’in mai na kasar.

    Gwamnan Tehran, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na IRNA cewa; “an dakatar da rarraba mai na dan wani lokaci” a babban birnin kasar.

    Wani duhu ne ya mamaye birnin mai dauke da mutane kimanin miliyan 10, wanda ya toshe rana, kuma warin man fetur ya jima yana bin iska.

    Har ila yau, hukumomin kasar sun yi gargadin cewa; hayakin na iya kasancewa mai dauke da guba tare da yin kira ga ‘yan kasar da su kasance sun zauna a gida, amma duk da haka, karfin fashe-fashen ya fasa tare da lalata tagogi da dama.

    “Fiye da sa’o’i 12 da gobarar ta ci gaba da ci, iskar ta ci gaba da gurbata da ta kai har ba ma iya yin numfashi ba. Kazalika, babu mai iya fita don yin sayayya ta yau da kullum,” in ji wani dan shekara 35 daga Tehran.

    “Da farko, na goyi bayan wannan yakin, bayan mutuwar Khamenei, inda muka yi biki tare da abokaina, muka sha ruwan inabi, muka kuma yi rawa.

    “Amma tun jiya mutane suke cewa, babu ko da dan kadan na man fetur da ya rage a gidajen mai,” in ji ta a cikin sakon tes zuwa Turai.

    Yayin da yakin ya tsawaita a kwana na tara, dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun ce; suna da isassun kayayyakin da za su ci gaba da yakin da suke yi da makamai masu linzami a Gabas ta Tsakiya, har na tsawon wata shida.

    An ji karar fashewar wasu abubuwa a cibiyar kasuwanci ta Isra’ila, Tel Abib, bayan da sojojin Isra’ila suka ce; sun gano wani makami mai linzami daga Iran. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Magen Dabid Adom ta ce, mutum shida sun jikkata a tsakiyar birnin Isra’ila.

    [ad_2]

    Source link

  • Amurka Ta Sanya Kyautar Ladan Dala Miliyan 10 Kan Bayanin Shugabannin Sojin Iran

    [ad_1]

    Gwamnatin Amurka ta sanar da bayar da ladan da ya kai dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan wasu manyan jami’an soji da na leƙen asirin Iran, ciki har da sabon jagoran ƙasar, Ayatollah Mojtaba Khamenei.

    A cewar bayanan da aka wallafa a shafin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ladan ya shafi jami’ai 10 da ake dangantawa da Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), rundunar sojin Iran da aka kafa bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979 domin kare tsarin mulkin addini na ƙasar.

    • An Kama Na Hannun Daman Ganduje Kan Badaƙalar ‘Dala Dry Port’ A Kano
    • Kamfanin Shell Ya Yi Alƙawarin Zuba Jarin Dala Biliyan 20 A Najeriya Bayan Dala Biliyan 7 Da Aka Kashe – NNPCL GCEO

    Rahotanni sun ce Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifinsa, Ali Khamenei, a matsayin jagoran ƙasar bayan mutuwarsa tare da wasu manyan jami’an Iran a hare-haren haɗin gwuiwa da Amurka da Israel suka kai tun daga ranar 28 ga Fabrairu.

    Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa Ali Larijani ya bayyana a wani gangami a Tehran tare da shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian, da ministan harkokin waje, Abbas Araqchi, duk da iƙirarin da sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya yi cewa shugabannin Iran suna ɓoye a karkashin ƙasa.

    Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce waɗannan jami’an na jagorantar sassan IRGC da ke tsarawa da aiwatar da hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na duniya. Sai dai Iran ta daɗe tana musanta zargin tallafa wa ta’addanci, tana mai cewa zarge-zargen na Amurka siyasa ce da ake amfani da ita wajen ƙara matsin lamba ko kakaba takunkumi a kan ƙasar.

    [ad_2]

    Source link

  • An kashe jami’in Sibil Difens a wurin rabon tallafin Alhassan Doguwa a Kano

    [ad_1]



    Ajali ya kaste hanzarin wani jami’in hukumar tsaro ta Sibil Difens a wajen rabon tallafin kayayyakin azumi da na sallah a Karamar Hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano.

    Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a yayin da ake rabon tallafin wanda ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa ya ɗauki nauyin raba wa al’ummar yankin.

    Da yake tabbatar da lamarin, ɗan majalisar ya ce jami’in ya rasu ne a yayin da wasu ɓata-gari suka yi yunƙurin tayar da tarzoma a wurin tabon tallafin.

    Alhassan Doguwa ya bayyana alhininsa kan lamarin, inda ya miƙa ta’aziyyarsa ga hukumar sibil difens da iyalan mamacin da kuma al’ummar Tudun Wada baki ɗaya.

    Ya buƙaci jami’an tsaro da su gaggauta gudanar da bincike domin bankaɗo masu hannu a wannan aika-aika da ya ce tilas ne su fuskanci fushin doka.

    Doguwa ya kuma gargaɗi masu yaɗa jita-jitar da ke alaƙanta shi da rasuwar jami’in, yana mai jaddada cewa zai ɗauki matakin shari’a kan duk wani da ya yi yunƙurin ɓata masa suna ko ta mazaɓar da yake wakilta.

    Ya yi adduar Allah Ya jiƙan mamacin, tare da nanata buƙatar a riƙa lura a kowane wuri na taron jama’a.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Kwara Za Ta Gyara Makarantu 898

    [ad_1]

    Gwamnatin Jihar Kwara za ta gyara manya da kananan Makarantu 898  domin tabbatar da za’a  samar da ilimi mai nagarta.

    Gwanbatin Jihar ta kaddamar da kwamiti mai samar da fasaha (TSPs) a karkashin tsarin kula da ‘yanmata da suke  a tsakanin shekarun 10, 18, da 24,na taimaka masu ta bangaren ilimi da kuma yadda za su dogara da kansu ( AGILE).

    • Nijeriya Na Yunkurin Mayar Wa Da Manoman Tumatir Asarar Da Suka Yi Ta Naira Biliyan 1.3
    • Arsenal Na Tattaunawa Da Declan Rice Kan Tsawaita Kwantiraginsa A Ƙungiyar

    Kwamishinan ilimi da ci gaban al’umma, Dokta. Lawal Olohungbebe,shi ne ya kaddamar da horon na kwana biyu ga mambobin kwamitin.

    Olohungbebe ya jinjinawa  Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ta yadda ya maida hankalin sa da  kuma kulawa da abinda zai taimakawa rayuwa domin bunkasa tattalin arziki da ilimi na al’umma, ta hanyar maida hankali akan wasu mutanen da suke bukatar saboda halin da suke ciki na fatara, za kuma a iya cutar da su ko gallaza masu,suna fuskantar rashin tsaftam da dai wadansu abubuwan da suka sa ba za su iya yin wani abu ba.Irin wadannan sau da yawa ana nuna masu wariya ga kuma kuntata masu idan wata bukata ta taso, bama kamar idan abin ya zama tilas ne sai an same shi.Wadannan mutane sun hada da yara, tsofaffi, mutane masu bukata ta musamman,‘yan gudun Hijirar,da kuma wadanda kabilarsu bata da yawa.

    Duk da hakan jami’in da yake kula da shirin AGILE na Jihar Kwara, Mista Adeshina Salami, ya bayyana muhimmanci  da irin hadin kai da ganin mutuncin juna da ke tsakanin kwamitin  makaranta da kuma masu samar da fasaha a tabbatar da an samu nasara.

    Ya bada tabbacin cewar duk makarantu za su amfana da tanadin samar da tsaftataccen ruwa, kulawa da muhalli da duk abubuwan da aka san za su taimaka ga cimma shi tsarin na (WASH).

    Ita jami’ar kulawa da muhalli ta kasa mai kulawa da Abuja (NPCU), Mrs. Nkechi Ikemefuna cewa ta yi shi horon, yana da matukar miuhimmanci domin yana taimakawa wajen ganewa,  ta yadda za’a hana aukuwar matsalar da za’a iya fuskanta data shafi muhalli da kuma abinda ka iya shafar zamantakewa ta al’umma bama kamar idan bukatar tsugunnar da mutane zuwa wani wuri idan bukatar hakan ta taso.

    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnatin Kano Ta Amince Da Ayyuka Na Sama Da Biliyan ₦310

    [ad_1]

    Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da aiwatar da ayyuka dan darajarsu ta haura Naira biliyan 310 domin inganta ababen more rayuwa a fannin ilimi, da lafiya, da gidaje da sauran muhimman fannoni a faɗin jihar.

    An yanke wannan hukunci ne a zama na 38 na majalisar da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranta a zauren majalisar da ke Fadar Gwamnatin Kano. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar bayan kammala taron.

    • Kotun Ƙoli Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masarautar Kano
    • Lauyoyin Gwamnatin Kano Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Rufe Ma’aikatar Shari’a

    A cewarsa, majalisar ta amince da ayyuka da ƙudurori da kudinsu ya kai N310,266,203,046 a fannoni daban-daban na tattalin arziƙin jihar. A ɓangaren ilimi kuwa, an amince da kashe Naira miliyan 238.02 domin biyan kuɗin JAMB ga ɗaliban da suka cancanta a fadin jihar, tare da gyaran makarantu a ƙananan hukumomi da dama.

    Haka kuma an amince da ayyukan hanyoyi da gine-gine da suka haɗa da gyaran shalƙwatar hukumar kashe gobara ta jihar, ƙarin wasu ayyuka a Asibitin Yara na Hasiya, da kula da titin Rimin Auzinawa a ƙaramar hukumar Ungogo da kuma gina hanyoyin Ladanai. Majalisar ta kuma amince da Naira biliyan 13.2 domin aiwatar da ayyukan mazabu na shekarar 2026 a faɗin jihar.

    A ɓangaren gidaje, majalisar ta amince da sama da Naira biliyan 113 domin gina gidaje 480 a wani babban shirin gidaje mai suna Gida Gida Mega City a Rijiyar Gwan-Gwan. Haka kuma an amince da sayen injinan wankin ƙoda ga cibiyar Abubakar Imam Urology Centre da kuma kayan aikin haƙora ga asibitocin jihar.

    [ad_2]

    Source link

  • Yadda Aka Bar Iyakokin Nijeriya 1,978 Babu Jami’an Tsaro

    [ad_1]

    Iyakar kasar Nijeriya mai fadi da rashin cikakken sa ido ta zama hanyar buya da kungiyoyin ‘yan bindiga, safarar makamai da sauran laifukan ketare iyaka ke amfani da ita. Rahotanni sun nuna cewa daga cikin kusan mashigai kusan 2,000, guda 84 ne kadai ke da jami’an tsaro a kan iyakar kasar mai tsawon kusan kilomita 4,000 da ke makwabtaka da kasashe. Wannan gibi na tsaro na karuwa duk da kasancewar hukumomin tsaro daban-daban a yankunan.

    A wani rahoto da Tarkaa Dabid ya rubuta, majiyoyin soji da na cikin gida sun yi gargadin cewa ’yan ta’adda da ‘yan bindiga na cin gajiyar wadannan iyakoki masu rauni domin shiga da fita ba tare da tsangwama ba.

    • An Yi Musayar Kwarewa Game Da Ayyukan Rage Talauci Ga Masu Bukatar Musamman Na Sin a Dandalin FAO
    • Arsenal Na Tattaunawa Da Declan Rice Kan Tsawaita Kwantiraginsa A Ƙungiyar

    Nijeriya na da iyakar kasa mai tsawon fiye da kilomita 4,000 da kasashe hudu masu amfani da Faransanci a matsayin harshen hukuma: Benin, Nijar, Chad, da Kamaru. Wadannan kasashe ma suna fama da barazanar tsaro, tawaye, ‘yan bindiga da matsanancin karancin abinci.

    Wadannan manyan iyakoki da suka ratsa dazuzzuka, hamada da hanyoyin ruwa suna da muhimmanci wajen kasuwanci da zirga-zirgar mutane. Sai dai a yanzu suna kara zama wuraren aikata laifukan ketare kasa, safarar makamai da kuma motsin kungiyoyin ‘yan bindiga marasa bin doka, wadanda ke amfani da rauni ta hanyar rashin sa ido na tsaro a kan iyakokin.

    Duk da muhimmancin wadannan iyakoki ga tsaro da tattalin arziki, bincike ya nuna cewa kusan mashigai na hukuma 2,000 ba su da jami’an tsaro, lamarin da ke haifar da babban gibi ta fuskar tsaro.

    Majiyoyin tsaro sun yi gargadin cewa wasu hanyoyin arewacin kasar, musamman a yankunan Jihar Borno, Adamawa, da Sokoto, sun zama hanyoyi masu rauni da ‘yan ta’adda da kungiyoyin masu aikata laifi ke amfani da su wajen shiga da fita cikin sauki. Wannan na barazana ga tsaron kasa tare da kara tsananta matsalar jin kai a al’ummomin da tuni suke cikin mawuyacin hali.

    A halin da ake ciki kuma, Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Bernard Doro, ya bayyana kwanan nan cewa Hukumar Kula da Kwararowar Bakin Haure da ‘Yan Gudun Hijira ta Cikin Gida (NCFRMI) na kula da fiye da kimanin mutum miliyan 6.7 ‘yan Nijeriya da suka rasa matsugunansu.

    Ya ce wadannan mutane na zaune ne a sansanonin ‘yan gudun hijira na cikin gida da kuma a cikin al’ummomin da suka karbe su a sassa daban-daban na Nijeriya.

    Yawancin wadannan mutanen da suka rasa matsugunansu ba sakamakon bala’o’in yanayi ba ne, sai dai rikice-rikicen da mutane ke haddasawa, kamar ta’addanci, ‘yan bindiga, rikice-rikicen al’umma da sauran tashin hankali.

    A watan Yunin 2025, tsohon Babban Hafsan Tsaro, Christopher Musa, ya yi kira da a gina katanga a kan iyakokin Nijeriya da makwabtan kasashe domin rage shigowa da fitar ‘yan bindiga da masu aikata laifi ta kan iyaka, tare da karfafa tsaron kasa.

    Ya yi gargadin cewa Nijeriya, wadda ke kewaye da kasashe hudu masu amfani da Faransanci a yankin Sahel, Benin, Nijar, Chadi, da Kamaru na iya fuskantar babban hadarin tsaro idan yankin Sahel ya kara tabarbarewa saboda iyaka masu rauni da saukin ketarawa.

    Ya ce: “Kula da iyaka abu ne mai matukar muhimmanci. Akwai kasashen da saboda tsananin matsalar tsaro a cikin kasarsu suka gina katanga a kan iyakokinsu. Idan aka ambaci wannan a Nijeriya, mutane sukan ce ba zai yiwu ba.

    “Pakistan ta gina katanga mai tsawon kilomita 1,350 a kan iyakarta da Afghanistan, kuma daga lokacin ne suka samu zaman lafiya.

    “Haka kuma Saudi Arabia da Iraki sun gina katanga gaba daya a kan iyaka mai tsawon kilomita 1,400.”

    Ya ce: “Ya kamata mu fara tunanin gina katanga a kan iyakokinmu. Muna da kilomita 1,500 da Nijar, kusan kilomita 1,900 da Kamaru, sannan akwai Chadi. A kusan dukkan bangarorinmu muna kewaye da kasashen da ke amfani da Faransanci. Yankin Sahel na kara rikicewa, kuma idan yankin Sahel ya fadi, Nijeriya ce za ta zama babbar manufa gare su.”

    Har ila yau, a watan Fabrairu 2026, Christopher Musa ya sake jaddada kiran da ya yi na karfafa tsarin sa ido da kula da iyakoki domin inganta tsaron kasa.

    Ya kuma sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na karfafa tsaron iyakoki, inganta jin dadin tsoffin sojoji, da kuma duba muhimman manufofin tsaro domin karfafa tsarin tsaron kasa na Nijeriya.

    Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar Tsofaffin Daliban Kwalejin Tsaro ta Kasa, wato ‘Alumni Association of the National Defence College,’ (AANDEC), a wata ziyara ta girmamawa da suka kai masa ranar Litinin 23 ga Fabrairu, 2026, a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.

    A cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Enderline Chukwu, ta fitar, ministan ya ce: “Yana da muhimmanci mu san waye ke shigowa kasarmu, waye ke fita, da kuma abin da ke shigowa cikin kasarmu,” yana mai karawa da cewa karfafa kula da iyakoki zai taimaka sosai wajen rage laifukan ketare kasa da matsalolin tsaro.

    Ministan ya kuma lura cewa yanayin tsaron Nijeriya na ci gaba da sauyawa kuma yana da sarkakiya, wanda ke bukatar ci gaba da duba da sabunta manufofin tsaro da ake da su, ciki har da Manufar Tsaro ta Kasa ta (2017) da kuma Aiwatar da Manufofin Kasa (2019).

    Ya ce: “Rayuwa tana sauyawa koyaushe kuma matsalolin tsaronmu suna canzawa. Saboda haka yana da muhimmanci rundunonin sojinmu da tsarin hukumominmu su dace da wadannan sauye-sauyen.”

    Ya kara da cewa takardun manufofi dole su rika sabuntuwa domin su dace da sabbin barazana da sauye-sauyen yanayin duniya.

    Christopher Musa ya kuma jaddada bukatar ba da fifiko ga jin dadin tsoffin sojoji, yana mai cewa wadanda suka yi wa kasa hidima sun cancanci cikakken tallafi bayan sun bar aiki, ciki har da kulawar lafiya da sauran tallafin jin dadi.

    Ya bayyana cewa ma’aikatar za ta yi aiki tare da hukumomin da suka dace, ciki har da Babban Sakatare na ma’aikatar da sauran abokan hulda na dabaru, domin fara tattaunawa a tsare da nufin duba da sabunta muhimman manufofin tsaro da sauran takardu masu alaka da suke bukatar gyara.

    Da yake ci gaba da magana, ministan ya bayyana cewa tsaron iyakoki muhimmin ginshiki ne na tsarin tsaron kasa na Nijeriya, yana mai jaddada muhimmancin karfafa sa ido da tsarin kula da iyakoki, domin tabbatar da cewa hukumomi suna da cikakken bayani kan motsin mutane da kayayyaki da ke shiga da fita ta iyakokin kasar.

    Ya kuma tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa ma’aikatar na nazarin wasu tsare-tsare domin karfafa tsarin jin dadin tsoffin sojoji, tare da nemo ingantattun hanyoyi mafi kyau da za su tabbatar da mutunci da ingantacciyar rayuwa ga sojojin da suka yi ritaya.

    A nasa bangaren kuma, Shugaban Alumni Association of the National Defence College (AANDEC), Ndidi Patrick Agholor (mai ritaya), ya bayyana cewa kungiyar tana da kwarewa da gogewa ta kwararru da za ta ba ta damar yin hadin gwiwa yadda ya kamata da Ma’aikatar Tsaro wajen aiwatar da Manufofin Tsaron Kasa.

    Ya kuma tabbatar da cewa kungiyar za ta ci gaba da goyon bayan ma’aikatar wajen karfafa tsarin tsaron Nijeriya ta hanyar bincike, ba da shawarwari, da tattaunawar dabaru.

    Ya kuma nemi goyon bayan Ma’aikatar wajen kara karfin aiki na AANDEC, ciki har da taimako kan sufuri, kayan ofis, kayan taro, gudanar da taron Tsaro na Kasa mai zuwa, da kuma ci gaban ginin dindindin na Kungiyar.

    Rear Admiral Agholor (mai ritaya) ya kuma tabbatar da sadaukarwar AANDEC wajen yin hadin gwiwa da Ma’aikatar don inganta manufofin tsaron kasa, yana mai jaddada cewa karfafa hadin gwiwar cibiyoyi zai taimaka matuka wajen magance kalubalen tsaro masu tasowa a Nijeriya.

    A yayin bayyana ra’ayinsa kan wannan ci gaba, Daraktan Gudanarwa na Beacon Security and Intelligence Ltd, Dr. Kabir Adamu, ya ce Nijeriya tana da iyakokin kasa tare da kasashe makwabta hudu, jimillar kilomita 4,047.

    Ya bayyana cewa mafi tsawon iyaka da ake rabawa ita ce da Jamhuriyar Nijar.

    Ya lura cewa tsaron iyakokin Nijeriya na fuskantar manyan kalubale, musamman saboda yanayin su mai rami da saukin wucewa.

    Ya danganta rahoton kwanan nan da aka gabatar wa Majalisar Wakilai, inda aka ce: “Daga cikin shige-shigen hukumomi 1,978 na kasar, ana kula da ma’aikatan tsaro ne kawai a wurare 84 a halin yanzu. Wannan yana barin yawancin hanyoyin da ba a hukunta ba da na haramun suna cikin rashin kulawa.”

    Ya ce wannan yana nuna cewar gwamnati tana kashe kudi mai yawa kan tsaro ba tare da samun sakamakon da ya dace ba, a cewar ‘yan majalisar.

    “Rashin cikakken kulawa irin wannan ya haifar da barazanar tsaro da dama, ciki har da: shigo da makamai ba bisa ka’ida ba, safarar mutane, da safarar miyagun kwayoyi.”

    “Karuwar hadarin shigar kungiyoyin ‘yan ta’adda da ‘yan fashi daga yankin Sahel,” in ji Adamu.

    Ya ce kiran da Ministan Tsaro ya yi na gina shinge a iyakokin Nijeriya kada a dauka a matsayin mafita guda daya kawai, amma wani bangare ne na cikakken tsari.

    “Kuma tun da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ce ke da alhakin kula da tsaron iyakoki, ya kamata a hada ta sosai a cikin wannan aiki,” ya shawarci.

    Ya jaddada cewa duk da cewa gwamnatin Nijeriya tana aiwatar da tsari mai yawa don magance wadannan kalubale, tana mai da hankali kan ma’aikata, kayan aiki, fasaha, da manufofi.

    Inganta karfin ma’aikata da kayan aiki ta hanyar daukar ma’aikata 10,000 kari; kafa tashoshin iyaka guda bakwai (tare da wasu bakwai da ake shirin kara) da aka tanada da kayan aiki gaba daya, ciki har da wutar lantarki daga hasken rana, ruwa, da hadin sadarwa.

    “Kara amfani da fasaha da inganta sa ido kamar tsarin e-border na kasa, wanda yanzu ya rufe fiye da kashi 60 cikin 100 na iyakokin kasa; kafa cibiyar bayanai mai karfin 8.3-petabyte tare da cibiyar umarni da sarrafawa; ingantaccen sa ido daga sama; da kuma motocin sintiri 55 masu karfin aiki,” in ji shi.

    A bangaren manufofi, ya jaddada bukatar sake duba da sabunta Manufofin Tsaron Kasa (National Defence Policy, 2017) da Tsarin Tsaron Kasa na 2019 da suka dade sun tsaya cik, karfafa hadin gwiwar hukumomi daban-daban da musayar bayanai; yin aiki tare da abokan hulda na kasashen waje wajen kula da harkokin hijira; da kuma la’akari da gina shinge a iyakoki a matsayin wata hanyar dabaru.

    Haka kuma, ABM Olatokunbo Adesanya (mai ritaya), tsohon mai magana da yawun Sojan Sama na Nijeriya da tsohon Jakadan Tsaro na Nijeriya a Rasha, ya ce iyakokin Nijeriya na fuskantar manyan kalubale, mafi girma daga ciki shi ne yawan ramukan shiga da fita.

    Ya lura cewa Nijeriya tana da iyakoki masu yawa tare da wuraren shiga da fita ba bisa ka’ida ba, wanda ke ba da damar hanyoyi marasa izini inda ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka marasa izini ke shigowa kasar ba tare da an gano su ba ko an rubuta su ba.

    Ya kara da cewa wahalar wurare a wasu sassan kasar na kara ta’azzara matsalar.

    “Ma’anar wadannan kalubale shi ne cewa ma’aikatan ‘yan gudun hijira a tashoshin iyaka suna kula ne kawai da shigar/fitar mutanen da suke so a sani. Wadanda ke da mugun nufi sau da yawa suna amfani da ramukan iyakokinmu,” in ji shi.

    Ya ce, magance wannan matsalar na bukatar hadin dabaru da yawa.

    “Wadannan sun hada da amma ba’a takaita ga amfani da fasaha ba kamar jiragen sama marasa matuki masu dogon tafiya (UABs) da saka kyamarorin CCTB masu karfin gaske a wurare da aka zaba, duk wadannan za su kasance da cibiyar sarrafawa daga nesa/umurni da sarrafawa.

    “Na ga irin wannan tsarin yayin ziyarata iyakar Belarus a matsayin Jakadan Tsaro na Nijeriya a Moscow. Tsarin Belarus ya hada da gina shinge na zahiri tare da tsarin fadakarwa a gefen iyaka.

    “Na tuna da bayar da shawarar gina shinge na zahiri a iyakokinmu a cikin daya daga cikin rahotannina. Wasu na iya tambayar farashin gina shinge na zahiri amma ni ma zan tambayi farashin rashin gina shi a yanzu musamman a fannin rayuka, dukiyoyi da karfafa iyaka,” in ji shi.

    Bugu da kari, ya bukaci a dauki karin ma’aikata cikin Hukumar ‘Yan Gudun Hijira tare da samar da isassun motocin sintiri masu makami.

    ABM Adesanya (mai ritaya) ya kuma jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa mai karfi tsakanin hukumomi don magance wadannan kalubale.

    [ad_2]

    Source link

  •  ‘Yan Ta’adda Na Neman ‘Yan Matan Indiya Da Tabar Wiwi Da Hodar Iblis A Matsayin Kudin Fansa

    [ad_1]

    Kungiyar zamantakewa da siyasa ta kabilar Yarbawa, Afenifere, ta yi Allah-wadai da sabon yawaitar kutsen ‘yan ta’adda a yankin kudu maso yammacin Nigeria, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen ceto yankin daga matsalar ‘yan bindiga.

    A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar Asabar, Sakataren Yada Labarai na kungiyar na kasa, Jare Ajayi, ya bayyana damuwar al’ummar Yarbawa kan yadda ake samun asarar rayukan jama’a kusan kullum a jihohi da dama.

    • Nijeriya Na Yunkurin Mayar Wa Da Manoman Tumatir Asarar Da Suka Yi Ta Naira Biliyan 1.3

    Sun kuma yi nuni da yadda ake mummunar mu’amala da mutanen da aka sace, inda ake dukansu da wulakanta su ba tare da jin kai ba.

    Ajayi ya kawo misalai na hare-hare da dama, ciki har da: hare-hare kan coci-coci, ofisoshin ‘yan sanda, gidajen jama’a da manyan hanyoyi a Ondo, kore al’ummomi daga garuruwansu a Jihar Kwara, kisan manoma da kai hari kan matafiya a kan hanyar Igbeti–Kisi a yankin Oke-Ogun na Jihar Oyo, da kuma munanan sace-sacen mutane a Jihar Ekiti, inda aka kashe wasu daga cikin wadanda aka sace sannan aka rike gawarwakinsu domin neman kudin fansa.

    Kudin Fansa

    Ya kara da cewa: “Babbar shaida ta rashin tausayi da mugunta na wadannan miyagu ita ce yadda suka nemi Naira miliyan 1.5, tabar wiwi (Indian hemp), hodar iblis (cocaine), wani maganin maye na roba da ake kira ICE, da kuma kwandunan giyar kwalba, domin a sako gawar wani mutum da ke hannunsu.”

    Ya ci gaba da cewa masu garkuwa da mutanen har ma sun bukaci a kawo musu ‘yan mata budurwai a matsayin fansa domin su saki maza hudu da suka sace a baya.

    A cewar Sakataren Yada Labarai na Afenifere, Jare Ajayi: “Har zuwa kwanan nan, ana kallon gida a matsayin mafaka mai aminci. Abin takaici, hakan ba haka yake ba yanzu. Wasu ma’aurata an kai musu hari a gaban gidansu a Akure, a Jihar Ondo, inda aka harbi mijin yayin da yake kokarin hana sace matarsa.”

    Ajayi ya kuma bayyana cewa Elder Igwe, mahaifin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ebonyi, an sace shi ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa coci a ranar Lahadi, 1 ga Maris.

    Haka kuma a Erinmope-Ekiti da ke Jihar Ekiti, an sace iyali guda mai mutum biyar da misalin karfe 7 na yamma, a lokacin da mutane suke sallar magariba a masallaci.

    Ajayi ya kara lura cewa irin wadannan hare-hare na dogon lokaci ana samun su a jihohi da dama, ciki har da Jihohin Kwara, Filato, Binuwe, Borno, Kebbi, Nasarawa, Neja, Katsina, da Jihar Kaduna.

    Ya kuma ce ’yan gudun hijira da suka dawo daga Kamaru su ma sun fada cikin irin wadannan hare-hare a Jihar Bauchi.

    Da yake tuna wani lamari da ya faru a Jihar Edo, Sakataren Yada Labarai na Afenifere, Jare Ajayi, ya bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka sace wani likita da dan’uwansa, inda suka kashe kanin amma suka saki likitan bayan an biya kudin fansa.

    Ajayi ya ce: “Lokacin da ’yar daya daga cikin masu garkuwar ta kamu da rashin lafiya, likitan wanda ke bakin aiki a asibiti ya gane mutanen da suka aikata laifin, sannan ya sanar da ‘yansanda, lamarin da ya kai ga kama su.”

    Ya kara da cewa: “Abin lura a nan shi ne cewa dan bindigar ya daraja rayuwar ‘yarsa har ya kai ta asibiti domin a kula da lafiyarta, amma a lokaci guda bai ga laifi ba wajen kashe rayukan wasu mutane.”

    Ajayi ya jaddada cewa ta’addanci da sace mutane sun yawaita sosai, amma ya ce matsalar ba wadda ba za a iya shawo kanta ba ce, yana mai cewa:

    “‘Yan bindiga ba aljanu ba ne kuma ba su da karfin da ba za a iya kayar da su ba.”

    Daga nan ya yi kira ga a dauki mataki mai karfi domin katse hanyoyin da ‘yan bindiga ke samun kudi, wadanda suka hada da:

    Wasu attajirai marasa gaskiya, kungiyoyin gida da na kasa da kasa, wasu jami’an gwamnati, al’ummomin da ke biyan kudin kariya ko kudin girbi, kudin fansa daga wadanda aka sace, da kuma sata kai tsaye.

    Masu Hakar Ma’adanan Kasar Waje

    Ya kuma yi kira a gudanar da bincike kan ’yan waje da ke da hannu a cikin harkokin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, wadanda ka iya zama suna jawo korar al’ummomi daga garuruwansu.

    “Bayanan da aka samu daga ’yan bindiga da aka kama kuma aka gurfanar da su sun nuna cewa suna da masu daukar nauyi. Saboda haka, yana da muhimmanci a bi diddigin masu daukar nauyin da masu shiga tsakani, katse hanyoyin samun kudade da makamai, kai farmaki a dazuzzukan da suke boye, magance cin hanci da barnar da ke cikin hukumomin tsaro, karfafa ma’aikata, da tabbatar da kafa ‘yan sanda na jiha nan da nan,” in ji Ajayi.

    Afenifere ta yaba wa Shugaba Bola Tinubu saboda jajircewarsa wajen ci gaba da kafa ‘yan sanda na jiha, tana mai jaddada kira da ya yi ga Majalisar Kasa da ta hanzarta gyara kundin tsarin mulki don tabbatar da fara aiki nan take.

    Haka kuma an yabi sabon Sufeto Janar din ‘yansanda, Tunji Disu saboda kafa kwamitin da zai tsara hanyoyin da za a yi amfani da su wajen tura ‘yan sanda na jiha.

    Kungiyar ta sake jaddada kiranta ga gwamnonin kudu maso yamma da su aiwatar da matakai na kai farmaki a boyayyun wuraren ‘yan bindiga, kula da yankunan da suka fi fuskantar barazana, da hadin kai sosai da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da kafa ‘yan sanda na jiha cikin gaggawa a jihohinsu.

    [ad_2]

    Source link