Category: Latest News

  • ’Yan bindiga sun kashe magidanci sun sace matarsa mai juna biyu a Kebbi

    [ad_1]



    Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa magidanci, Sufiyanu Garba, sun yi awon gaba da matarsa mai juna biyu a yankin Badariya da ke Birnin Kebbi a Jihar Kebbi.

    Wani ɗan uwan matar, Shehu Mohammed Yauri, ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hari gidan ƙanwarsa Zainab wadda take ɗauke da juna biyu a cikin daren Juma’a, inda suka harbe mai gidanta sannan suka yi awon gaba da ita.

    Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kebbi, Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa tuni suka bazama domin gudanar da bincike tare da ɗana wa maharan tarko.

    Ya ƙara da cewa, bayan faruwar lamarin, sun garzaya da Sufiyanu mai shekaru 35 zuwa asibitin Sir Yahaya Memorial, inda a nan ƙwararrun mahukunta kiwon lafiya suka tabbatar da rasuwarsa.

    Kakakin ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar ya ba da umarnin mayar da lamarin hannun sashen binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike mai zurfi.

    Ya ce suna fatan binciken zai ba su nasarar ceto matar da kuma cafke duk masu hannu a lamarin.


    [ad_2]

    Source link

  • Sin Ta Yi Nasarar Harba Rukunin Taurarin Dan’adam Guda Biyu

    [ad_1]

    A yau Juma’a ne kasar Sin ta yi nasarar harba rukunin taurarin dan’adam guda biyu, masu aikin samar da hidimar intanet da wadanda aka tsara domin gudanar da gwaje-gwajen kimiyya.

    An harba rukunin taurarin na farko ne da karfe hudu saura mintuna 12 agogon Beijing, daga cibiyar harba kumbuna ta Hainan, ta amfani da rokar Long March-8A. Rahotanni sun ce aikin shi ne irinsa karo na 20, na harba taurarin dan’adam marasa nisa daga doron duniya, domin samar da hidimomin intanet da kasar Sin ke gudanarwa.

    A daya bangaren kuma, da karfe bakwai saura minti 27 na safiyar yau, aka harba rukunin taurarin dan’adam na biyu, daga cibiyar harba kumbuna ta Xichang dake lardin Sichuan, ta amfani da rokar Long March-2D, inda karkashin wannan aiki aka yi nasarar harba taurarin dan’adam na Shiyan-30 mai lamba 03 da 04. Wadannan taurarin dan’adam za a yi amfani da su ne wajen gudanar da gwaje-gwaje na fasahohin nazarin doron kasa. Shi ne kuma karo na 632, da aka yi nasarar amfani da rokar Long March wajen harba taurarin dan’adama a kasar Sin. (Saminu Alhassan)

    [ad_2]

    Source link

  • NiDCOM Ta Nemi A Saki ‘Yan Nijeriya 42 Da Ake Tsare Da Su A Mozambikue

    [ad_1]

    Shugabar kuma Babbar Daraktar Kungiyar ‘yan Nijeriya Mazauna Kasar Waje, (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta yi Allah-wadai da rahoton kama ‘yan Nijeriya 42 a kasar Mozambikue ba tare da gabatar musu da wata tuhuma a hukumance ba, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin damuwa da kuma abin da ba za a amince da shi ba.

    Dabiri-Erewa ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja ta hannun Daraktan Yada Labarai, Hulda da Jama’a da Kuma Tsare-tsare na Hukumar, Abdur-Rahman Balogun.

    • Yawan Dazuzzuka Da Filin Ciyayi a Kasar Sin Ya Wuce Kashi 56%
    • Sin Ta Himmatu Wajen Raya Ci Gaban Duniya Na Bai Daya

    Ta nuna damuwa cewa an zargi jami’an tsaro da ware ‘yan Nijeriya ne kadai domin kamawa a cikin wasu ‘yan kasuwa da ke kasuwancin kayan gyaran motoci (spare parts).

    A cewarta, abin takaici ne yadda aka ce an ware ‘yan Nijeriya kadai aka kama tare da tsare su ba tare da wani bayani daga hukumomi ba.

    Shugabar kungiyar, Abike Dabiri-Erewa, ta ce idan har wasu daga cikin wadanda aka kama sun karya dokokin Mozambikue, to ya kamata a tuhume su a hukumance sannan a gurfanar da su a gaban kotu mai iko.

    Ta kara da cewa kamun da aka yi musu ba zato ba tsammani tare da ware su musamman yana tayar da damuwa kan yiwuwar nuna kiyayya ga baki (denophobia) ga ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasar.

    Saboda haka, ta bukaci hukumomin Mozambikue da su saki wadanda aka tsare nan take, ko kuma su tabbatar an bi dukkan matakan doka yadda ya kamata.

    Rahotanni sun nuna cewa an ware ‘yan Nijeriyar ne aka kama a kasuwar kayan gyaran motoci (spare parts) duk da cewa akwai ‘yan kasuwa daga wasu kasashe daban-daban a wurin.

    An kuma ce mutanen da aka kama suna zaune a Mozambikue bisa ka’ida, yayin da aka ruwaito cewa Babban Lauyan kasar bai ma san da wata tuhuma da aka shigar a kansu ba.

    Har ila yau, an yi zargin cewa an ci zarafin wasu daga cikin wadanda aka kama yayin aikin, tare da kwace musu kayayyakinsu na kashin kai. An kuma ce wasu daga cikinsu sun kamu da rashin lafiya kuma suna bukatar kulawar likita cikin gaggawa.

    Dabiri-Erewa ta bukaci hukumomin Mozambikue da su mutunta hakkoki da martabar ‘yan Nijeriya da ke kasar, tare da tabbatar da cewa adalci da gaskiya sun yi rinjaye.

    [ad_2]

    Source link

  • Amurka Ce Tushen Matsalar Da Ake Ciki Dangane Da Batun Nukiliyar Iran

    [ad_1]

    Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce Amurka ce tushen matsalar da ake ciki yanzu haka dangane da batun nukiliyar kasar Iran, kuma matakan da ta dauka sun saba wa dokokin kasa da kasa, da ka’idojin dake kunshe cikin kundin kafuwar MDD.

    Fu Cong, wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin zaman kwamitin nazarin takunkuman da aka kakabawa kasar Iran na kwamitin tsaron MDD, ya ce Sin na matukar adawa da matakan da Amurka ta aiwatar.

    Jami’in ya kara da cewa, wajibi ne a martaba ikon mulkin kai, da tsaro da hurumin yankunan kasar Iran, kuma Amurka da Isra’ila su gaggauta dakatar da aiwatar da matakan soji.

    Ya ce dole ne a yi kokarin warware batun nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya, kana a kare ikon Iran na cin gajiyar makamashin nukiliya ta hanyar lumana, a matsayinta na daya daga kasashe da suka amince da yarjejeniyar kasa da kasa ta hana yaduwar makaman nukiliya.

    Kazalika, bai kamata kwamitin tsaron MDD ya zamo makamin kakaba takunkumai, matsin lamba, ko dandalin aiwatar da ajandar siyasa ta wasu daidaikun kasashe ba. (Saminu Alhassan)

    [ad_2]

    Source link

  • Tinubu ya kafa kwamitin gyara harkar man fetur a Najeriya

    [ad_1]



    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa wani kwamiti na musamman domin ɓullo da sabbin matakan gyare-gyare a ɓangaren harkar man fetur a Najeriya.

    Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

    A cewar sanarwar, Fola Adeola, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa bankin Guaranty Trust Bank kuma shugaban Fate Foundation, shi ne zai jagoranci kwamitin.

    Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Ademola Adeyemi-Bero, Osagie Okunbor, Abubakar Suleiman, Adaeze Aguele, Farouk Gumel, Phillipa Osakwe-Okoye da Seyi Bella, yayin da Mofoluwasho Fadayomi zai zama sakataren kwamitin.

    An ɗora wa kwamitin alhakin tsara matakan gyare-gyare da za su bunƙasa harkar man fetur, su jawo ƙarin zuba jari, tare da ƙara wa tattalin arziƙin ƙasar nan daraja.

    Kwamitin zai riƙa kai rahoto kai-tsaye ga shugaban ƙasa duk wata, sannan zai gabatar da rahoton wucin gadi bayan watanni uku, yayin da ake sa ran kammala rahoton ƙarshe cikin watanni shida.

    Ana sa ran kwamitin zai gabatar da manyan tsare-tsare uku na gyara, ciki har da matakan sauya tsarin ɓangaren nan take.

    Shirin zai bayar da damar samun jarin dala biliyan biyar zuwa 10, da kuma wani tsari na sauya tsarin makamashi na ƙasa na tsawon shekaru 10.


    [ad_2]

    Source link

  • Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Aikin Noma Domin Samar Da Wadataccen Abinci

    [ad_1]

    Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da babban sabon aikin noma na zamani da zummar kara samar da wadataccen abinci a Nijeriya.

    Har ila yau, shirin ya kunshi rabar da kayan aikin noma na zamani daidai har guda 9,022, wadanda suka hada da Taraktocin noma, kayan Haro, kayan yin girbin amfanin gona da kuma sauran wasu kayan aikin noma.

    • Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan ISWAP 20 A Jihar Yobe
    • Kudaden Shiga Na Masana’Antun Kimiya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Da 16.1% a Watannin Janairu Da Fabrairun Wannan Shekara

    “Muna daukar kasar nan a matsayin daya daga cikin kasashen da suka mayar da hankali wajen aikin noma a fadin duniya, domin muna fitar da ingantaccen amfanin gona zuwa kasuwannin daban-daban a duniya tare kuma da tabbatar da kowane dan Nijeriya ya samu abinci mai gina jiki,” in ji Tinubu.

    “Muna tunkaho da abin da muke ci gaba da yi, domin wannan kokarin na daga cikin alkawuranmu na yakin neman zabe da muke burin cika wa al’ummar wannan kasa.”

    Tinubu ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa ta dauki fannin aikin noma da matukar muhimmanci, domin fannni ne da ke samar da wadataccen abinci ga ‘yan kasa.

    “Wannan aiki ne, wanda za a iya cewa; tamkar a yanzu ne muka fara dora damba a kansa”, a cewar shugaban.

    Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin  tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma sama da 2,000.

    Ya ci gaba da cewa, kayan za su kuma taimaka wajen kara ayyukan masana’antun kasar da samar da damar gudanar da yin bita da kuma kwararrun kayan aikin noma 9,000.

    Shugaban ya jaddada muhimmancin yin amfani da kayan aikin noma na zamani, wanda hakan zai taimaka wa manoman wannan kasa.

    Har ila yau, ya kuma yi nuni da cewa; kaddamar da wannan shiri, wanda yake daidai da na aikin noma a duniya, hakan zai kara bunkasa aikin noman kasar da samar da wadataccen abinci da kuma kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.

    “Ina so mu dauki wannan rana ta kaddamar da wannan shiri tamkar ranar farko ce da Nijeriya ta yunkuro, domin farfado da wannan fanni na aikin noma,“ in ji Tinubu.

    “Yin noma da kayan aiki na zamani, shi ne kadai zai iya mayar da manoma tamkar wasu manyan jarumai,” a cewar shugaban.

    Shugaban ya kuma bayyana cewa, wannan shiri; an yi shi ne bisa hadaka da gwamnatin tarayya da kuma kamfanin da ke kera kayan aikin noma na zamani da aka fi sani da ‘APRE BNCC’.

    Shi ma, babban Ministan Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa; shirin ya kara tabbatar da yunkurin gwamnatin tarayya, wajen kara habaka fannin aikin noma na kasar, wanda kuma shi ne babban ginshikin ciyar da ta tattalin arzikin kasar gaba.

    “Taron na yau da ka kaddamar, ba wai kawai shiri ne don mu ba, illa kawai wata manufa ce ta gwamnatin tarayya na cimma kudurin habaka fannin aikin noman kasar,“ in ji Kyari.

    “Ana sa ran za a gudanar da shirin ne, a hekt sama da 550,000 tare da kuma da samar da sama da tan miliyan biyu na hatsi, inda kuma shirin zai samar da ayyukan yi sama da 16,000, wanda kuma sama da ‘yan cirani 560,000 da ke shiyoyi shida na kasar nan, za su amfana, a cewar Ministan.”

    Kazalika, Kyari ya bayyana cewa; shirin ya kuma hada da samar da ingantattun Taraktocin noma 2,000, da kayan haro da na fanfunan ban ruwa masu feshi da kayan girbi da sauran makamantansu.

    “Mun tanadi sama da na’urori masu kwakwalwa guda 9,000 da kuma kayan gyaransu guda  9,000,” in ji Ministan.

    Shi kuwa, a nasa jawabin a wajen taron; Mataimakin Fira Ministan Jamhuriyar Belarus, Bictor Karankebich, ya nuna jin dadinsa kan wannan yarjejeniyar da Nijeriya ta kulla da kasarsa.

    Ya bayyana cewa, Jamhuriyar ta Belarus, tana da dogon tarihi wajen kera kayan aikin noma, musamman duba da cewa; kasar ta tura kayan aikin noma da ta kera zuwa sama da kasashe 100 da ke fadin duniya.

    Ya ce, shirin wanda ya kasance kashi na farko; ya jaddada muhimmancin bukatar kara hada guiwa, domin wanzar da kashi na biyu na shirin a kasar nan.

    Ya ci gaba da cewa, kashin na wannan shiri, ya hada da samar da cibiyoyin hada Taraktocin noman da sauran kayan aikin noma da kuma bai wa manoma horo, domin sanin yadda za su sarrafa kayan aikin noman, wadanda akasarin kayan na zamani ne.

    Idan za a iya tunawa, Majalisar Zartarwa ta Kasa a watan Agustan shekarar 2024 ne, ta amince da yarjejeniya a tsakanin Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci da kuma Jamhuriyar ta Belarus.

    [ad_2]

    Source link

  • Sin Na Adawa Da Lalata Tsarin Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Duniya Bisa Kafa “Karamin Rukuni”

    [ad_1]

    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya ce kiyaye yanayin kasuwanci mai bude kofa ga duniya da samun moriya ga kowa tsakanin kasa da kasa, ya dace da muradun kasashen duniya, kuma Sin na adawa da wata kasa ta lalata tsarin tattalin arziki da cinikayya na duniya bisa kafa wani “karamin rukuni”.

    Guo Jiakun ya bayyana haka ne a yau Jumma’a, yayin taron manema labarai na yau da kullaum, lokacin da ya ke amsa tambaya game da matakan da suka shafi batun “ma’adinai masu muhimmanci” da Amurka da Japan da sauran kasashe suka dauka.

    Game da hare-haren da aka kai wa wata makarantar firamare dake Iran, Guo ya ce, bangaren Sin ya yi ta’azziyar daliban da suka rasu a hare-haren, kuma kungiyar agaji ta Red Cross ta Sin ta yanke shawarar ba da agajin gagawa na dalar Amurka dubu 200 ga kungiyar Red Cross ta Iran, don taimakawa iyayen daliban da suka mutu.

    Bugu da kari, game da shirin raya kasa na Sin na shekaru biyar masu zuwa, Guo ya ce, Sin za ta dage wajen zama karfi mai muhimmanci, da daidato, da kuma adalci a duniya.(Safiyah Ma)

    [ad_2]

    Source link

  • Nijeriya Na Yunkurin Mayar Wa Da Manoman Tumatir Asarar Da Suka Yi Ta Naira Biliyan 1.3

    [ad_1]

    Gwamnatin tarayya ta yunkuro, wajen samar da shirye-shiyen magance asarar da mamoman Tumatir ke tabkawa a kasar.

    Idan za a iya tunawa, a watan Mayun shekarar 2025 ne, Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wataccen Abinci ta Tarayya, ta kiyasta cewa; cutar ta lalata gonakin da ake noman Tumatir, inda momansa suka yi asarar kimanin naira biliyan 1.3, wanda hakan ya kuma jawo tashin gwaron zabin Tumatirin a dukkanin kasuwannin kasar nan.

    • Yawan Dazuzzuka Da Filin Ciyayi a Kasar Sin Ya Wuce Kashi 56%
    • Kawar Da Dukkanin Haraji Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar Sin Daga Afirka Zai Bunkasa Cinikayyar Albarkatun Gona Na Afirka Ta Kudu

    Hakan ne ya sa, Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wataccen Abinci ta Tarayya, ta kaddamar da wani shiri na musamman, don lalubo mafita a kan wannan matsala, domin dakile yaduwar cutar zuwa sauran gonakin da cutar ba ta kai ga yaduwa ba.

    Misali, wata kwayar halitta da ke cin ganye da kuma sauran kayan lambu, na iya jawo wa manoma asarar da ta kai daga kashi 80 zuwa 100, matukar ba a dauki matakan kare ta da gaggawa ba.

    Wanann na zuwa ne dai, bayan samun wasu rahotanni da aka alakanta su da barkewar annobar cutar a shakarar da ta gabata, da ake kira a turance, ‘Tuta absoluta’, wadda ta bulla a wasu gonakin da aka shuka Tutamar, musamman a jihohin Kano, Katsina da kuma Kaduna.

    Bugu da kari, bisa wasu alkaluma da hukumar gudanar da bincike a fannin aikin noma ta kasa (NAERLS) ta fitar, sun bayyana cewa, a shekarar 2024 a kasar nan, an noma Tumatir,  din da ya kai kimanin tan miliyan 3.73.

    A cewar alkaluman, kimin hekta 824,000 manoman Tumatir a fadin kasar nan suka noma, wanda hakan ya nuna cewa; ba a iya samun wadataccen nomansa a shekarar ta 2024 ba.

    Haka zalika, wannan fadakarwar za ta kara taimaka wa da kuma rabar da kayan aikin noman Tumatirin da suka kamata, musamman domin samar da daukin da ya kamata na dakile yaduwar wannana cuta da ke lalata gonakin da ake nomansu.

    Kaza lika, a karkashin wani shirin noma na nau’ikan Tumatir da ake kira a turance ‘HORTITOM4’ da kuma ‘HORTITOM5’, wasu masu bincike ne a fannin nomansa suka kirkiro da su a shekarar 2025.

    Mahukuntan, sun gudanar da yin gwaje-gwajen ne na  wannan shiri a wasu gonakin, na yin noman na Tumatir da kuma a gonakin da ake yin nomansa da rani.

    Wasu jami’ai a bangaren na noman nasa, sun bayyana cewa; wadannan nau’ikan na shirin noman Tumatirin, wato ‘HORTITOM4 da HORTITOM5’, sun kasance suna bijire wa dukkannin wani nau’i na cuta da za ta iya lalata shi, bayan an shuka Irin na Tumatirin.

    Bugu da kari, manomi zai kuma iya samun yin girbin Tumatirin da zai kai daga kimanin tan 21.7 zuwa tan 27.2 daga cikin kowacce hekta daya da ya shuka Irin na Tumatirin.

    “A kasar nan dai, Tumatir ba wai kadai ana nomansa tare kuma da yin amfani da shi ba ne, wata hanya ce da ke kara samar da kudaden shiga ga wadanda suka rungumi yin noman nasa, musamman a tsakanin kananan manoman da ke fadin wannan kasa.

    Kasar nan dai, ta kasance tana daya daga cikin manyan kasashen da ke a nahiyar Afirka, wajen nomansa da kuma samar da shi mai dimbin yawan gaske.

    Kazalika, a kwanakin baya, an ruwaito karamin Minista na Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wataccen Abinci ta Tarayya, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi ya bayyana cewa; fannin na kuma kara samar da ayyukanyi da yin jigilarsa zuwa kasuwanni, domin sayar da shi da kuma sarrafa shi zuwa wasu nau’ika daban-daban.

    Bugu da kari, Hukumar Kula da Bincike Kan Harkokin Noma da Ayyukan Malaman Gona ta Kasa, wato NAERLS a cikin wani rahotan da ta fitar, ta sake bayyana sake bullar cutar ta Tuta absoluta  a shekarar 2024, musamman a Jihar Kano.

    [ad_2]

    Source link

  • An Yi Musayar Kwarewa Game Da Ayyukan Rage Talauci Ga Masu Bukatar Musamman Na Sin a Dandalin FAO

    [ad_1]

    A yayin gasar wasannin Olympic ajin masu bukatar musamman ta lokacin hunturu ta Milan, an gudanar da wani taro mai taken “Raba hakkin ci gaba: Aikin rage talauci na masu bukata ta musamman na Sin” a hedkwatar hukumar abinci da aikin gona ta MDD ko FAO dake birnin Roma.

    Yayin taron na jiya Alhamis, shugaban kungiyar masu bukatar musamman ta kasar Sin Cheng Kai, ya ce Sin ta sanya kawar da talauci ga masu bukatar musamman a matsayin muhimmin bangare na kawar da talauci, kuma masu bukata ta musamman miliyan 7 da dubu dari 1 a karkarar kasar Sin sun fita daga kangin talauci, inda Sin ta gano hanyar rage talauci, da hana komawa cikinsa saboda nakasa.

    Babban daraktan hukumar abinci da aikin gona ta MDD ko FAO Qu Dongyu ya nuna cewa, kwarewar Sin ta zamo misali mai amfani ga al’ummar kasa da kasa, kuma FAO na son karfafa hadin gwiwa da bangaren na Sin.

    Kimanin mutane 100 daga wakilan kasashe daban daban, da jami’ai da masana sun halarci taron, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan kwarewar rage talauci tsakanin masu bukata ta musamman na Sin, tare da tattauna hanyoyin ci gabansu. (Amina Xu)

    [ad_2]

    Source link

  • Za a Gudanar Da Tattaunawa Kan Batun Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka a Faransa Daga Ranar 14 Zuwa 17 Ga Watan Maris

    [ad_1]

    Ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, bisa yarjejeniya tsakanin bangarorin Sin da Amurka, za a gudanar da tattaunawar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu a karo na 6, a Faransa daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Maris.

    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, zai jagoranci tawagar Sin don halartar taron. Bangarorin biyu za su tattauna kan batutuwan kasuwanci da suka shafe su bisa matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron koli na Busan da sauran tattaunawar da suka yi ta wayar tarho.(Amina Xu)

    [ad_2]

    Source link