Category: Latest News

  • Sarki Sanusi Ya Goyi Bayan Karfafa Tattalin Arzikin Mata

    [ad_1]

    Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce; ya kamata a yi watsi da labaran da ke nuna yadda mata ke shiga harkokin tattalin arziki a matsayin wani ra’ayi na kasashen waje, yana mai jaddada cewa; Musulunci ya bai wa mata ‘yancin cin gashin kai.

    Sanusi ya bayyana haka ne, a lokacin kaddamar da manufar karfafa tattalin arzikin mata (WEE) a hukumance ga Jihar Kano, wanda aka bunkasa ta hanyar hadin gwiwa da Cibiyar Bincike da Ayyuka (dRPC), tare da tallafin abokan hadin gwiwa da suka hada da Ford Foundation, Asusun Kalubalantar Kasuwancin Afirka da Gidauniyar Gates.

    • Kawar Da Dukkanin Haraji Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar Sin Daga Afirka Zai Bunkasa Cinikayyar Albarkatun Gona Na Afirka Ta Kudu
    • Kudaden Shiga Na Masana’Antun Kimiya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Da 16.1% a Watannin Janairu Da Fabrairun Wannan Shekara

    Sarkin ya ce, ci gaban al’ummar Musulmi na farko, ya ginu ne a kan yadda mata za su shiga harkar kasuwanci da bayar da tallafin karatu da kuma jagorancin al’umma, inda ya ce; karfafa wa tattalin arzikin mata, ya yi daidai da koyarwar Musulunci da kuma tarihin Kano.

    A cewarsa, Kano ba za ta iya samun ci gaba mai dorewa ba, idan har mata suka ci gaba da zama saniyar ware.

    “Tarihinmu da imaninmu a bayyane yake, domin kuwa, Musulunci ya bai wa mata ‘yancin mallakar kadarori, gado, kasuwanci da kuma harkokin tattalin arziki mai zaman kansa. Dole ne mu yi watsi da duk wani labari da ke nuna karfafa tattalin arzikin mata a matsayin bako ga kimarmu,” in ji shi.

    Sanusi ya kara da cewa, idan har Kano za ta yi gogayya a fannin tattalin arzikin duniya, dole ne ta yi amfani da basirar mata da kuma samar da ayyukan yi, tare da tabbatar da cewa; ‘ya’ya mata sun samu ilimi da fasahar zamani da ake bukata a tattalin arzikin zamani.

    Har ila yau, sarkin ya yi alkawarin tallafa wa Majalisar Masarautar Kano, wajen inganta manufofin, gami da bayar da shawarwari kan ilimin ’ya’ya mata, kula da zamantakewar al’umma da kuma karbuwar da al’umma ke yi na sana’ar mata.

    Da yake yin jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda kwamishinan raya karkara da al’adu, Abdulkadir Abdulsalam ya wakilta, ya bayyana kaddamar da manufofin a matsayin wani ci gaba a yunkurin jihar, na samar da ci gaba.

    Ya ce, gwamnati ta fara aiwatar da matakan tallafa wa mata ta hanyar kason kasafin kudi da kuma bayar da tallafin naira 50,000 ga mata 5,200 a duk wata a fadin kananan hukumomi 484 na jihar.

    Ita ma wadda ta kafa kungiyar Isa Wali Empowerment Initiatibe, Maryam Uwais, ta bukaci masu ruwa da tsaki, da su tabbatar ba a bar matan karkara da ‘yan mata a baya ba.

    Manufar shirin na nufin fitar da mata kimanin miliyan biyu daga kangin talauci tare da ba da gudummawar kusan kashi 30 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin Kano.

    [ad_2]

    Source link

  • Rashin Nasara A Hannun Koriya Ta Kudu Ba Zai Sanyaya Ƙwazonmu Ba – Kociyar D’Tigress

    [ad_1]

    Kociyar babbar ƙungiyar ƙwallon kwando ta matan Nijeriya wadda ake kira D’Tigress, Rena Wakama, ta ce rashin nasarar da suka yi a hannun Koriya ta Kudu ba zai sanyaya ƙwazon tawagarta ba, tana mai cewa za su dawo kan turbar nasara.

    Tawagar ta Nijeriya ta sha kashi da ci 77–60 a wasan da suka buga ranar Alhamis a gasar neman tikitin shiga FIBA Women’s Basketball World Cup. Wannan shi ne karo na farko da D’Tigress ta sha kashi a hannun Koriya ta Kudu, bayan an tashi 36–32 a rabin farko na wasan.

    Koriya

    • Osimhen Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa Na Bana A Kasar Turkiyya
    • Nijeriya Ta Koma Matsayi Na 26 A Jadawalin Iya Taka Leda Na Hukumar FIFA

    A wasan, Victoria Macaulay, wacce ta kasance ‘yar wasa mafi ƙwarewa (MVP) a wasan farko da suka buga da Colombia, ita ce ta fi taka rawa ga Nijeriya inda ta zura maki 22.

    D’Tigress za ta fafata da Philippines a ranar Asabar a wasa na gaba, kafin ta kara da ƙasashen Turai da suka haɗa da Faransa da Jamus.

    Koriya

    Wakama ta yaba da ƙoƙarin tawagar Koriya ta Kudu, tare da jaddada cewa za su yi amfani da darussan da suka koya daga wannan rashin nasara domin inganta bangarorin kai hari da kuma shiri mafi kyau a wasanni masu zuwa.

    [ad_2]

    Source link

  • GORON JUMA’A

    [ad_1]

    Jama’a barkanmu da kasancewa a wannan rana ta juma’a, barkanmu da ibada, fatan kowa zai sha ruwa lafiya Allah ya karbi ibadunmu amin.    Kamar kowane mako shafin GORON JUMA’A shafi ne da ya saba karbar sakonnin gaishe-gaishenku zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa, da na nesa, har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba.    A yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishenku da kuka aiko mana kamar haka:

    Sako daga Aminu I.B daga Gezawa:

    Ina gaida mahaifina da mahaifiyata Karimatu, ina gaida kanne na Yusufu, isma’ilu, Lauratu, Aisha, Amina da yayana Zainuddin. Ina gaida abokaina na makarantar Malam  Kallamu me allo kamar su; Idirisu, Dahiru, Ubaidullahi, da dai saurans, fatan sun yi juma’a lafiya. Ina gaida ‘yan garinmu gabadaya, Allah kuma ya karbi ibadunmu, Amin.

    Sako daga Umar Lawan Jihar Katsina:

    Ina gaida masoyiyata abar kaunata, rabin raina Maryama, sako na gaba ina gaida Amir Yellow, da Hafiz a ci a zauna lafiya, ina gaida mainasara Kabeer dan fulani, ina gaida kannena da ‘yan’uwana da duk abokaina da suke ko’ina, duk ina gaishe su da fatan sun yi juma’a lafiya, da fatan kuma sun sha ruwa lafiya.

    Sako daga Alaja Habiba Abdulmajid Jihar Kano:

    Gaisuwar goron Juma’a zuwa ga mahaifiyata da kuma mahaifina, da fatan sun yi juma’a lafiya. Ina gaida kawayena kamar su; Mufida, takwarata Habiba, Zeenat, Munira, Amira, Fatima, Zainab Zeey Baby, Fa’iza, Amiran Mama, Zarah ‘Yar Chakaras, Salma Beauty, da dai sauransu da fatan kowacce ta yi juma’a lafiya.

    Sako daga Aminu Shu’aibu Gidan Kaji Jahun:

    Ina gaishe da yayana Buhari, Tijjani da Aisha da Zainab, Musa, da Yusuf, da abokina Audu. Ina gaida Awaisu, Abdulsalam, Yawale, da Kalis, da kanwata Shahida, da Baba Ado, da Baba Al’a, da Baba Sabo, da Halle, da Muzambilu, da Kamilu, da Gambo, da Baban kifi, da Sulaiman, Baban Yaya, da fatan sun yi juma’a lafiya, kuma za su sha ruwa lafiya.

    Sako daga Habib Ahmad, Jihar Kano Unguwar Goron Dutse:

    Ina gaishe da ‘Yan’uwana da ke garin Jos, irinsu Kalisat, Ummussalama, khadijatu, Auwal, Isuhu da sauransu. Sannan ina gaishe da Malamina Malam Muttaka da kuma Baballe abokina, ina gaishe da ‘Yan kungiyarmu ta ball, da fatan sun yi juma’a lafiya.

    Sako daga Usman Bello Dikko daga Jihar Katsina:

    Ina gaida Hajiyata, Mamana kenan Haj. Karima, kowa ya bar gida, gida ya barshi, sai mahaifina Alh. Bello, sai kannena da abokaina, irinsu, Yahaya ikon Allah, su Idris Shettima, Dan Maraya Musa, Lukman a zauna lafiya, ina gaida matata Hafsat Bebin bebi, ina gaida ‘Yan’uwanta da kannenta gabadaya, da fatan sun yi juma’a lafiya.

    Sako daga Al’amin Shehu Jihar Kaduna:

    Assalam. Ina gaida Mahaifana, ina gaida sauran ‘Yan’uwana, da abokan karatuna wadanda na jima ban gansu ba, da wadanda ma muke haduwa har yanzu, ina gaida Ummi da Mami, da Fati, ina gaida Abdulkareem, Idris dan baiwa, ina gaida, Alhaji Ali mazan duniya, ina gaida sauran al’umma gaba daya da fatan kowa yayi sallar juma’a lafiya.

    Sako daga Gimbiya Aishat Sa’id Jihar Bauchi:

    Gaisuwar goron juma’a zuwa ga ‘yan’uwa musulmi, da fatan sun yi juma’a lafiya. Ina gaida Zakiya da Haj.Mero, da Haj. Marka, da Haj. Sa’adatu me tuwon shinkafa, ina gaida Maryamu Isah, ina gaida Dijen Malan Aminu, da Hidayatu Ibrahim, ina gaida Abubakar Mustapha, Arabian kingboi, Muhd Kalgo, Mika’il Adam, da sauransu. Da fatan kowa ya yi Juma’a lafiya.


    [ad_2]

    Source link

  • Mu Fahimci Alkur’ani Da Kyau, Don Mu Iya Zama Da Zamaninmu, Kuma Mu Yi Aiki Da Kayan Zamanin

    [ad_1]

    A ci gaba da karatun Tafsirin Alkur’ani wanda Shehu Ismaila Umar Almadda (Mai Diwani) ke gabatarwa a Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group dake cikin garin Kaduna, ya cigaba da karatu game da yadda za a fahimci Alkur’ani da kyau domin Musulmai su iya zama da abokan zamansu lafiya ta hanyar koyi da kyawawan dabi’u da Annabi SAW ya koya musu.

    Wannan lokacin yana da matukar amfani wanda ke bamu damar fahimtar kalmomin Allah, samun ilimi mai mahimmanci da hikima wadanda muke amfani da su a rayuwarmu ta yau da kullum, domin samun ci gaban al’umma. Shehu Ibrahim Inyass Kaulakh, ya saukaka mana fahimtar wannan littafi, inda muke amfani da littafin Tafsirin Alkur’anin da ya yi, kuma aka rubuta, mai suna “Fi Riyadit Tafsir”. Wannan littafi mai albarka, ya bude mana kofofin ilimi da yawa yayin da muke ci gaba da nazarinsa.

    • Sin Ta Himmatu Wajen Raya Ci Gaban Duniya Na Bai Daya
    • Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan ISWAP 20 A Jihar Yobe

    Kamar yadda aka bayyana a bara, a cewar mazhabarmu, babu wani abu a Alkur’ani da ya zama maimaici, komai daban ne kuma yana da ma’anar shi, kowace kalma tana da nata ma’anar ta musamman.

    Alhamdulillahi, da wannan, Sheikh Mai Diwani ya nuna gamsuwarsa kuma ya yaba wa mambobin Ahlul Faidhati Mai Diwani Group a wurare daban-daban da ya ziyarta a lokacin bikin Mauludi musamman a yankunan karkara saboda gagarumin kokarinsu, kan yadda suke aiwatar da darussa daga Tafsirin bara.

    Ya bayyana jajircewarsu a matsayin abin yabo kuma alama ce da ke nuna cewa makoma mai kyau tana nan gaba.

    Suratu Naml ta bayar labarin Annabi Sulaiman, dan Annabi Dauda kuma Sarkin Urushalima. An albarkace shi da ilimi da hikima mai yawa kuma Allah ya ba shi fahimtar sautin tsuntsaye, kwari, da sauran dabbobi. Surar ta bayyana cewa, an koya wa AnnabibSulemanu sautin tsuntsaye (Mantik), wanda ya bambanta da magana (Kalam). Kalam yana nufin harshen da kuke fahimta, yayin da Mantik ke nufin harshen da baku fahimta. Don haka, Allah ya albarkaci Sulemanu da kwarewa akan sauti da girgiza wanda muhimmin fanni ne na bincike na zamani.

    Surar ta kuma ambaci manyan tukwane a masarautar Sulemanu. Masu tafsiri na al’ada suna fassara su a matsayin tukwane na girki ga rundunarsa mai yawa saboda girmansu. Duk da haka, ana iya fahimtar wadannan tukwane ko kwano a matsayin “kwano na tauraron dan adam” wadanda za su iya karbar sigina, kamar yadda na’urorin zamani namu ke yi a yau. Mu’ujiza mafi ban mamaki a cikin surar ita ce, daddako kujerar sarautar Sarauniya Bilkis nan take daga Yemen zuwa Urushalima. Saboda haka, wannan sura ta kunshi fannoni daban-daban na kimiyya, amma duk da haka, wannan wani dan karamin bangare ne na ilimin da aka boye a cikin haruffan farkon surar (kuraman baki). Wannan shi ne dalilin da ya sa, surar ta ambaci ‘Ayatul-Kur’an’ ba ‘Ayatul-Kitab’ ba, sabida banbancin ma’anar Alkur’ani da Alkitab. Alkur’ani, ya kunshi ayoyin ilimi, yayin da Alkitabu kuwa, ke kunshe hukunce-hukunce, da dokok bayanai, da labarai, da sauransu.

    Muhkamat – Wadannan dokoki ne na Allah wadanda ke da tasiri a nan duniya domin rayuwarmu, ba za a iya soke su ba, sai dai za a iya gyara su cikin iyakokin Allah. Daga cikin ayoyi sama da 6,000 na Littafi, ayoyi 200 ne kawai tabbatattu da suka yi magana game da Muhkamatu; sauran sun kunshi tsantsar ilimi. Wasu ayoyi suna isar da ilimin Allah, wasu kuma suna magana ne game da ilimin duniya da halitta wanda ya zama mafi girman bangaren Littafin.

    An taba yin wani lokaci da mutane ke tsarkake zuciyarsu da nufin samun ilimi daga Ubangiji tun kafin zuwan Annabawa. A wannan zamani, mai neman wani ilimi, zai iya shiga dakin gwaje-gwaje don gano wani ilimi kuma zai samu abin da yake nema, kamar yadda mutanen baya ke yi kafin zuwan Annabawa don samun wani ilimi, bambancinsu yana cikin kwarewa, jarumtaka, da fahimta ne kawai.

    Tsarkake rai ko ruhi, shine ainihin Sufanci. Daga cikin Muhkamatu akwai ayoyi da yawa da ke kira ga tsarkake ruhi. Sauran ayoyin tabbatattu suna magana ne game da umarni da hani. Don haka, Mai Diwani ya yi kira ga kowa da kowa da ya yi kokari a kan hanyar Allah don samun ilimi mai zurfi.

    Sabida kokari da jajircewa, manyan kasashen yamma ke ci gaba da jagoranci a cikin ilimi da kirkire-kirkire. Kungiyar da ke bin irin wannan hanya ita ce Sufaye, saboda ibadarsu ga Allah. Ya bayyana cewa wasu manyan kasashen yamma suna mika kansu ga Shaidan don samun ilimi. A nan, Sheikh Mai Diwani ya ankarar da cewa, ba yana magana akan sun yi daidai ko ba daidai ba, amma akan niyyarsu.

    Ma’anar kalmar Shaidan a yaren mutanen yamma (haske), a matsayin babban ruhin mugunta, makiyin Allah, kuma mai jarrabar dan adam.

    Ta hanyar kwaikwayon koyarwarsa, irin wadannan mutanen na manyan kasashen yamma suka samun damar samun ilimin duniya mai zurfi – mai kyau da mara kyau, har ma da sarrafa lamarin halitta. Ayyukan sararin samaniya na Elon Musk sun zama misali na saurin ci gaban fasahar dan adam. Haka nan, Sufanci yana ba da wata hanya zuwa ga ilimi mai zurfi idan aka yi aiki da sadaukarwa, juriya, da mika wuya ga Shehi masani, da kuma kebewa na wani lokaci.

    Wannan tsohuwar koyarwar da ake cewa, bai kamata mutum ya rika yin tambayoyi game da maganganun addini ba, ta yi illa ga bangaren koyo; ilimi na gaskiya yana farawa da bincike. An tabbatar da wannan a cikin ayar: “Wa kurrabi zidni ilma – Ya Ubangiji, ka kara mini ilimi.” Annabi SAW ya roki Allah ya ba shi karin ilimi, kuma Allah ya amsa masa ta hanyar ba shi shawara da kada ya yi gaggawa wajen fassara wahayi, inda Ubangiji ya yi masa alkawarin ba shi zurfin fahimta.

    Don haka, idan wasu suna neman ilimi ta hanyar bauta wa Shaidan, to ya kamata mu nemi namu ta hanyar bauta wa Allah.

    Ilimi Yana Canzawa Tare da sabbin kayan bincike da tunani. Gwargwadon yadda kafi mayar da hankali game da neman ilimi, gwargwadon yadda za ka samu. Ilimi yana canzawa tare da kayan aikin da ake amfani da su don bincike.

    Yawancin abin da dan adam ya gano sun fito ne ta hanyar kayan aikin fasaha da aka kirkira ta hanyar ilimin da aka samu. Idan aka yi amfani da shi da kyau, fasahar zamani za ta iya ba wa Musulunci damar dawo da matsayinsa na duniya, inda za a iya daukar kowa a matsayin Musulmi bisa ga Littafi.

    Masana sun raba duniyar zamani zuwa matakai daga 1928 zuwa yanzu. Yanzu muna cikin lokacin juyin juya halin dijital da masana’antu da rashin tabbas mai girma.

    Sheikh Mai Diwani ya lura cewa, Ahlul Faidhati Mai Diwani Group ita ma ta fuskanci manyan canje-canje tun daga 2018. Shekarar 2025 ta nuna babban sauyi ga dan adam, saboda daidaituwar taurari biyar da ya faru a farkon shekarar.

    Yayin da duniya ke fuskantar kalubale masu tasowa kuma kasashen duniya ke barazanar tsunduma rikici ta hanyar amfani da karfin soja da tattalin arziki, wannan shi ne lokacin da za mu shirya kanmu ta hanyar ilimi. Za mu iya sanya Littafi Mai Tsarki ya zama abin koyi ga duniya mafi kyau, amma ta hanyar saukake koyarwarsa da ayyukansa. Da yardar Allah, Sheikh Ibrahim Niasse ya bude mana wannan kofa ta hanyar koyarwarsa, wanda ya nusar da tunaninmu don samun ilimi mai zurfi. A hankali, muna fara samun fahimtar Littafin bisa ga bukatun lokacinmu.

    [ad_2]

    Source link

  • Sojoji sun halaka shahararren Kwamandan ISWAP a Borno

    [ad_1]



    Sojojin rundunar haɗin gwiwa ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kashe Sa’ad, wani babban kwamandan ISWAP wanda ya addabi al’ummomin tafkin Chadi da yawaitar hare-haren ta’addaci a yankin.

    Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an kashe Sa’ad a ranar Talata ne a lokacin wani mummunan artabu da aka yi a Doron Baga, ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

    Majiyar tsaro na cewa, wannan Kwamandan na ISWAP ya shahara wajen kitsa munanan hare-hare, sace-sacen mutane da kuma sa haraji ba bisa ƙa’ida ba ga masunta na yankin.

    Ya mallaki manyan sassan hanyar ruwa, wanda hakan ya tilasta wa mazauna yankin biyan haraji don samun izinin kamun kifi.

    A cewar majiyoyin soji, ‘yan ta’addan sun kai hari a Doron Baga da misalin ƙarfe 1:00 na safe, inda suka isa da yawa a kan babura da kwale-kwale.

    Sojoji, ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar A.E. Ozemhoya, sun mayar da martani da ƙarfin wuta, inda suka daƙile harin tare da haifarwa ‘yan ta’addan asara mai yawa.

    ’Yan ta’addan sun gudu, da yawa suna ɗauke da gawarwakin su ‘yan uwan su ne da aka kashe a wannan gumurzu yayin da, da yawa daga cikin su suka tsere da munanan raunuka.

    A ranar Laraba, majiyoyi sun tabbatar da cewa Sa’ad yana cikin waɗanda aka kashe yayin da mazauna yankin suka ce an yi jana’izarsa a wannan rana.

    An bayyana Sa’ad a matsayin babban mutum a hare-haren da aka kai wa manoma, masunta da ‘yan kasuwa, kuma ya daɗe yana zama abin tsoro a yankin.

    Wani memba na rundunar haɗin gwiwa ta farar hula ya jaddada cewar da hannun Sa’ad a hare-hare da dama a wannan yankin na tafkin Chadi.


    [ad_2]

    Source link

  • Hobbasar Gwamna Abba Kan Titunan Birnin Kano

    [ad_1]

    Kamar dai yadda kowa ya sani ne, kowace gwamnati na kammala wa’adin lokacinta, ba tare da ta gama dukkan ayyukan da ke gabanta ba. Sau da dama, za ka ga idan gwamnati ta tafi, wata ta zo, za ka ga an samu wasu ayyukan da gwamnatin da ta gabata ba ta iya yi ba, ko ba ta samu damar yin su ba.

    Haka lamarin yake, kafin shigowar gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano, akwai wasu tituna masu muhimmanci a cikin kwaryar birni, wadanda gwamnatin baya ba ta samu yin su ba. Ba wai babu titunan ba ne a wuraren, a’a sai dai kawai sun lalace yadda suke jawo cunkushewar hanyoyin sufuri tare da jawo hadura a wasu lokutan.

    • Yawan Dazuzzuka Da Filin Ciyayi a Kasar Sin Ya Wuce Kashi 56%
    • Majalisar NPC Ta Gudanar Da Zaman Rufe Taronta Na Shekara-shekara Na Bana

    Domin kauce wa matsalolin da ire-iren wadannan lalatattun tituna ke haifarwa, sai gwamna ya shigo da wani tsari na kula da titunan cikin birni da ya ba shi suna; “Urban Renewal Project.”

    Ta karkashin wannan shiri ne aka samu aka duba titunan da suka ji jiki, suke kuma kawo tare da kara cunkoson ababen hawa, babu gaira babu dalili. Amman fa hanyar da aka fito da ita wajen tantance ire-iren titunan da za a taba, ta taimaka matuka gaya wajen lalubo wuraren da suka dade a dankwafe, ba tare da kula ba yadda ya kamata.

    Wannan fa ba kuma a maganar wasu katafaren gadoji da gwamnatin ke yi a halin da ake ciki ba. Akwai katafariyar gadar Tal’udu da kuma daya katafariyar gadar ta Kofar Dan Agundi. Dukkan wadannan gadoji, an yi nisa sosai a aikinsu. Sannan kuma, irin gadojin nan ne na ‘da gani babu tambaya’. A nan, ina maganar yadda ayyukan ke da karko da kuma kayatarwa.

    Daga lokacin da aka kammala wadannan gadoji, za kuma a ga da wace fuska ce kuma abokan adawar siyasa, masu cewa gwamna Abba bai taba kammala wani ko wasu katafaren ayyuka ba, tun bayan shigowarsa, za su kalli mutane? A nan, ba fa ana maganar wasu ayyukan da aka rigaya aka kammala ba.

    Kasancewar shi birnin Kano ya shahara wajen samun yawan zirga-zirga na ababen hawa da ma wadanda ke tafiya kafafuwansu, ya sa gyare-gyaren titunan da ake yi suka yi tasirin gaske, wajen kara saukaka wa al’umma wahalar sufuri a cikin birnin na Kano.

    Kasancewar Kano garin kasuwanci ne, hakan ta sa aka kara samun sauki da walwala wajen zirga-zirgar harkokin kasuwanci a cikin kwaryar birnin na Kano. Musamman ma da yake wasu daga cikin titunan da aka kammala ko aka kusa kammala gyaransu, suna da alaka ta kut-da-kut na kusanci da wasu kasuwannin namu.

    A dai karkashin wancan shiri na ‘Urban Renewal Project’, gwamnatin ta mai girma Abba, ta kammala gyaran titunan, Lodgeroad da Murtala Muhammad Way da titin Airport da Club road da titin Yahaya Gusau da Titin Sharada da kuma sauran makamantansu. Ba wai gyara titunan ba kawai, an kawata su, kuma an yi musu aiki mai karko da kyawun gani.

    Baya ga wadanda aka kammala yin su, akwai kuma wadanda a halin yanzu ana kan yin nasu gyaran. Wasu an kusa kammala su. Daga cikin wadanda ake kan aikin nasu, akwai titin Audu Bako da Lamido Crescent da Sulaiman Crescent da titin da ya kewaye kasuwar Farm Centre da Katsina road da titin Sabo Bakinzuwo da kuma titin Amadu Sambo, wanda ya taso daga titin Gandun Albasa zuwa titin Sharada.

    Babban abin ban sha’awar ma shi ne, yadda jama’ar da ke amfana da wadannan hanyoyi ke nuna farincikinsu ga wadannan gyare-gyare da ake yi, tare da kara yaba wa zurfin tunanin gwamnan, musamman wajen gano cewa; ya kamata a sauwaka wa mutane ta bangaren gyara tituna, domin samun sufuri mai inganci a birnin na Kano.

    Da yawa daga cikin wasu da na dan yi wani kwarya-kwaryar bincike a kai sun tabbatar da cewa, ba wai samar da kyawawan hanyoyin kawai ba, sun ma tabbatar da cewa; hatta ababen hawansu, sun kara samun lafiya. Saboda an fara ceto ababen hawan nasu daga kwazazzaban da suka yi wa titunan kaca-kaca kafin wannan lokaci.

    Misalin titunan Lodge road da na Sabo Bakinzuwo, wadanda daya yake jikin gidan Gwamnatin Jihar Kano, da kuma dayan da ke tsallaken gidan gwamnatin, ba karamar dabara aka yi ba, wajen yi musu gagarumin aikin da ake kan yi musu. Misali, shi Lodge road, an kammala gyara shi har ma an sa masa fitilu da wasu furanni masu kayatarwa. Sannan ga magudanan ruwa na zamani da aka yi musu.

    Yanzu ba abu ne mai wahala ba, idan aka ce wanda ya dan yi ‘yan watanni bai shiga Kano ba, idan ya je yanzu daidai yake da ya bata bata, saboda yadda ake ta kawata wurare da hanyoyi babu kakkautawa. Wannan shirin na kyautata titunan cikin birni, ya yi daidai da yadda gwamnan ke yi, wajen kula da wasu bangarori na gwamnatinsa.

    Wani babban abin kawatarwa kuma shi ne, yadda aka kara buda titunan, domin su kara fadi a samu isassun hanyoyin sufuri, ba tare da samun wani cikas a nan gaba ba.

    Haka zalika, wani abin ban sha’awa ma ga wannan hobbasa da gwamnan ke yi shi ne, tun bayan hayewarsa kan karaga mulkin, ya sha alwashin inganta bangaren sufuri a jihar, wanda hakan ya hada da kara inganta hanyoyin sufurin da ya hada da titunan da kuma sauran ababen sufurin, wato ababen hawa na al’umma.

    [ad_2]

    Source link

  • Ramadan: Kamfanin Indomie Ya Shirya Shan Ruwa A Gidajen Kwastomominsa A Kaduna

    [ad_1]

    Kamfanin taliyar Indomie ya shirya wani taron shan ruwa na musamman a Jihar Kaduna domin karrama mutanen da suka yi nasara a gasar tambayoyin Ramadan da aka gudanar ta gidajen rediyo a jihar, kamar yadda ake yi a jihohin Kano da Sakkwato, tare da ƙara ƙarfafa alaƙa da al’umma a wannan wata mai alfarma.

    Shirin na daga cikin shirye-shiryen da kamfanin ya tsara domin samar da farin ciki a lokacin buɗa-baki tare da kwastomominsa da suka halarci gasar amsa tambayoyin da aka gabatar a gidajen rediyo a lokacin watan Ramadan.

    • Indomie Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Al’adu A Bikin Kamun Kifi Na Argungu Karo Na 61
    • NAFDAC Ta Haramta Shigo Da Indomie Saboda Zargin Sanya Ciwon Daji

    Nura Yusuf Muhammad da Maryam Husaini ne suka zama zakarun gasar tambayoyin a Jihar Kaduna, bayan sun nuna ƙwarewa wajen amsa tambayoyin da aka gabatar a shirin.

    Domin murnar wannan nasara tasu, Indomie ta shirya wani taron shan ruwa na musamman a Unguwar Millennium City da ke jihar, inda waɗanda suka yi nasara tare da iyalansu da sauran al’ummar yankin suka taru domin buɗa-baki tare da Indomie.

    Taron ya samar da yanayi na farin ciki da annashuwa ga mahalarta, inda aka raba abinci da kuma kyaututtuka a lokacin buɗa-baki.

    A yayin taron, waɗanda suka yi nasara sun bayyana farin cikinsu tare da nuna godiya ga kamfanin Indomie bisa wannan karramawa da aka yi musu. Sun ce shirin ya ƙara sanya musu farin ciki a watan Ramadan tare da ba su damar yin buɗa-baki tare da iyalansu da maƙwabta cikin annashuwa.

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi nasara ya bayyana cewa wannan kyakkyawan shiri ya sa watan Ramadan ya zama abin tunawa a gare su, tare da ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin al’umma.

    Wasu daga cikin mahalarta taron sun yaba da wannan shiri, inda suka ce irin wannan ɗawainiya ta kamfanoni masu zaman kansu irin Indomie na taimakawa wajen ƙarfafa zumunci da haɗin kai da taimakon juna a tsakanin al’umma a wannan lokaci na Ramadan.

    Da yake jawabi a wajen taron, wakilin kamfanin Indomie, Gabriel Ajeh, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin kamfanin na kusantar al’umma tare da karrama waɗanda suka halarci gasar tambayoyin Ramadan.

    Ya ƙara da cewa karrama waɗanda suka yi nasara a irin wannan taro na shan ruwa na taimakawa wajen sanya shirin ya zama abin tunawa, tare da ƙarfafa alaƙa tsakanin kamfanin da kwastomominsa.

    Har ila yau, kamfanin Indomie ya faɗaɗa damar shiga gasar ta hanyar shafukansa na sada-zumunta na yanar gizo mai suna Indomie Arewa, inda ake wallafa tambayoyi a kowace rana domin bai wa waɗanda ba su samu damar sauraron shirin rediyo ba damar shiga gasar.

    Mutanen da suka amsa tambayoyin daidai a waɗannan shafuka na sada-zumunta suna samun kyautar kwalin taliyar Indomie domin taimaka wa iyalai a wannan lokaci na watan Ramadan.

    Kamfanin ya bayyana cewa wannan shiri na nuna ƙudurinsa na tallafa wa al’umma da kuma samar da farin ciki a tsakanin jama’a a watan Ramadan mai alfarma.

    [ad_2]

    Source link

  • An Samu Karuwar Kayan Da Aka Sauke A Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Da Kashi 24.8 A 2025 —Rahoto

    [ad_1]

    NPA na kasa Dakta Abubakar Dantsoho, ya alakanta wannan karuwar, a matsayin babban ci gaba, da aka samar a fannin na sufurin Jiragen Ruwan.

    “ Wannan karuwar ta kasance daga cikin daya da aka samu a kasar, musamman a cikin tarihin tafiyar da harkar sufurin Jiragen Ruwan kasar nna, wanda hakan ya kuma kara saita kara tabbatar da yin gasa a fannin, musamman a tsakanin jiga-jigan ‘yan kasuwa, da ke a fadin duniya, “ A cewar,” Dantsoho.

    • Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan ISWAP 20 A Jihar Yobe
    • Gwamna Uba Sani Bai Nuna Goyon Bayan Wani Ɗan Takarar Majalisa Ba – Gwamnatin Kaduna

    Wasu masu yin fashin baki a fannin sun sanar da cewa, karuwar ta kai kusan ta kaso 59.2, musamman saboda tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta samar a fannin, wanda hakan ya kara habaka hada-hadar da bata shifi bangaren man fetur ba.

    Bugu da kari, kwantainar da aka fitar da su daga cikin kasar sun kai kaso Containerised 25.7 wanda hakan ya nuna cewa, jimlarsu sun kai na miliyan 2.1.

    Kazalika, kwatianr da aka shigo da su cikin kasar sun karu zuwa kaso 32.8, wanda hakan ya nuna irin bukatar da ake da su, a cikin kasar, inda kuma karin wasu kawantar da aka fitar zuwa ketare, suka karu zuwa kaso 3.1.

    Hakazalika, an kuma samu wata karuwar wajen shiga kwantai daga Tashoshin Jiragen Ruwan kasar zuwa Afirka ta Yamma da kuma zuwa Afirka ta Tsakiya, da suka kai kaso 205.8.

    Rahoton ya nuna cewa, a Tashar Jiragen Ruwa ta Lekki an sauke kayan da suka kai kaso 40.6 inda a Tashar Onne, aka sauke kaso 19.1  sai kuma a ta Apapa, aka sauke kaso 16.7.

    Bugu da kari, a Tashar Lekki a nan ne,  Jiragen Ruwa suka fi sauka,  inda ake da, 55,712,  sai kuma Tashar Onne, da ke bi mata da kayan  53,022.

    A tashohin Apapa da Tin Can Island, sun tarbi Jiragen Ruwa da suka kai akalla 33,251 zuwa 36,909, inda kuma ta Delta, ta tabi kayan da suka kai 17,414.

    Ko da yake, Tashar Tin Can Island ce da fi sauke Jiragen Ruwa, inda suka kai kaso 22.7, inda kuma Tashoshin Lekki da Onne, suka tarbi kasa da Jiragen Ruwan da suka yo safarar kaya.

    Gaba dayan safarar ta kusan kai wa ta kaso 12 4,477 wanda hakan ya nuna cewa, an samu gagarumin karuwa a fannin.

    Kazalika, karin da aka samu na kaso 205.8 na sauke kwantainoni, hakan ya nuna irin kara habakar hada-hadar da ake gudanarwa a fannin na sufurin Jiragen Ruwan kasar.

    Dantsoho ya sanar da cewa, karin da ake sa ran samu a zango nag aba, zai samu ne, saboda yadda gwamnatin tarayya ta samar da tsarin zamani na tfiyar da hada-hadar sururin Jiregn Ruwan kasar wato tsarin NSW.

    A cewarsa, wannan zamantar da aikin, zai mayar da hankali ne, wajen samar da kayan aiki na zamani da za a yi amfani da su a fannnin.

    [ad_2]

    Source link

  • Ranar Mata Ta Duniya: Mata Kashi 60 A NPA Ke Rike Da Mukamai Na Musamman —Dantsoho

    [ad_1]

    Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Kasa NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya sanar da cewa, Hukumar ba ta mayar da mata saniyar ware ba, domin kuwa, kaso 60 a cikin dari na matan da ke aiki a Hukumar, na rike da mukaman Mataimakin Injiniya.

    Wannan furucin na Dantsoho, na zuwa ne, a yayin da aka gudanar da zagowar bikin ranar mata duniya, da aka saba gudanarwa a duk ranar 8 na kowanne watan Maris na na kowacce shekara.

    • Yawan Dazuzzuka Da Filin Ciyayi a Kasar Sin Ya Wuce Kashi 56%
    • Sin Ta Himmatu Wajen Raya Ci Gaban Duniya Na Bai Daya

    Shugaban ya bayyana cewa, wannan matakin na nuna cewa, Hukumar ba ta kyamar mata kuma tana janyo su a Niki, domin su ma ayi tafiya da su, yadda sima za su bayar da ta su gudunmawar, wajen kara ciyar da kasar gaba.

    Dantsoho ya bayyana haka a jawabinsa a taron bikin zagayowar ranar, musamman ga matan da ke yin aiki, a Hukumar.

    A cewarsa,  nade-naden mukamai da aka yiwa matan da ke aiki a Hukumar, na daga cikin matakan kara ba su damar gudanar da shugabanci, a Hukumar.

    “Mata na rike da mukamai da suka kai kaso 60 a cikin dari a Hukumar ta NPA, inda kuma maza ke rike da mukamai kaso 40 a cikin dari, a Hukumar,” Inji Dantsoho.

    Ya kara da cewa, wadannan matakan sun nuna a zahiri irin, mayar da hankali da Hukumar ta ke ci gaba da yi, na bai wa mata damar samun cin nasara a fannin na sufurin Jiragen Ruwa na kasar nyi, hakan ya nuna cewa, Mad’s da ke aiki a Hukumar, ba su iya mama ye ayyukan Hukumar ba…

    Shugaban na Hukumar ta NPA ya jinhinawa matan da ke aiki a Hukumar musamman kan gudunmawar da su ke ci gaba da bayarwa, a sassa da ban da ban na Hukumar.

    Shugaban ya bayyana cewa, matan da ke aiki a Hukumar na kara samun daukaka wajen gudanar da ayyukan su tare da kuma yin aiki da kwarwa, a bangaren gudanar da harkar mulki, a Hukumar.

    Dantsoho ya sanar da cewa, karuwar gudunmawar da matan da ke aiki a Hukumar ke ci gaba da yi, hakan ya sanya maza ‘yan uwansu, ba su iya mamaye daukacin ayyukan da ake gudanarwa a Hukumar ba.

    [ad_2]

    Source link

  • Birtaniya ta fara shirye-shiryen tarbar Tinubu da mai ɗakinsa

    [ad_1]



    Hukumomi a ƙasar Birtaniya sun sanar da ɗaukar ƙwararan matakan tsaro, waɗanda suka haɗa da rufe hanyoyi na ɗan lokaci da kuma takaita zirga-zirga a sararin samaniya, gabannin ziyarar aiki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ƙasar.

    Ziyarar, wadda Sarki Charles na III zai karbi baƙuncinta, an shirya fara ta ne a ranar 18 ga watan Maris, inda ake sa ran shugaban Nijeriyar zai isa tare da uwargidansa, Oluremi Tinubu domin gudanar da liyafar tarba a fadar Windsor Castle.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Thames ɓalley ta wallafa a shafinta na intanet, ta bayyana cewa tana haɗa gwiwa da hukumomin gundumar Royal Borough of Windsor da Maidenhead, da ma’aikatan fadar sarki, da sauran abokan hulɗa domin tsara dabarun tsaro kafin ziyarar.

    ’Yan sandan sun bayyana cewa, za a faɗaɗa takunkumin zirga-zirgar sararin samaniya da ke kan fadar Windsor Castle a ranar 18 ga Maris, tun daga ƙarfe 7 na safe zuwa ƙarfe 11:59 na dare, a matsayin ɓangare na shirye-shiryen tsaro.

    Da yake ƙarin bayani kan shirye-shiryen, babban jami’in ’yan sanda Adrian Hall na sashin haɗin gwiwa na rundunar, ya ce waɗannan matakan wani ɓangare ne na babban shirin tsaro na ziyarar shugaban Najeriya Tinubu a mako mai zuwa.

    “Takunkumin sararin samaniya ɓangare ɗaya ne kawai na ƙwararan matakan tsaronmu na ziyarar Shugaba Tinubu na Nijeriya a mako mai zuwa; akwai matakai da dama da za ku gani, wasu kuma ba za ku gani ba,” in ji Hall.

    Ya ƙara da cewa: “A matsayinmu na runduna, muna da ƙwarewa sosai wajen tabbatar da tsaro a tarukan masarauta a Windsor, kuma an ɗauki lokaci mai tsawo ana tsare-tsare da shirye-shirye domin wannan taron.”

    Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya karya dokar zirga-zirgar jiragen sama za a ɗauke shi a matsayin mai aikata laifi. “Za mu ɗauki tsauraran matakai wajen tabbatar da bin waɗannan dokoki; duk wanda ya karya su yana aikata laifi ne a ƙarƙashin dokar zirga-zirgar sararin samaniya kuma ana iya kama shi,” in ji shi.

    A cewar Hall, aikin tsaron zai haɗa da jami’ai masu ƙwarewa na musamman, waɗanda suka haɗa da ƙungiyoyin bincike, ’yan sanda masu dawakai, sashin kula da zirga-zirgar hanyoyi, da jami’ai masu ɗauke da makami, tare da jami’an ‘yan sandan unguwa.

    Hukumomin sun kuma shirya yin amfani da dukkan kyamarorin tsaro (CCTV) na Windsor da sauran dabarun kariya na zamani domin tabbatar da nasarar aikin.


    [ad_2]

    Source link