Category: Latest News

  • Yakin Iran: Duniya Na Fuskantar Tsadar Kayan Abinci Da Man Fetur

    [ad_1]

    Rikicin da ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya, ya fara shafar Nijeriya kai tsaye, sakamakon tashin farashin danyen mai a duniya, lamarin da ya haifar da karin farashin sufuri da kuma farashin kayan abinci a sassa da dama na kasar.

    A manyan biranen kasar da suka hada da Legas, Abuja, Kano, Kaduna, Fatakwal da Yenagoa, masu ababen hawa na kokawa da sabon farashin man fetur, wanda a halin yanzu ya kai daga tsakanin naira 1,020 zuwa N1,100 kan kowace lita a gidajen sayar da man da dama.

    • Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan ISWAP 20 A Jihar Yobe
    • Kudaden Shiga Na Masana’Antun Kimiya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Da 16.1% a Watannin Janairu Da Fabrairun Wannan Shekara

    Wannan matsala ta haifar da damuwa a tsakanin mazauna wadannan yankuna, musamman ga masu harkar sufuri da kuma ’yan kasuwa, wadanda ke fargabar karuwar za ta iya sake kawo tabarbarewar tsadar rayuwa da kuma sauran al’amuran yau da kullum.

    Sabon tashin farashin man fetur din na da nasaba da tashin farashin danyen mai a duniya, biyo bayan tashin hankalin da ya barke a tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, lamarin da ya kawo cikas ga hasashen samar da man a kasuwannin mai na kasa da kasa.

    An samu hauhawar farashin man a Legas, Abuja, Kano, Fatakwal da sauransu.

    A Legas, matafiya da magidanta sun ce; tuni sun fara kashe kudade wajen sufuri da sayen kayan abinci, biyo bayan karin farashin man fetur din da aka samu.

    Binciken da Daily trust ta yi a gidajen mai da dama ya nuna cewa; yanzu ana sayar da kowace litar mai a tsakanin naira 1,050 zuwa naira 1,100, ya danganta da gidan man.

    A gidajen sayar da man fetur na Northwest Petroleum, ana sayar da man a kan kusan naira 1,050 kan kowace lita, yayin da gida mai na TotalEnergies, ke sayar da shi a kan naira 1,055 kan kowace lita.

    Kamfanonin mai na MRS, suna sayar da shi a kan kusan naira 1,057, yayin da Kamfanonin Mobil ke karbar naira 1,100 kan kowace lita.

    Tashin farashin man fetur din, ko kadan bai haifar da da mai ido a sassan sufuri da na abinci ba, lamarin da ya kara sanya kashe kudade a hidimomin yau da na kullum, musamman ga matafiya da kuma magidanta, wadanda tuni suka fara kokawa da wannan tsada ta rayuwa.

    Masu safarar kayayyaki na kasuwanci, sun fara daidaita farashin kayayyakinsu da farashin man fetur, saboda tsadar da man din ya yi.

    Ekundayo Oladimeji, wani direban haya na bas da ke zirga-zirga tsakanin Ogba da Ikeja, ya tabbatar da cewa; tuni farashin sufuri ya tashi daga naira 400 zuwa naira 500, sakamakon tashin farashin man fetur.

    “Babu shakka, akwai yiwuwar kara kudin sufuri, mun fara karbar naira 500 daga Ogba zuwa Ikeja.

    “A ranar Litinin, zai iya karuwa zuwa naira 700. Na sayi mai a kan N935 a ranar Juma’a, amma a safiyar jiya (Asabar) na sayo shi kan N1,057, kuma farashin na iya ci gaba da karuwa,” in ji shi.

    Wasu masu jigilar kayayyaki sun ce, suna kokawa saboda juriyar da fasinjoji suke da ita, musamman idan aka lura da yadda farashin yake yanzu.

    Nelson, wanda ke kula da titin Ogba–Agege, ya ce; “Ba mu kara farashin ba, saboda tuni fasinjoji dama suna kokawa a kan farashin kudin da ake biya a halin yanzu, amma karin farashin man fetur ya shafi kudaden da muke kashewa, sannan ya kuma rage ribar da muke samu.”

    Har ila yau, ana kuma ganin tasirin karin farashin man fetur a kasuwannin abinci da ke fadin Jihar Legas, inda farashin jigilar kayan amfanin gona ya yi tashin gwauron zabi.

    ‘Yan kasuwan dai sun ce, farashin barkono da tumatur, sun yi tashin gwauron zabo a cikin kankanin lokaci, inda suka ce; farashin sufuri ya yi matukar tsada.

    Yanzu haka, ana sayar da barkono a kan naira 82,000, idan aka kwatanta da naira 18,000 a baya.

    Matsakaicin buhu ya karu zuwa kusan naira 122,000 daga naira 22,000, yayin da babban buhu ya kai kusan naira 172,000, idan aka kwatanta shi da kusan naira 70,000 a baya.

    Haka zalika, farashin tumatur ya yi tashin gwauron zabi, inda a baya ake sayar da buhu kan naira 22,000, yanzu kuma ya kai kimanin naira 50,000, yayin da babban buhu ya tashi daga kimanin naira 62,000 zuwa naira 125,000.

    Oyekale Oluwasegun, wani mazaunin Legas da ke yin zirga-zirga a kullum don zuwa aiki, ya ce; karin kudin da aka yi masa ya shafi kudaden da yake kashewa duk wata.

    A cewarsa, tafiya daga Powerline zuwa Ogba, wanda a baya yake biyan naira 200, yanzu ya kai naira 300.

    “Na riga na kasafta kudina da zan kashe a wata, amma wannan karin ya rusa min lissafin nawa,” in ji shi.

    “Na fahimci cewa, tattalin arziki yana fuskantar matsin lamba daga wasu dalilai na waje, amma akwai bukatar gwamnati ta dauki matakin gaggawa kafin lamarin ya kara tabarbarewa.”

    Wasu gidajen man a Legas da Abuja da Kano a ‘yan kwanakin da suka gabata, wadanda suka hada da AY Maikifi, Aliko Oil da AA Rano, sun daidaita farashin famfunansu daga kimanin naira 980 kan kowace lita zuwa tsakanin naira 1,050 zuwa naira 1,104, yayin da wasu gidajen man suke sayarwa a kan naira 1,060, kan kowace lita.

    A gidajen man da ke karkashin Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC), ana sayar da man fetur a kan Naira 1,084 kan kowace lita, yayin da AMMASCO da ke titin Kotu ke sayar da man a kan naira 1,104 a ranar Lahadi.

    Wani mazaunin garin, Abubakar Danzaria, ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro, inda ya yi gargadin cewa; karin farashin man da ake yi a lokuta daban-daban na iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasar, idan har aka ci gaba da hakan.

    “Muna gudanar da azumin watan Ramadan, kuma babu zato babu tsammani farashin mai yana karuwa akai-akai,” in ji shi.

    Masu harkar sufuri a jihar, sun kara kudin sufuri a jihar, sakamakon tashin farashin man fetur.

    Saifullahi Rabi’u, mai sana’ar tuka Adaidaita Sahu a Kano, ya ce; ya sayi man fetur a kan naira 1,060, kan kowace lita a gidan mai a karshen makon da ya gabata.

    “Lokacin da farashin mai ya karu, dole ne mu daidaita namu farashin,” in ji shi. “Idan muka ci gaba da cajin adadin abin da muke caza a da, ko shakka babu za mu yi asara,” in ji shi.

    A wasu sassan Abuja, yanzu ana sayar da man fetur a tsakanin naira 1,050 zuwa 1,080, ya danganta da wurin da ake sayar da mai, sabanin yadda yake a da a tsakanin N845 zuwa N875.

    [ad_2]

    Source link

  • Ana iya samun ɓullar cutar sanƙarau a jihohi 11 — NiMet

    [ad_1]



    Hukumar binciken yanayi a Nijeriya (NiMet) ta gano jihohi 11 da ke fuskantar barazanar hatsarin kamuwa da cutar sanƙarau mai taɓa lakar baya da kwakwalwa, inda ta yi kira ga mazauna yankunan da su kasance cikin shiri tare da ɗaukar matakan kariya.

    A cikin wata shawarwarin kiwon lafiya da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta yi gargaɗin kan  jihohin Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe, da Borno a halin yanzu suna fuskantar barazanar ɓarkewar cutar.

    A cewar NiMet, ciwon sanƙarau wata cuta ce mai tsanani da ke shafar ƙwaƙwalwa da lakar baya, wadda ƙwayar cutar Neisseria meningitis ke haddasawa.

    Hukumar ta ce: “Ciwon sanƙarau cuta ce mai tsanani da ke shafar ƙwaƙwalwa da lakar baya, kuma tana yaɗuwa ta hanyar ɗigon ruwan numfashi, musamman a wuraren da mutane suka yi cunkoso ko kuma inda iska ba ta ratsawa yadda ya kamata.”

    Hukumar ta yi gargaɗin cewa cutar na iya yin ƙamari cikin sauri kuma ta zama barazana ga rayuwa idan ba a yi maganinta cikin gaggawa ba.

    “Cutar na iya yin ƙamari cikin sauri kuma tana iya kashe mutum cikin sa’o’i kaɗan idan ba a yi jinya ba. Sai dai, gano cutar da wuri da kuma amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta  na inganta damar rayuwa da rage raɗaɗin matsalolin cutar,” in ji NiMet.

    Haka kuma, shawarwarin sun bayyana rukunin mutanen da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar:

    “Yara da matasa, mutanen da ke zaune a wuraren cunkoso, mutanen da ke rayuwa a wurare masu ƙura da bushewa, da kuma waɗanda garkuwar jikinsu ba ta da ƙarfi su ne suka fi fuskantar haɗari.”

    NiMet ta buƙaci mazauna jihohin da abin ya shafa da su sanya ido kan alamun farko na cutar, waɗanda suka haɗa da: zazzaɓi mai zafi farat ɗaya, ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, amai sannan su gaggauta neman taimakon likita idan waɗannan alamun suka bayyana.


    [ad_2]

    Source link

  • A Magance Karancin Abinci Mai Gina Jiki A Nijeriya

    [ad_1]

    A bisa kokarin da ake yi magance kalubalen rashin abinci mai gina jiki musamman a tsakanin yara kanana da kuma kara karafawa iyalai a daukacin fadin kasar nan guwai, hakan ya sanya, a kwnan baya, Sanata Remi Tinubu, mai dakin shugaban kasa,ta kaddamar da wani shiri na kasa, domin a magance wannan matsalar.

    A jawabinta a yayin kaddamarwar Remi da alakanta wannan matsalar a matsayin gagarumar matsala wadda ake bukatar a magance ta, matakin kasa, a karkashin wannan shirin.

    Shirin dai, za a  fara wanzar da shi ne gadan-gadan a cikin watan Afirilun wannan shekarar, wanda kuma aka tsara shi musamman domin inganta samar da abinci mai gina jiki a tsakanin marasa karfi da yara da shekarun su, suka faa daga shekaru shida.

    A cewar Remi, za a gudanar da shirin ne a hukumomin kiwon kula da kiwon lafiya na farko da ke a daukacin fadin kasar, inda a  nan ne, za gudanar da yin rijistar iyalan da aka zabo domin amfana da shirin.

    Ta kara da cewa, wadanda za su amfana, za a wayar masu da kai da kuma raba masu kayan abinici masu gina jiki da aka noma a kasar nan.

    Taron kadamawar, ya samu halartar Sarakunan Gargajiya, Malaman Addini Ministan kiwon lafiya Farfesa Muhammad Pate ya sanar da cewa, kimanin yara kanana kaso 40 a cikin dari a kasar, na fuskantar matsalar karamcin abinci mai gina jiki, wanda ya ce, wannann matsalar, na fara ne, tun kafin a haifi yaran.

    A cewarsa, rashin abinci mai gina jiki, na kara haddasa mutuwar yara kanana, tun suna gakiyar tasowarsu, da hana su samun ingantaccen ilimi da fuskantar kalubale na dogon zango a rayuwarsu.

    A bisa ra’ayin mu a  wannan Jaridar yakar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara kanana a kasar abu ne, da yake da matukar mahimanci, musamman duba da cewa, a duk makon farko na kowanne watan Agustan shekara, ana gudanar da fadakarwa ta duniya kan mahimmancin shawar da jarirai  Nonon Uwa.

    Kazalika, tun kafin a fara fustantar kalubalen rashin tsaro a kasar, da kuma dimbin abincin da ake da shi a kasar, yara kanana na ci gaba da fuskantar karancin abinci mai gina jiki.

    A wasu shekarun baya, Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato  UNICEF ta yi hadaka da shirin samar da abinci wato RUTF na Gwamnatin Tarayya wa, musamman wannan shirin an samar da shi ne, yadda za a rinka yin amfani Gydar da aka sarrafa, domin magance babbar matsalar karancin abinci mai gina jiki a Arewacin Nijeriya.

    Bugu da kari, shayar da Jarirai Nonon Uwa zalla, ya ci gaba da kasance kan akalla kaso 29 a cikin dari, a wan Agustan 2025, inda hakan ya nuna shayarwar, ta ragu da kaso 50 a cikin dari, kamar yadda Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Duniya da Gwamnatin Tarayya, suka ayyana ana son a cimma

    A cewar UNICEF, duk da cewa, mata masu shayarwa a kasar, sun kirkiro da tsarin shayarwa da ya kao kaso 90 a cikin dari, amma har yanzu, ana ci gaba da kai wa wata shida na sahayar da Jarirai Nonon Uwa, wanda hakan ya nuna cewa, akwai bukatar kara samar da tsare-tsare da bayar da goyon baya, a guraren yin aiki yadda mata ma’aikata masu shayarwa, za su samu karin damar shayar  da Jariransu, a wajen da suke yin aiki.

    A shekaru da dama da suka gabata Gwamnatin Tarayya ta sha kikiro da dauki iri da ban da ban na magance kalubalen rashin abinci mai gina jiki, a tsakanin yara kanana, sai dai, Gwamnatin na samar da daukin ne kawai, na wucin gadi.

    Bugu da kari, wannan Jaridar za ta iya tunawa, a shekarar 2025, Gwmantin Tarayya ta kiriro da wani shiri na samar da abinci mai gina jiki wanda aka kaddamar, a kananan hukumomi 774 da ake da su a kasar.

    Bayan wannan kaddamarwar, babban taro na kasa na samar sa abinci mai gina jiki da kuma samar da wadataccen abinci, ya biyo baya.

    Taron, ya samu halartar kwararru daga fannoni da ban da ban, ministoci, hukumomin gwamnati, hukumomin tsaro, Sarakunan Gargajiya, ‘yan majalisar taraya da majalisun dokkki da sauran abokan hadaka.

    Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima, wanda ya kaddamar da bude taron ya bukaci, da samar da dabarun kara inganta samar da abinci mai gina jiki da kuma wadataccen abinci a kasar.

    Sai dai, batun, ba wai kawai halartar Sarakunan Gargajiya da Mlaman Addainai waje kaddamarwa bane, akwai kuma matukar bukatar, su kara zage damtse wajen fadadar da alumomin su, kan mauhimmancin ciyar da yara kanana abinci, mai gina jiki, duba da cewa, ana samun koma baya, wajen ciyar da yaran, wadanda sune, manyan gobe.

    Wannan Jaridar na yin la’akari da cewa, ko da yake kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da aka sabunta, bai bai wa Sarakunan damar bayar da wata gudunmawa ba, amma suna taimaka wa, wajen wanzar da zaman lafiya da warware rikice-rikice.

    Daga watan Afirilun 2025, bisa wasu rahoton da Bankin Duniya ya fitar, sun nuna cewa, akalla ‘yan Nijeriya kaso 75.5, na ci gaba da zaman cikin talauci.

    Bugu da kar, yawan masu zama a cikin talauci a karkara, sun rubanya yawan mazauna a birne,  inda a karkara, ake da kaso 41.3.

    Bisa bincken kiwon lafiya da aka gudanar daga 2023 zuwa 2024  na NDHS da kuma fashin bakin da aka yi a kwanan baya kan karancin abnci mai gina jiki, daga 2024 zuwa 2025, hakan ya nuna cewa, yara kanana ‘yan shekaru kasa da biyar da ke fama da karancin abinci maras jina jiki,  da ke zaune a karkara, sun kai sama da kaso 50.

    Akwai kuma bukatar Sarakunan Gargajiya, su rinka fadadar musamman mata, kan mahimmancin shayar da Jarirai, Nonon Uwa.

    Sai dai, abin damuwar mu shi ne, hujjoji da dama a baya sun nuna cewa, irin wannan daukin da ake samarwa, a karshe, ana yin watsi da shi ne, ba tare da wadanda ake da burin su amfana ba, sun ci gajiyar daukin ba.

    A kasar nan, ba wai an gaza samar da tsare-tsare bane, amma matsalar itace, rashin wanzar da tsare-tsaren, yadda ya kamata.

    A kwanan baya, an ruwaito shugaba Bola Tinubu ya sanar da cewa, ana samar da ingantacciyar kiwon lafiya, hakan ne zai sanya, a samar da yara manyan gobe, wajen gina kasa.

    A lokacin yana raye, tsohon shugaban kasar Amurka John F. Kennedy, ya bayyana cewa, yara sune babban ginshikin yari, a duk fadin duniya kuma wadanda ake da babban fana, samar masu da gobe, mai kyau.

    [ad_2]

    Source link

  • NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?

    [ad_1]

    Ƙarin Podcasts



    Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa?

    Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl?

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai ya yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan’Adam, musamman mai azumi.

    Domin sauke shirin, latsa nan


    [ad_2]

    Source link

  • Dimokuradiyya Mai Tsarin Al’umma Baki Daya: Wata Aba Ce Mai Yiwuwa A Siyasar Wayewar Kai Ta Bil Adama

    [ad_1]

    Chen Junqing, mai shekara 82 da haihuwa daga birnin Xiangxiang na lardin Hunan na kasar Sin, ya shiga damuwa sosai bisa yadda jikansa yake fama da ciwon ciki, saboda yawan cin abincin da ake sayarwa a kan titi.

    Bisa damuwar da ya shiga game da ingancin abincin da yara ke ciki, a ranar da ake rufe karbar ra’ayoyin al’umma game da daftarin “dokar kula da kananan harkokin sarrafa abinci da cibiyoyin sarrafawa, da kananan shagunan cin abinci da kuma masu sayar da abinci a lardin Hunan” cikin watan Satumbar 2024, cikin gaggawa ya rubuta shawara kan wata doka mai kunshe da kalmomi 120 a bayan kwalin taba sigari tare da mika ta.

    Jigon shawarar shi ne a kara tsananta hukuncin ladabtarwa ga masu samar da abinci da masu aikin gudanarwa wadanda suka kasa cika ka’idojin ingantacciyar tsafta. Wannan shawarar, daga karshe ta samu amincewar zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’a ta lardin Hunan kuma ya sanya ta cikin sashe na 40 na sabbin dokokin da aka yi wa kwaskwarima.

    Wannan ba wani lamari ne da ya kasance kebantacce ba, amma wata fa’ida ce ta dimokuradiyya irin ta kasar Sin. Wannan nau’i na dimokuradiyya na musamman, wanda aka fi sani da “dimokradiyya mai tsarin al’umma gaba daya,” yana bayar da sabuwar kafa ta yiwuwar samun siyasar wayewar kai ta bil’adama. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • Sin Ta Himmatu Wajen Raya Ci Gaban Duniya Na Bai Daya

    [ad_1]

    Yayin da aka karkare manyan tarukan siyasa biyu na kasar Sin, wato taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar Sin NPC, da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar CPPCC na bana, masharhanta da suka shaida abubuwan da aka tattauna yayin tarukan, sun jinjinawa kwazon kasar Sin ta fuskar aiwatar da manufofin samar da ci gaba mai inganci, da yadda kasar ta himmatu wajen tattauna dabarun tsara ayyuka na dogon lokaci, wadanda dukkaninsu ke zama muhimman ginshikai na daidaita yanayin ci gaban duniya baki daya.

    Baya ga muhimmin aikin nazari, da zartar da daftarin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da kasar za ta aiwatar tsakanin shekarar nan ta 2026 zuwa ta 2030, wani muhimmin bangare na tasirin tarukan shi ne tsara manufofi daga bangaren Sin, wadanda za su karfafa daidaiton ci gaban duniya baki daya.

    La’akari da ayyuka daban daban da tuni gwamnatin Sin ke gudanarwa, mun shaida yadda kasar ke shigar da sabon kuzari a fannin bincike da samar da ci gaba, da bullo da dabarun samar da ci gaba mai inganci, wadanda muhimman ginshikai ne cikin shirin na raya kasa karo na 15.

    Ko shakka babu, wannan shiri na raya kasar Sin ya tabbatar da alkiblar kasar ta gaggauta rungumar sabon tafarkin bunkasa masana’antu ta amfani da fasahohi, da kirkire-kirkire da kere-keren zamani.

    A ganina, matsayin da kasar Sin ke kai a halin yanzu, na shige wa gaba wajen jagorantar samar da hajoji masu inganci, da kakkarfan ikon zuba jari a masana’antun dijital, da sauran muhimman fannoni, zai wanzar da kasar a matsayin ginshikin ingiza sabon sauyin da duniya za ta samu a fannin fasahohin zamani cikin shekaru da dama masu zuwa.

    Har ila yau, a babin misali, manufofin samar da ci gaba irin su shawarar ziri daya da hanya daya, wadanda ake kokarin daidaita tafiyarsu da ajandoji irin na raya ci gaba Afirka nan zuwa shekarar 2063, za su tabbatar dabarun ci gaba na sassan duniya mabanbanta, sun ci gaba da karfafa juna.

    A takaice, muna iya cewa wadannan manyan tarukan siyasa biyu na kasar Sin, sun baiwa duniya wata kofa ta kara fahimtar gudummawar Sin ga raya ci gaban duniya na bai daya, da ma kyakkyawar aniyar kasar ta ci gaba da bayar da gudummawa ga ci gaban duniya baki daya.

    [ad_2]

    Source link

  • An kama mutum 5 da kuɗin jabu, bindiga da tumaki 180

    [ad_1]



    Rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato ta kama mutane biyar da ake zargi da hannu a harkar kuɗin jabu, sannan ta ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da tumaki 180 yayin wasu samame daban-daban da aka kai a faɗin jihar.

    Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa’i ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce jami’an sashin yaƙi da garkuwa da mutane sun gano wata ƙungiyar masu kuɗaɗen jabu da aka sani da sunan “Sai Malam”.

    A cewarsa, Jami’in ɗanda (DPO) na shiyyar Illela ya miƙa wasu mutane uku da ake zargi ga sashen binciken manyan laifuka (CID) domin gudanar da bincike, waɗanda suka haɗa da: Muhammad Hamidu daga Kwanni a Jamhuriyar Nijar, Umar Hassan da kuma Sadik Isah daga ƙaramar hukumar Illela.

    Rufa’i ya ƙara da cewa, binciken sirri ne ya kai ga kama wasu ƙarin mutane biyu, Buhari Abubakar da Kasimu Muhammad, dukansu mazauna unguwar Makera Asada a cikin birnin Sakkwato. Ya ce rundunar ta yi nasarar ƙwato kudi na jabu da wasu kayan tsafi da ake amfani da su wajen gudanar da haramtacciyar sana’ar tasu.

    A wani samamen na daban a ranar 10 ga Maris, sashin yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar ya amsa kiran gaggawa game da wasu da ake zargi mambobin haramtacciyar ƙungiyar ‘Yan Sakai ne a ƙauyen Dakalo da ke ƙaramar hukumar Dange Shuni. Kungiyar, ƙarƙashin jagorancin wani Sani Nabuzuwa, ana zarginta da hannu a kisan kai da satar shanu.

    “Ganin ’yan sanda ya sa maharan suka buɗe wuta, amma jami’anmu suka fatattake su inda suka tsere zuwa cikin daji,” in ji shi.

    Kayan da aka ƙwato a wurin sun haɗa da: “Bindiga ƙirar AK-47, kunshi mai ɗauke da harsasai 11, tumaki 180 da ake zargin na sata ne, da kuma babur ƙirar Kasea.”

    A gefe guda kuma, jami’an ofishin ’yan sanda na Arkilla sun kama wani matashi mai suna Auwal Sani daga ƙaramar hukumar Yabo, bisa zargin sojan gona.

    Rundunar ta ce, wanda ake zargin da wani abokin aikinsa da har yanzu yake tsere, sun sanya kayan jami’an ’yan sanda na tafi-da-gidanka (MOPOL), inda suka tsayar da wani ɗan achaɓa sannan suka ƙwace babur ɗinsa ƙirar Boxer da sunan za su kai shi ofishin ’yan sanda.

    Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ahmed Musa ya tabbatar wa mazauna jihar ƙudurinsa na kakkaɓe miyagu, sannan ya buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa rundunar bayanan sirri masu amfani.


    [ad_2]

    Source link

  • Kudaden Shiga Na Masana’Antun Kimiya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Da 16.1% a Watannin Janairu Da Fabrairun Wannan Shekara

    [ad_1]

    Bayanan haraji na hukumar haraji ta kasar Sin sun bayyana cewa, a watannin Janairu da Fabrairu na wannan shekara, ci gaban fasaha da kimiyya na kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi.

    Bayanan sun nuna cewa, a watannin Janairu da Fabrairu, masana’antun kirkire-kirkire na kasar Sin sun samu ci gaba cikin sauri. Kazalika, kudaden shiga na manyan masana’antun kimiya da fasaha na zamani ya karu da kashi 16.1% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kana yana ci gaba da bunkasa cikin sauri. Daga cikinsu, kudaden shiga na manyan ayyukan hidima ya karu da kashi 17.2%, musamman ayyukan dillalan fasaha, da binciken kimiyyar hallitu da gwaje-gwaje, sun karu da kashi 25.6% da 17.4% bi da bi.

    Har ila yau, kudaden shiga na manyan masana’antun kere-kere ya karu da kashi 14.5%, sakamakon bunkasar da ake samu daga tattalin arzikin sararin sama kusa da doron kasa, da kasuwancin sararin samaniya, da kayan laturoni, da masana’antun kera jiragen sama, da na’urorin sadarwa na laturori sun karu da kashi 28.5%, da 18.4% bi da bi. (Amina Xu)

    [ad_2]

    Source link

  • Yawan Dazuzzuka Da Filin Ciyayi a Kasar Sin Ya Wuce Kashi 56%

    [ad_1]

    A yau Alhamis 12 ga watan nan na Maris, kasar Sin ta yi bikin ranar dasa bishiyoyi karo na 48. Ofishin kwamitin kula da dazuzzuka na kasar Sin ya fitar da wani rahoto na halin da dazuzzukan kasar Sin a shekara ta 2025 ke ciki, inda ya nuna cewa a shekarar da ta gabata, an kammala dasa bishiyoyi har hekta miliyan 3.563, an kuma gyara filayen ciyayi da suka lalace har hekta miliyan 4.927. Alkaluma sun nuna yawan dazuzzukan ya kai kashi 25.09%, kana yawan filayen ciyayi ya wuce kashi 56%, yayin da adadin itatuwa ya kai kyubik mita biliyan 20.988.

    A shekarar da ta gabata, an ci gaba da ayyukan dasa bishiyoyi cikin himma da gwazo, tare da aiwatar da ayyuka 166 na muhimman a bangarori 2, wato aikin karewa da gyara tsarin muhallin halittu, da ayyuka 27 na karewa da gyara dazuzzuka, da ciyayi, da koguna, da tafkuna, da hamada cikin hadin gwiwa, kana da ayyukan gwaji 10 na dasa bishiyoyi, da ayyukan gwaji 68 na gyara mahakar ma’adanai da aka yi watsi da su, don kyautata inganci, da tabbacin tsarin muhallin halittu na wasu yankuna masu muhimmanci. (Amina Xu)

    [ad_2]

    Source link

  • Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan ISWAP 20 A Jihar Yobe

    [ad_1]

    Sojojin rundunar haɗin gwiwa a Arewa maso Gabas sun kashe ’yan ta’addan ISWAP sama da 20, bayan sun daƙile hare-haren da suka kai wa sansaninsu a Goniri, Jihar Yobe.

    Sojojin da ke ƙarƙashin Operation Haɗin Kai sun fuskanci hare-hare daga ɓangarori daban-daban a daren 9 ga watan Maris zuwa safiyar 10 ga watan Maris, 2026.

    • Gwamna Uba Sani Bai Nuna Goyon Bayan Wani Ɗan Takarar Majalisa Ba – Gwamnatin Kaduna
    • Kamfanonin Ketare Na Ganin Sabbin Fa’Idodin Ci Gaba Daga Sabbin Bukatun Kasuwar Sin

    A cikin wata sanarwa, jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce an fara gano motsin ’yan ta’addan ta hanyar na’urorin sa ido yayin da suke tahowa daga ƙauyen Goniri da kuma hanyar Ngamdu domin kewaye sansanin sojoji.

    Ya ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa da ƙarfin wuta da dabarun kare kai.

    Haka kuma an tura ƙarin sojoji yayin da rundunar sama ta Operation Haɗin Kai ta ba da tallafin kai hare-hare ta sama.

    A yayin artabun, ’yan ta’addan sun ja da baya bayan sun yi asara mai yawa.

    Fiye da 20 daga cikinsu aka kashe, ciki har da wani babban kwamandansu mai suna Abu Yusu.

    Sojojin sun kuma ƙwato makamai da kayayyaki da ’yan ta’addan suka bari yayin da suke tserewa, ciki har da bindigogin ƙirar AK-47, bama-bamai da alburusai iri-iri.

    A yayin sintiri a wasu wurare da ke kusa da yankin, ciki har da Gwaigomari a yankin Timbuktu Triangle, an sake gano ƙarin gawarwakin ’yan ta’addan.

    Uba ya ce wasu sojoji sun samu raunuka a artabun, amma an kai su asibiti kuma yanzu suna cikin ƙoshin lafiya.

    Ya ƙara da cewa sojoji na ci gaba da riƙe yankin tare da gudanar da bincike a wasu ƙauyukan da ke kusa da yankin, inda ake zargin wasu ’yan ta’addan da suka ji rauni na can.

    [ad_2]

    Source link