Category: Latest News

  • Yara miliyan 6.4 na fama da matsanancin rashin abinci a Arewacin Najeriya — ICRC

    [ad_1]



    Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Duniya, International Committee of the Red Cross (ICRC), ta bayyana damuwa kan ƙaruwar matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a yankunan da ke fama da rikici a Arewacin Najeriya.

    Ƙungiyar ta ce kimanin yara miliyan 6.4 ’yan ƙasa da shekara biyar a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ne ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

    A cewar ƙungiyar, rikicin da aka shafe kusan shekara 15 ana yi ya lalata rayuwar jama’a, noma da samar da abinci, wanda ya sa magidanta da dama suka rasa isasshen abinci.

    A wata cibiyar kula da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki a Damaturu da ke Jihar Yobe, wata uwa mai suna Zainab Isa ta kawo ɗanta ɗan watanni 22, Umar, wanda jikinsa ya kumbura saboda matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

    Bayan an kwantar da shi a asibiti tare da ba shi abinci mai gina jiki da magani, lafiyarsa ta fara inganta cikin mako guda.

    A Biu da ke kudancin Jihar Borno, wata mata mai suna Fatima ta ce tana shan wahala wajen ciyar da ’ya’yanta 13 bayan rikicin ’yan ta’adda ya tilasta musu barin gidansu da gonakinsu.

    ICRC, ta ce tana kula da yara sama da 1,000 masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a kowace shekara.

    Sannan tana kula da lafiyar yara da tallafin noma, samar da ruwan sha mai tsafta da kuma tallafin kuɗi ga magidanta masu rauni.

    Ƙungiyar ta ce a shekarar 2025, sama da mutum 348,000 sun samu magani kan matsanancin rashin abinci mai gina jiki a cibiyoyin lafiya da ta ke tallafawa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

    Sai dai duk da wannan taimako, ƙungiyoyin agaji sun yi gargaɗin cewa matsalar na ci gaba da ƙamari saboda matsalar tsaro da kuma raguwar hanyoyin samun kuɗin shiga a yankin.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamna Uba Sani Bai Nuna Goyon Bayan Wani Ɗan Takarar Majalisa Ba – Gwamnatin Kaduna

    [ad_1]

    Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta bisa zargin cewa gwamnan jihar, Uba Sani, ya goyi bayan wasu ’yan takara domin kujerun majalisar tarayya gabanin zabukan 2027 masu zuwa.

    Gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin mara rushe tare da bukatar al’umma su yi watsi da shi baki daya.

    • Lauyoyin Gwamnatin Kano Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Rufe Ma’aikatar Shari’a
    • Kamfanonin Ketare Na Ganin Sabbin Fa’Idodin Ci Gaba Daga Sabbin Bukatun Kasuwar Sin

    A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya sanya wa hannu , ya ce gwamna Uba Sani bai goyi bayan kowane dan takara ba, kuma bai fifita wani mai neman wata kujera ta zabe ba.

    Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan mai kishin dimokuradiyya ne, wanda ya yi imani da tsarin gaskiya da adalci, inda ’yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki za su zabi ’yan takararsu ta hanyoyin da kundin tsarin jam’iyya ya tanada.

    Sanarwa ta ci gaba da cewa ” Mun sanu wani sako mai rudani da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa gwamna ya goyi bayan wasu ’yan takara. Wannan ikirari karya ne gaba daya, kuma bai da tushe balle makama,”

    Malam Maiyaki , ya kara da cewa a halin yanzu gwamnan ya fi maida hankali ne wajen inganta shugabanci nagari da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su kyautata rayuwar al’ummar jihar Kaduna, maimakon shiga batun goyon bayan ’yan takara tun kafin lokaci.

    Sanarwar ta kuma gargadi mutane ko kungiyoyi da su guji yada labaran karya da bayanan siyasa marasa tushe, domin irin hakan na iya haifar da rudani a fagen siyasa tare da yaudarar jama’a.

    Akan haka kwamishinan ya bukaci ’yan siyasa da magoya baya da sauran jama’a da su rika tabbatar da sahihancin labarai daga sahihan majiyoyi kafin yadawa, yana mai cewa sadarwa mai kyau na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

    Maiyaki ya jaddada cewa gwamna Uba Sani zai ci gaba da mutunta hakkokin dimokuradiyya na dukkan masu neman takara, tare da tabbatar da cewa doka da ka’idoji ne za su jagoranci dukkan harkokin siyasa a jihar.

    [ad_2]

    Source link

  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15, Sun Jikkata Da Dama A Katsina

    [ad_1]

    Aƙalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata a hare-haren daban-daban da ‘yan bindiga suka kai a ƙauyukan Dansoda da Jikamshi da ke ƙananan hukumomin Dandume da Musawa a Jihar Katsina.

    A cewar ‘yansanda da mazauna yankunan, hare-haren sun faru ne a yammacin ranar Talata.

    • Babu Lokacin Da Aka Fi Bukatar Shawarar GGI Ta Shugaba Xi A Duniya Kamar Yanzu
    • Kamfanonin Ketare Na Ganin Sabbin Fa’Idodin Ci Gaba Daga Sabbin Bukatun Kasuwar Sin

    Wani mazaunin Dansoda, Kabir Adamu, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba, ya ce ‘yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, inda suka kashe mutane 11 nan take.

    A wani hari na daban kuma, an ruwaito cewa mutane huɗu sun mutu lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a garin Jikamshi da ke ƙaramar hukumar Musawa.

    Dukka wadanda suka rasa rayukansu, an riga an binne su bisa ga koyarwar addinin Musulunci.

    [ad_2]

    Source link

  • Shugaban jam’iyyar PDP na Zamfara ya koma APC

    [ad_1]



    Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Dokta Jamil Jibo Magayaki, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC.

    Dokta Jamil ya koma jam’iyyar mai mulki ne bayan komawar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, APC.

    A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, tsohon shugaban PDP na jihar, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bisa halin da siyasa ta ke ciki a Jihar Zamfara.

    Sanarwar ta ce: “Ni, Dokta Jamil Jibo Magayaki, shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, ina sanar da ku a hukumance cewa na koma jam’iyyar APC.”

    Ya ƙara da cewa: “Na yanke shawarar komawa APC ne bisa halin da siyasa ta ke ciki a Zamfara.

    “Tana buƙatar mu haɗa kai da jam’iyyar da ta fi ƙarfi don fuskantar ƙalubalen tsaro, ci gaba da kuma shugabanci domin amfanin al’ummar jihar.”


    [ad_2]

    Source link

  • Tsagin PDP Mai Biyayya Ga Wike Ya Sanya 23 ga Mayu, Domin Zaɓen Fidda Gwani Na Shugaban Ƙasa

    [ad_1]

    Wani ɓangare na jam’iyyar PDP mai biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sanya ranar 23 ga Mayu, 2026 domin gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, alamar fara wani muhimmin tsari na cikin gida na zaɓen ɗan takarar jam’iyyar.

    An cimma wannan matsaya ne a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) karo na 106 na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, inda shugabannin jam’iyyar suka amince da cikakken jadawalin gudanar da dukkan zaɓukan fidda gwani bisa ƙa’idojin hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

    Da yake gabatar da sanarwar bayan taron, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na kwamitin riƙo, Jungudo Mohammed, ya bayyana jadawalin da aka amince da shi.

    Ya ce: “Kwamitin NEC ya duba batun gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyya a mukamai daban-daban da kuma jadawalin warware takaddamar da ka iya tasowa daga waɗannan zaɓukan.

    NEC ta kuma buƙaci dukkan sassan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki su fara shirye-shiryen da suka dace tare da bin jadawalin da aka amince da shi da kuma dukkan tanade-tanaden doka.”

    Bisa ga jadawalin:

    • Jam’iyyar za ta miƙa rajistar mambobinta ga INEC ranar 10 ga Afrilu, 2026.
    • Zaɓen fidda gwani na Majalisun Dokokin Jihohi zai gudana 2 ga Mayu.
    • Na Majalisar Tarayya, zai kasance 9 ga Mayu.
    • Zaɓen fidda gwani na gwamnonin jihohi zai gudana 16 ga Mayu.
    • Daga ƙarshe, za a gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ranar 23 ga Mayu.

    [ad_2]

    Source link

  • Gabas Ta Tsakiya: Najeriya ta fara kwaso ’yan ƙasarta daga Iran ta iyakar Armenia

    [ad_1]



    Gwamnatin Tarayya ta fara kwashe wasu ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasar Iran waɗanda suka buƙaci a dawo da su gida, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Jami’an ofishin jakadancin Najeriya sun raka wasu daga cikin ’yan Najeriya zuwa iyakar ƙasar Armenia domin su tsallaka zuwa waje mai tsaro.

    Daraktan yaɗa labarai na Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abdur-Rahman Balogun ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba, yana mai cewa bayanin ya fito ne daga shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa.

    Ya ce: “Wasu ’yan Najeriya da suka nuna buƙatar su fice daga Iran domin tsira sun samu rakiyar jami’an ofishin jakadancin Najeriya har zuwa iyakar Armenia domin su tsallaka cikin aminci.”

    Shugabar hukumar ta kuma bayyana cewa kawo yanzu babu wani ɗan Najeriya a Iran da rikicin ya shafa.

    Ta ce jami’an gwamnati suna kan iyakar Iran da Armenia domin karɓar duk wanda ke son barin ƙasar.

    Hukumomi sun ce suna aiki tare da ofisoshin jakadanci da sauran abokan hulɗa domin tabbatar da cewa an samar da tsaro da takardun tafiya ga duk ’yan Najeriya da ke son a kwaso su.

    Dangane da jiragen da za su dawo da su gida, Dabiri-Erewa ta ce a halin yanzu sararin samaniyar yankin ba shi da tsaro saboda hare-haren da ke aukuwa.

    Ta ƙara da cewa: “Da zarar an buɗe sararin samaniyar yankin, tawagar Gwamnatin Tarayya da ta ƙunshi jami’ai daga ma’aikatu daban-daban za su fara aikin kwaso ’yan Najeriya zuwa gida.”

    Wannan mataki na zuwa ne yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta, lamarin da ya sa ƙasashe da dama suka fara kwashe ’yan ƙasarsu daga yankin.

    An fara wannan rikicin ne kwanaki 12 da suka gabata bayan wani hari da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a kan Iran, wanda ya haddasa sabon tashin hankali a yankin.


    [ad_2]

    Source link

  • Gusau ya zama sabon shugaban sabuwar tashar jirgin saman Zamfara

    [ad_1]



    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya naɗa Kabiru Yahaya a matsayin sabon shugaban sabuwar tashar jirgin saman jihar.

    Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne, ya bayyana hakan.

    Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da sabuwar tashar jirgin saman ta fara aiki cikin ƙanƙanin lokaci.

    A cikin wata sanarwa da Babban Mashawarcin Gwamnan kan Yaɗa Labarai, Suleiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce samar da tashar jirgin saman zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.

    Hakazalika, ya ce tashar za ta jawo masu zuba jari, da kuma ƙarfafa tattalin arziƙin Jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.

    Ya ce: “Kabiru Yahaya ƙwararre ne a fannin harkokin jirgin sama, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki a wannan fanni da kuma gudanar da shi.”

    Sanarwar ta ƙara da cewa Yahaya ya taɓa riƙe muƙamin manaja a Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA), sannan ya taɓa zama mataimaki na musamman ga babban daraktan hukumar a matakin ƙasa.

    Tudu ya ƙara da cewa: “Ya yi karatun difloma da kuma digiri na biyu a fannin Tsara Zirga-zirgar Jiragen Sama a Jami’ar Legas (LASU).

    “Sannan ya samu takardar shaidar kammala horo kan sadarwar jiragen sama a Kwalejin Horas da Fasahar Jirgin Sama da ke Zariya (NCAT).”


    [ad_2]

    Source link

  • Tinubu ya naɗa Yuguda a matsayin mataimakin Gwamnan CBN

    [ad_1]



    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Lamido Abubakar Yuguda, a matsayin Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

    Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

    Ya ce naɗin zai fara aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta amince da shi.

    Onanuga, ya ce an yi naɗin ne bisa tanadin Sashe na 8(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya ta shekarar 2007.

    An naɗa Yuguda ne, bayan tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Bala Bello, ya samu sabon muƙami a matsayin Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tattalin arziƙi da siyasa.

    Shugaba Tinubu, ya buƙaci su gudanar da ayyukansu da jajircewa, ƙwarewa da kuma sadaukarwa domin bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.

    Kafin wannan naɗi, Yuguda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Darakta Janar na Hukumar Kula da Kasuwannin Hannayen Jari (SEC) daga shekarar 2020 zuwa 2024.

    Yuguda ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello, inda ya kammala digiri a fannin Accountancy a shekarar 1983.

    Daga bisani a shekarar 1991 ya samu digiri na biyu a fannin Kuɗi, Banki da Harkokin Kuɗi a Jami’ar Birmingham da ke Birtaniya.

    Shi mamba ne na Cibiyar Ƙwararrun Masu Lissafi ta Najeriya (ICAN) kuma yana da takardar shaidar Chartered Financial Analyst (CFA).

    Ya fara aikinsa a shekarar 1984 a Babban Bankin Najeriya (CBN) a matsayin babban mai kula da ayyuka a sashen harkokin kuɗaɗen waje.

    Tsakanin shekarar 1997 zuwa 2001, ya yi aiki a matsayin masanin tattalin arziƙi a sashen Afirka na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) kafin ya koma aiki a CBN.

    Daga bisani ya yi ritaya daga CBN a shekarar 2016 bayan ya yi shekaru shida yana riƙe da muƙamin Daraktan Sashen Kula da Ajiyar Kuɗi.


    [ad_2]

    Source link

  • SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 23

    [ad_1]

    Fa’idar Sahur

    1. Yin sahur koyi ne da annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam), kuma malamai sun yi ijma’i a kan mustahabbi ne yinsa kamar yadda Ibnul Munzir da Imamu Annawawi suka naƙalto.

    2. Yin sahur saɓa wa Yahudu da Nasara ne, domin su ba sa yin sahur a azuminsu kamar yadda Muslim da Abu Dawud Tirmizi da Nasa’i suka ruwaito.

    • Darussa Daga Ramadan Na 9: Danne Fushi Da Nutsuwa A Ramalana
    • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 10

    3. Sahur albarka ne ga mai yinsa kamar yadda hadisi ya gabata.

    4. Sahur yana samar da karfi ga mai azumi wajen yin ibada, da kuma ƙaruwar nishadi, da kuma tunkuɗe mummunar dabi’a da yunwa take haifarwa. Kuma a lokacin yinsa sahur, mutum yana samun dama ya yi sadaƙa ga almajiri ko kuma su ci tare. kuma yana sa mutum ya yi zikiri da addu’a, domin lokacin ne da ake karbar addu’a… “kamar yadda Hafiz Ibnu Hajar ya bayyana a littafinsa Fathul Bari (4/496) da malaminsa Ibnu Mulaƙƙin a cikim  al’I’ilamu (5/187)

    5. Samun salati daga Allah da mala’ikunsa.

    Allah ya datar da mu ga koyi da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam) a cikin al’amuranmu baki daya.

    [ad_2]

    Source link

  • Champions League: Real Madrid ta lallasa Man City a Santiago

    [ad_1]



    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta doke Manchester City da ci uku da nema a filin wasa na Santiago Bernabeau da ke birnin Madrid.

    Ƙungiyoyin biyu sun fatata a wasan zagayen ’yan 16 na Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) a daren ranar Laraba.

    Sai dai wasan bai yi wa baƙi daɗi ba, domin Madrid ta yi musu wankan jego mai zafin gaske.

    Ɗan wasan tsakiyar Real Madrid, Fede Verlvade ne ya jefa wa Manchester City ƙwallo uku rigis a ragarta.

    Ɗan wasan ya fara jefa ƙwallo a minti na 20 da minti na 27, sannan ya ƙarƙare a wata ƙwallon a minti na 42.

    Hakazalika ɗan wasa Vinicius Jrn ya samu bugun fenariti a minti na 57, amma mai tsaron ragar Manchester City, Donnaruma ya tare ƙwallon.

    Yanzu dai ƙungiyoyin za su sake fafatawa da juna a ranar Talata mai zuwa a filin Etihad da ke Ingila, domin ware wanda zai je mataki na gaba na gasar.


    [ad_2]

    Source link