Category: Latest News

  • Babu Lokacin Da Aka Fi Bukatar Shawarar GGI Ta Shugaba Xi A Duniya Kamar Yanzu

    [ad_1]

    Tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a duniya sun kara tsananta kwarai da gaske tun bayan kaddamar da hare-haren kawancen Amurka da Isra’ila a kan kasar Iran da kuma zafafan martanin da Iran take mayarwa. Tun bayan dawowar shugaba Donald Trump na Amurka karagar mulki a farkon shekarar 2025, duniya take fuskantar wasu ire-iren sauye-sauye da masana ke cewa ba a taba ganin irinsu ba tun bayan yakin duniya na biyu.

    Tsarin mabambantan bangarori da kasashen duniya suka shimfida kuma suka yi mubaya’a a kai a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a duniya na fuskantar barazanar wargajewa, sakamakon lullubin birin da aka yi wa babakeren Amurka da sunan shirin “sake mayar da Amurka gawurtacciya, watau MAGA.”

    Tun kafin shiga wannan hali a duniya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya mai lakabin GGI yayin gudanar da taron kungiyar hadin gwiwar kasashe ta Shanghai (SCO) a shekarar 2025, da nufin kyautata yadda ake tafiyar da al’amuran harkokin kasa da kasa, ta yadda za su dace da zamani da kuma nuna gaskiya da adalci. Wannan ba karamin hangen nesa ba ne, domin a halin yanzu, duk kalubalen da ake fargabar aukuwarsu suna kara bayyana daya-bayan-daya kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a kwanan nan.

    Babban abin da aka fi tsoro shi ne rugujewar tsarin kasa da kasa a karkashin inuwar MDD, domin hakan zai mayar da duniya zamanin bakin duhun zalunci da mulkin mallaka ta yadda kasashe masu karfi za su ci karensu ba babbaka a kan kananan kasashe, sannan daga bisani su juya kan junansu. Shugaba Xi ya taba bayyana cewa, bai kamata a mayar da muhallin rayuwar bil’adama ya zamo irin na namun daji ba wanda mai karfi zai buge mara karfi ya cinye, kuma an kama hanyar hakan tun daga lokacin da Amurka ta tura sojojinta suka shiga har cikin gidan kasar Venezuela suka sace shugaban kasar sukutum tare da ingiza keyarsa zuwa kurkukunta.

    Dabi’un Amurka suna kara rura wutar rashin tabbas a fagen kasa da kasa, inda yanzu haka manyan kawayenta ciki har da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) suka fara debe tsammani da ita da kuma tunanin rage dogaro da tsarin mabambantan bangarori wajen fuskantar barazanar tsaro kamar yadda shugabar hukumar EU, Ursula von der Leyen ta bayyana kwanan nan. Shi ma shugaba Faransa ya fito fili ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da kera makaman nukiliya, kuma ba za ta fada wa duniya adadinsu ba.

    Don haka, bisa la’akari da yadda abubuwa ke kara ta’azzara, babu lokacin da aka fi bukatar gaggauta amfani da shawarar GGI ta shugaba Xi kamar wannan lokaci domin sake daidaita tsarin kasa da kasa da zai yi wa kowane bangare adalci, lamarin da ke bukatar goyon baya da gudunmawar al’ummomin kasa da kasa. Kumma tabbas za a iya cimma hakan, kamar yadda gaggan kawayen Amurka suka kware mata baya ta hanyar kin shiga da ba da sansanoninsu don kai hare-hare na fitinar da ta tayar ita da Isra’ila a kan Iran. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • Wakilin Kasar Sin: Rikici A Yankin Gulf Ba Zai Amfanawa Kowa Da Komai Ba

    [ad_1]

    Manzon musamman na kasar Sin a yankin Gabas ta Tsakiya Zhai Jun, ya jaddada muhimmancin dakatar da bude wuta da rikici a yankin Gulf, yayin da ake fargabar rikicin dake gudana tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila ka iya kara dagula al’amura.

    Yayin ganawarsa da Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, mataimakin firaminista kuma ministan harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawa a jiya, Zhai Jun wanda ke rangadi a yankin Gabas ta Tsakiya, ya ce kasar Sin ta damu matuka da yanayin da yankin ke ciki.

    Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fitar ta ruwaito Zhai Jun na cewa, rikici da tashe-tashen hankula ba za su amfani muradun kowa ba. Yana mai cewa dakatar da bude wuta ita ce mafita ga yanayin da ake ciki. (FMM)

    [ad_2]

    Source link

  • Kotun Ƙoli Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masarautar Kano

    [ad_1]

    Kotun Ƙoli na shirin yanke hukunci kan rikicin shari’ar da ya dabaibaye Masarautar Kano.

    Ana sa ran kotun za ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen da suka taso daga sauye-sauyen da aka yi wa tsarin masarautar, wanda ya haifar da mayar da wasu sarakuna kan muƙamansu da kuma sake amincewa da su a matsayin sarakuna.

    • Majalisar CPPCC Ta Kasar Sin Ta Kammala Taronta Na Shekara
    • Ɗan Nijeriya Ya Jikkata Yayin da Iran Ta Harba Sabbin Makamai Masu Linzami Zuwa UAE

    Majiyoyi da ke da masaniya kan yadda shari’ar ke gudana sun shaida wa jaridar Kano Times cewa, hukuncin da kotun za ta yanke zai tantance ko sauye-sauyen da aka yi wa masarautar sun halatta a doka, tare da fayyace ikon da Gwamnatin Jihar Kano ke da shi kan harkokin sarautun na gargajiya.

    Wata majiya da ke kusa da shari’ar ta shaida wa jaridar cewa, ana sa ran kotun za ta yanke hukuncin a wannan watan, duk da cewa ba a bayyana takamaiman ranar ba.

    Majiyar ta ce: “Abin da zan iya faɗa shi ne, Kotun Koli za ta yanke hukunci a wannan watan na Maris. Ba zan iya faɗin ainihin ranar ba, amma tabbas za a yanke hukuncin a watan Maris.”

    [ad_2]

    Source link

  • Kamfanonin Ketare Na Ganin Sabbin Fa’Idodin Ci Gaba Daga Sabbin Bukatun Kasuwar Sin

    [ad_1]

    Ana iya ganin amincewar kamfanonin ketare ga kasuwar Sin lokacin da Sin take gudanar da taron shekara-shekara na majalisar NPC da CPPCC.

    Shugaban kamfanin Sanofi na babban yankin Sin Shi Wang ya ce, “Na yi magana da shugabannin hedkwatar kamfanoinmu sau da yawa kan abin da muke godewa, wato na farko, karfin juriya na tattalin arzikin Sin, yawan jama’ar Sin da bukatun cikin gidanta. Abu na biyu shi ne, yiwuwar hasashe kan tattalin arziki da manufofin Sin, matakin dake samarwa manyan kamfanonin kasa da kasa tabbaci yayin da suke yanke shawara ta matsakaici da dogon lokaci.

    Wadannan abubuwa biyu su ne manyan dalilan da suka sa kamfanoninmu ke kara zuba jari a Sin.” Shi Wang ya kara da cewa, kamfanin ya fara kafa kamfanin samar da kayayyakin hada maganin Insulin a birnin Beijing, a farkon wannan shekara da kudi har Euro biliyan 1. Ana sa ran samar da maganin a kasuwar Sin kafin shekara ta 2030. (Amina Xu)

    [ad_2]

    Source link

  • Lauyoyin Gwamnatin Kano Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Rufe Ma’aikatar Shari’a

    [ad_1]

    Lauyoyin da ke aiki a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani, inda suka ce, sakacin gwamnati na kin mayar da hankali ga jin daɗin su da wasu matsaloli kuma da aka gaza warware ne ya jefa su yajin aikin.

    Jami’an shari’ar, ƙarƙashin ƙungiyar ‘Law Officers Association of Nigeria’ (LOAN) reshen Jihar Kano, sun kulle ƙofar shiga ma’aikatar da safiyar Laraba, inda suka hana ma’aikata da baƙi shiga cikin harabar ma’aikatar.

    • Majalisar CPPCC Ta Kasar Sin Ta Kammala Taronta Na Shekara
    • Ɗan Nijeriya Ya Jikkata Yayin da Iran Ta Harba Sabbin Makamai Masu Linzami Zuwa UAE

    Shugaban ƙungiyar, Barrista Abdullahi Aminu Shamsu, tun da farko ya sanar da shawarar fara wannan yajin aiki, yana mai cewa gwamnati ta kasa magance matsalolin da suka dade suna addabar jami’an shari’a a ma’aikatar.

    Shamsu ya ce lauyoyin na fuskantar wahalhalun yanayin aiki, kuma har yanzu akwai wasu alawus-alawus na doka da sauran hakkokinsu da doka ta tanada, ba a basu ba.

    Ya ƙara da cewa, duk da tattaunawa da dama da suka yi da Gwamnatin Jihar Kano kan lamarin, har yanzu ba a magance damuwar jami’an shari’ar ba, wanda hakan ya sa suka yanke shawarar fara yajin aikin da babu ranar dakatarwa.

    A cewar sanarwar da ƙungiyar ta fitar domin bayyana yajin aikin, wanda ya fara a ranar 11 ga Maris, 2026, an ɗauki matakin ne domin neman inganta jin daɗin ma’aikata, mutunta aikin lauya, kyakkyawan yanayin aiki, da kuma girmama ofishin Shari’a na jihar.

    [ad_2]

    Source link

  • Capital FM Na Kenya: Taruka 2 Na Sin Suna Da Muhimmanci Ga Afirka Har Ma Da Kasashe Masu Tasowa Baki Daya

    [ad_1]

    Gidan rediyon Capital FM na Kenya, ya wallafa wani rahoto a kwanan nan, wanda ke cewa taron majalisar wakilan jama’ar Sin wato NPC da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na Sin wato CPPCC, suna da tasiri mai yawa ga Kenya da ma dukkan fadin nahiyar Afirka, har ma da kasashe masu tasowa na duk duniya baki daya.

    A cikin rahoton, marubucinsa Stephen Ndegwa, ya ce wadannan taruka 2 na bana suna da muhimmanci na musamman, domin an gabatar da shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15 a yayin taron. Wannan shirin karo na 15 zai yi tasiri ga harkar gudanar kudaden, da bunkasar hadin gwiwar fasaha da kuma dangantakar abota ta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.

    Stephen Ndegwa ya jaddada cewa, wannan yana da muhimmanci sosai ga Afirka. Sin ta dade tana kasancewa muhimmin karfi mai ingiza ci gaban duniya, kuma gudunmawarta ga ci gaban tattalin arzikin duniya ya kai fiye da kashi 30%. Idan Sin ta samu ci gaba, tsarin samar da kayayyaki zai fadada, kuma kasuwannin kayayyaki za su samu tabbaci, kana kasashe masu tasowa za su amfana saboda huldar kut da kut a bangaren hadin gwiwar kasuwanci da zuba jari tsakaninsu da Sin. Rahoton ya kuma yi amfani da bayanan cibiyoyin kasa da kasa dake cewa, duk lokacin da tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 1%, tattalin arzikin kasashen da ke da alaka da Sin zai karu da kashi 0.3%.

    Stephen Ndegwa ya ce, tsarin da Sin take bi na karkata zuwa masana’antun kere-kere bisa kirkire-kirkire, da makamashi da ake iya sabuntawa, da kayan aiki na dijital ya haifar da muhimman damammaki ga tattalin arzikin Afirka. (Amina Xu)

    [ad_2]

    Source link

  • Sin Ta Yi Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya

    [ad_1]

    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce Sin na kira da a gaggauta dakatar da bude wuta a yankin gabas ta tsakiya, tare da aiwatar da matakan shawo kan tashin hankalin da ya barke ta hanyar siyasa, kana a goyi bayan kasashen yankin Gulf wajen kare makomar yankinsu da kansu.

    Wang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya yi kiran ne a jiya Talata, yayin zantawarsa ta wayar tarho da firaministan kasar Qatar, kana ministan wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani.

    A cewarsa, matakin kaddamar da hare-hare da Amurka da Isra’ila suka dauka kan Iran, ba tare da amincewar kwamitin tsaro na MDD ba, ya sabawa sharudda da ka’idojin kafuwar MDD, da ma sauran matakan wanzar da alakar kasa da kasa.

    A wani ci gaban kuma, kasar Sin ta nuna rashin amincewa da fadada kai hare-hare, tare da yin Allah wadai da hare-hare kan fararen hula, da wuraren da ba su shafi aikin soji ba. A cewar Wang, ya zama wajibi a martaba ikon mulkin kai, da tsaro da hurumin yankunan kasashen Larabawa dake yankin Gulf.

    Har ila yau, a jiyan Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da mataimakin firaminista, kuma ministan wajen kasar Pakistan Mohammad Ishaq Dar, inda ya bayyana cewa, ginshikin kaucewa kara tsanantar halin da ake ciki dangane da Iran, shi ne Amurka da Isra’ila su dakatar da kaddamar da hare-haren soji kan kasar, kuma Sin ba ta amince da kaiwa kasashen yankin Gulf hare-hare ba, kana ta yi tir da dukkanin hare-haren da ake kaiwa kan abubuwan bukata na fararen hula, da al’ummun da ba su ji ba ba su gani ba. (Saminu Alhassan)

    [ad_2]

    Source link

  • Majalisa ta amince da ɗaurin shekara 2 ga duk wanda aka samu cikin jam’iyya sama da ɗaya

    [ad_1]



    Majalisar Wakilai ta yi gyara sashe na 77 na sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026, inda ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari ko biyan tarar Naira miliyan 10 ga duk wanda aka samu cikin jam’iyyun siyasa biyu a lokaci guda.

    Aminiya ta ruwaito cewa ’yan majalisar sun yi wannan gyara ne bayan muhawara mai zafi, inda suka ƙara yin gyara a sashe na 8, 9 da kuma 10 a cikin dokar.

    Sabon sashe na 8 ya bayyana cewa duk wanda aka samu a cikin jam’iyyu biyu a lokaci guda ba za a yi masa rajistar zama ɗan jam’iyya ba.

    Sashe na 9 kuma ya ce idan aka gano mutum yana cikin jam’iyyu biyu a lokaci guda, za a soke rajistar duka jam’iyyu biyun nan take.

    Sai kuma sashe na 10 wanda ya tanadi cewa duk wanda da gangan ya yi hakan, ya aikata laifi da zai iya jawo masa ɗaurin shekara biyu a gidan yari.

    Hakazalika, sashen ya bayar da zaɓin biyan tarar Naira miliyan 10, ko kuma a haɗa masa hukuncin duka biyun.


    [ad_2]

    Source link

  • Ɗan Nijeriya Ya Jikkata Yayin da Iran Ta Harba Sabbin Makamai Masu Linzami Zuwa UAE

    [ad_1]

    An bayyana cewa, aƙalla ɗan Nijeriya ɗaya yana cikin mutane da dama da suka jikkata bayan tare wasu makamai masu linzami na Iran a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a yayin da rikici ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Mahukunta a ƙasar da ke yankin Gulf sun ce tsarin kariyar sararin samaniyarsu yana ci gaba da mayar da martani ga hare-haren makamai masu linzami na ramuwar gayya da Iran ke harbawa tun bayan da rikicin ya fara a ranar 28 ga Fabrairu.

    • Rikicin Gabas Ta Tsakiya: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Kwaso ‘Yan Nijeriya Daga Iran
    • NDLEA Ta Kama Mutane 56 A Wuraren Hada-hadar Miyagun Ƙwayoyi A Kano

    A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron UAE ta fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa rundunonin kariyar sararin samaniyarta sun kirga jimillar makamai masu linzami na ballistic guda 262 da aka harbo daga Iran tun farkon wannan rikici.

    A cewar ma’aikatar, 241 daga cikin makaman an samu nasarar tare su, yayin da 19 suka fadi cikin teku.

    Sai dai kuma makamai biyu sun faɗa a cikin yankin ƙasar UAE, lamarin da ya haddasa mace-mace da kuma jikkata.

    “Wadannan hare-hare sun yi sanadin mutuwar mutane shida da suka hada da ‘yan ƙasar UAE, Pakistan, Nepal da Bangladesh, sannan kuma mutane 122 sun samu ƙananan raunuka da matsakaita,” in ji ma’aikatar.

    Ta ƙara da cewa mutanen da suka jikkata sun fito ne daga ƙasashe daban-daban da suka haɗa da UAE, Masar, Sudan, Habasha, Philippines, Pakistan, Iran, Indiya, Bangladesh, Sri Lanka, Azerbaijan, Yemen, Uganda, Eritrea, Lebanon, Afghanistan, Bahrain, Comoros, Turkiyya, Iraki, Nepal, Nijeriya, Oman, Jordan da Falasdinu.

    [ad_2]

    Source link

  • Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah

    [ad_1]



    Ga shi dai kwanakin Ramadan suna ta gudu, har mun kawo ga goman ƙarshe wanda shi ne dama ta ƙarshe ga wanda ya yi sakaci a farkon watan, ko kuma ya zama cikon alheri ga wanda ya kyautata ya bayar da abin da ake so a baya.

    Ya ku masoya! Goman ƙarshe na watan Ramadan kasuwa ce babba da masu tsere suke tserereniya a cikinta.

    Lokaci ne da wanda ya yi sakaci yake ƙara ƙwazo a cikinsa, ake jarraba masu himma a cikinsa, ake tantance ma’abota Lahira da ma’abota duniya.

    Da yawa masu huɗuba sun yi magana, masu wa’azi sun yi wa’azi, masu nasiha sun yawaita nasiha kan falalolin wadannan kwanaki da darare, zukatan da suka jiku da imani sun amshi wannan kira, wata jama’a ta amshi kiran ta bi hanyar muminai, ta koma cikin masu ruku’u da sujada, hawayensu na kwarara a tsakiyar dare mai duhu, kuma Ubangijinka Yana ji kuma Yana amsa musu, Ubangijinka bai zama Mai zaluntar bayi ba.

    Wata jama’ar kuma ta ji kiran amma kamar ba ta damu ba. Suna jin muminai suna salloli da tsayuwar dare don ibada ga Ubangijinsu, amma su kamar ba su da bukata, kai kamar an yi musu lamunin Aljanna, shin masu wannan watsewa ba za su yi tunani ba?

    Shin masu wannan sakaci ba za su sake tunani ba?

    Ya ku Musulmi! Ranakun watanku suna raguwa, dararensa masu daraja suna karewa, suna masu shaida a kan abin da kuka aikata, suna kiyaye abin da kuka yi, su masu taskace kyawawan ayyukanku, masu tsarewa da adana su har zuwa lokacin da za a kira ku a Ranar Kiyama: “A Ranar da kowane rai ke samun (sakamakon) abin da ya yi.”

    Ubangijinku Yana kira: “Ya ku bayiNa! Abin sani ayyukanku ne Nake kidaya muku kuma zan saka muku a kai.

    Duk wanda ya samu alheri sai ya gode wa Allah, wanda ya samu wanin wannan kuma, kada ya zargi kowa sai kansa!”

    Wannan watanku ne kuma wannan ne dama ta karshe, mutum nawa ne ya fara azumin bai kawo yanzu ba, ko ba zai kammala shi ba?

    Kuma mutum nawa ya yi kwadayin dawowarsa a bana amma bai riske shi ba? Shin ba za ku yi nazari a kan ajali da makomarku ba?

    Shin ba za ku dubi yaudarar da dogon buri yake yi muku ba?

    Ya ku Musulmi! Idan akwai mai gargadi ga rayuka ko mai wa’azi ga zukata, to, bai wuce dan abin da ya saura na kwanakin Ramadan ba.

    Saura kwana nawa ne? Muna shirin shiga goma na karshe, kwanakin da Annabinku (S.A.W) yake matukar zage damtse domin bauta wa Allah.

    A ashirin na farko yana hada sauran ibadoji da Sallah da barci, amma da goman karshe ya shigo, sai ya tattara shimfidarsa ya daure mazagin wadonsa, ya kaurace wa shimfidar barcinsa, ya tashi iyalansa ya kwankwasa kofar Fatima da Aliyu (Allah Ya yarda da su) yana mai cewa: “Ashe ba za ku tashi ku yi Sallah ba?”

    Sannan ya fuskanci dakunan matansa yana umarni tare da bayyana cewa: “Ku farka Ma’abota Babban Gida (Ahlul Bait), da yawa masu sutura a duniya tsirara suke a Lahira.”

    Annabi (S.A.W) ya kasance idan goman karshe na Ramadan ya zo, ba ya barin duk wanda zai iya tsayuwar dare daga cikin iyalinsa a kwance face ya tashe shi.

    Kuma magabatan kwarai sun fi sauran mutane bibiya da koyi da Annabi (S.A.W).

    Ya zo a cikin Muwadda na Imam Malik (Allah Ya yi masa rahama) cewa Umar dan Khaddabi (RA) ya kasance yana Sallah gwargwadon yadda Allah Ya so, har sai dare ya raba, sai ya tashi iyalansa yana ce musu “Sallah! Sallah!”

    Sannan sai ya karanto wannan aya: “Ka umarci iyalinka da yin Sallah da hakuri a kanta. Ba Mu tambayarka dukiya, Mu ne masu azurta ka, kuma kyakkyawan karshe na masu taƙawa ne.”

    Sufyanu Suri (Rahimahullah) ya ce, “An so idan goma karshe ya shigo (Musulmi) ya yi kokari da daddare ya yi kokari a cikinsa, ya tashi iyalinsa da ’ya’yansa su yi Sallah matukar za su iya hakan.”

    Wata mata daga cikin magabatan kwarai ta fada wa mijinta cewa: “Hakika dare ya tafi alhali akwai doguwar tafiya a gabanmu, sannan guzirinmu kadan ne, kuma ayarin salihai ya yi mana nisa, mu ne muka saura a hanya!”

    Ya ku Musulmi! Ku san darajar zamaninku, ku girmama mafi falalar lokacinku, ku gabatar da aikin alheri domin kanku.

    Kada ku bata lokacinku a cikin abin da ba neman kusanci ba ne ga Allah. Ba da buri ake kyautata zaton alheri ba, ana kyautata zato ne da kyautata aiki.

    Sanya ran samun rahama tare da aikata sabo wani nau’i ne na wauta da tabewa. Ba da kuka da share hawaye ake tsoron Allah ba, ana tsoron Allah ne ta barin abin da ake tsoron ukuba a kansa.

    Ya ku masoya! Ku gabatar da aikin alheri ga kanku, ku tsayu kuma ku yi kankan da kai.

    Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Ya Manzon Allah! Shin idan na riski daren Lailatu Kadari me zan ce a cikinsa?

    Sai ya ce: “Ki ce: “Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa, fa’afu anni.”

    Ma’ana “Ya Ubangiji! Kai Mai yawan afuwa ne, Kana son afuwa, Ka yi min afuwa.” Ku yawaita wannan addu’a a cikin goman karshe.

    Ubangijinku Ya ce, “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, lallai ne Ni ina kusa, Ina amsa kiran wanda ya yi kira idan ya kira Ni.

    “Don haka su amsa Min, kuma su yi imani da Ni, tsamaninsu suna shiryuwa.”

    Ko kun san su wane ne wadannan bayi? Halittu dukkansu bayin Allah ne, sai dai kuma wadannan bayi kebantattu ne.

    Su ne bayi daga ma’abuta addu’a, bayin da suke jirar a amsa musu, su ne masu addu’a cikin kankan da kai, masu addu’a tare da babbar fata, masu kankan da kai wajen kwadayin amsawa; “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, lallai Ni ina kusa…”

    Lallai addu’a tana da wani sha’ani mai ban-mamaki da tasiri babba wajen kyawun karshe da gyara hali da dukiya da dacewa a cikin ayyuka da albarka a cikin arziki.

    Shin ba ku ganin wanda ya dace da rabo ta wajen addu’a, yana samun rabonsa daga kankan da kai da fakewa ne a wurin Allah a kowane hali ba?

    Shi ne yake komawa ga Allah a dukkan bukatunsa ya yi addu’a, a yi masa addu’a, ya rabauta da addu’arsa ta kashin kansa da ta waninsa.

    Mahaifansa suna son sa, ’ya’yansa suna yi masa da’a, mutanen da suke kusa da shi dukkansu suna kewaye shi da addu’a.

    Mahaliccinsa Yana son sa, don haka Ya fawwala karba masa. Sai halayensa su kyautata, aikinsa ya yi kyau, hannuwa su dagu sama, harsuna su daukaka wajen yi masa addu’a.

    Allah Yana lura da shi Ya datar da shi, sha’aninsa yana kyautatuwa tare da dacewa.

    Yaya za a kwatanta shi da wanda aka haramta masa haka, wulakatacce wanda bai dandani zakin ganawa da Ubangijinsa a Ramadan ba?

    Yaya za a hada shi da wanda ya ji kunyar bauta wa Ubangijinsa, ya yi girman kai daga rokon Ubangijinsa? Abin haramtawa da ya rufe kofar rahama ga kansa, ya lulluba da tufar gafala?

    Hudubar Juma’a daga Muhammad bin Mabrouk Lu’awani, Masallacin Khalid bin Walid da ke Saudiyya


    [ad_2]

    Source link