Category: Latest News

  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 11 a Katsina

    [ad_1]



    ’Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 11 tare da jikkata wasu da dama a wani hari da suka kai garin Dansoda da ke Ƙaramar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina.

    Rahotanni sun ce harin ya faru ne ranar Litinin daddare, a daidai lokacin da al’umma da dama ke hutawa bayan buɗa baki a cikin wannan wata na Ramadan.

    Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da takaici, inda mazauna garin ke bayyana harin a matsayin babban zalunci ga mutane masu zaman lafiya.

    Wani mazaunin yankin da ya tsallake rijiya da baya wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ’yan bindigar sun shiga garin ne da daddare suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

    Ya ƙara da cewa, Ƙaramar Hukumar Kankara na daga cikin yankunan da a baya aka yi yarjejeniyar sulhu da ’yan bindigar, amma a cewarsa hakan bai hana su ci gaba da kawo hare-haren ba.

    Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga jami’an tsaro dangane da harin, duk da ƙoƙarin jin ta bakinsu da aka yi.


    [ad_2]

    Source link

  • Kotu A Norway Ta Ɗaure Ɗan Wasan Nijeriya Kan Zargin Aikata Fyaɗe

    [ad_1]

    Wata kotu a ƙasar Norway ta yanke wa ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya, Daniel Daga, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bayan ta same shi da laifin yin lalata da wata mata ba tare da izininta ba.

    An bayyana hukuncin ne a ranar Talata, inda kotun ta kuma umarci ɗan wasan mai shekaru 19 da ya biya tarar Kroner 10,000 na kuɗin Norway.

    • Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato
    • Gwamnati Ta San Sunaye Da Wuraren Da ‘Yan Ta’adda Suke — Sheikh Gumi

    Gidan talabijin na Norway, TV 2, ne ya ruwaito hakan.

    Rahoton ya ce hukuncin da kotun ta yanke ya yi daidai da abin da mai gabatar da ƙara ta nema.

    Sai dai lauyan Daniel Daga, Astrid Bolstad, ya ce ɗan wasan ya yi matuƙar takaici da hukuncin, kuma ya dage cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

    Bolstad ya ce Daga yana cikin damuwa matuƙa saboda hukuncin, kuma yana ganin abin da ya faru tsakaninsa da matar ya kasance da yardarta.

    Lauyan ya ƙara da cewa ɗan wasan na shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun.

    A wata sanarwa da ƙungiyar kwallon kafa ta Molde ta fitar daga baya a ranar Talata, ta ce ba za ta saka Daga cikin ‘yan wasan da za su buga wasan ƙungiyar a wannan makon ba, saboda hukuncin da kotu ta yanke masa.

    Daniel Daga ya koma ƙungiyar Molde kafin fara kakar wasa ta 2025, kuma ya buga wasanni 15 inda ya zura ƙwallaye uku.

    Kafin komawarsa Turai, Daga ya taɓa buga wa ƙungiyar Enyimba wasa a gasar Firimiyar Nijeriya.

    A matakin ƙasa da ƙasa kuwa, ya taɓa wakiltar tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta ‘yan ƙasa da shekaru 20, inda ƙoƙarinsa ya ja hankalin manyan ƙungiyoyin Turai kafin daga bisani ya koma Molde FK.

    [ad_2]

    Source link

  • Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato

    [ad_1]

    Dakarun Rundunar Sojin Ƙasan Nijeriya sun kashe wasu da ake zargin ’yan ta’adda uku tare da ƙwato makamai a wani samame da suka kai a cikin dajin Kadam da ke ƙaramar hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

    Sojojin Bataliya ta 7 ta rundunar sojin ƙasa ce suka gudanar da aikin tare da tawagar farmaki ta 8, ƙarƙashin Operation Fansan Yamma.

    • Saudiyya Ta Rage Samar Da Man Fetur Saboda Matsalar Jigila A Hormuz
    • Gwamna Abba Ya Sauke Shugaban Ma’aikatan Kano Daga Muƙaminsa

    A wata sanarwa da Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na runduna ta 8, Olaniyi Osoba ya fitar, ya ce sojojin sun fafata da wata ƙungiyar ’yan ta’adda da ke da alaƙa da Lakurawa.

    Ya ce samamen ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da suka nuna cewa ’yan ta’adda sama da 100 sun taru a cikin dajin Kadam domin kai hare-hare da sace-sace a ƙauyukan da ke kusa da yankin.

    “A bisa wannan bayanin sirri, sojoji suka yi gaggawar zuwa wajen domin tare su. An yi arangama da su da misalin ƙarfe 12 na rana,” in ji shi.

    Ya ƙara da cewa an yi musayar wuta mai tsanani, inda ’yan ta’addan suka yi ƙoƙarin kai hari daga baya, amma sojojin suka daƙile su.

    Bayan arangamar, sojojin sun ci gaba da bincike a cikin dajin inda suka tabbatar da kashe ’yan ta’adda uku, yayin da ake zargin wasu sun tsere da raunukan harbin bindiga.

    Haka kuma sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar PKT guda ɗaya, bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 350 na PKT, harsasai 111 masu ɗangon 7.62mm, mujallu uku na bindiga, rediyoyin sadarwa guda biyu, babura uku da kuma wayar hannu guda ɗaya.

    [ad_2]

    Source link

  • Matatar Dangote ta rage farashin man fetur

    [ad_1]



    Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 1,175 kan kowace lita zuwa naira 1,075, wato ragin naira 100 kenan.

    Wata sanarwa da matatar ta wallafa a shafinta na X, ta ce matakin ya biyo bayan saukar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, kuma an yi hakan ne bisa sabon tsarin farashi da kamfanin ya fitar.

    Sanarwar ta kuma bayyana cewa matatar ta rage farashin man dizal zuwa naira 1,430 kan kowace lita, daga tsohon farashin naira 1,620.

    A Talatar da ta gabata ce farashin mai ya faɗi a duniya bayan Shugaba Donald Trump ya yi hasashen kawo ƙarshen yakin Gabas ta Tsakiya nan ba da jimawa ba.

    Man Fetur samfurin Brent ya faɗi da kusan kashi 10 zuwa ƙasa da dala 90 kowane ganga ɗaya a kasuwannin Asiya a ranar Talata, bayan da ya kai dala 119.50, farashi mafi tsada da aka taɓa gani tun tsakiyar 2022.


    [ad_2]

    Source link

  • Saudiyya Ta Rage Samar Da Man Fetur Saboda Matsalar Jigila A Hormuz

    [ad_1]

    Saudiyya ta rage yawan man fetur da take samarwa saboda matsalar jigilar kaya ta ruwa a kogin Hormuz, sakamakon rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

    Sauran ƙasashen da ke cikin ƙungiyar OPEC kamar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Kuwait da Iraq su ma sun rage yawan man fetur da suke samarwa.

    • SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 22
    • Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 5 A Jihar Zamfara

    Masana sun ce Saudiyya ta rage samar da man tun da wuri domin kada tankunan ajiyarta su cika, tare da tabbatar da cewa rijiyoyin man nata na ci gaba da aiki ba tare da an rufe su gaba ɗaya ba.

    A kullum Saudiyya na samar da kusan ganga miliyan 10 na man fetur, kuma tana fitar da kusan ganga miliyan bakwai zuwa ƙasashen waje.

    Saboda wahalar wucewa ta mashigar Hormuz, Saudiyya na karkatar da wasu daga cikin man zuwa Yanbu ta hanyar bututun mai da ya nufi Red Sea.

    Sai dai wannan bututun na iya ɗaukar ganga miliyan biyar ne kawai a rana, wanda bai kai yawan man da ake fitarwa ba.

    Wannan matsala ta sa farashin man fetur a duniya ya haura dala 100 kan kowace ganga, tare da jawo matsaloli a harkokin samar da shi a duniya.

    Masana sun yi gargaɗin cewa idan rikicin ya ci gaba, zai iya jawo hauhawar farashi a duniya.

    A halin yanzu kamfanin man fetur na ƙasar, Saudi Aramco, bai fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, yayin da yawancin jiragen ruwa masu ɗaukar man fetur ke gujewa wucewa ta mashigar Hormuz saboda dalilan tsaro.

    [ad_2]

    Source link

  • Gwamna Abba ya sauke Shugaban Ma’aikatan Kano

    [ad_1]



    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shugaban Ma’aikatan Jihar, Abdullahi Musa, daga muƙaminsa nan take.

    Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.

    Sanarwar ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na sake fasalta aikin ma’aikatan gwamnati domin ƙara inganci, ladabtarwa da kuma inganta ayyukan hidima ga jama’a a hukumomin gwamnati.

    Gwamna Yusuf ya kuma gode wa tsohon Shugabar Ma’aikatan Jihar bisa gudunmawar da ya bayar wajen hidimta wa jihar a lokacin da yake kan muƙamin.

    Hakazalika, gwamnan ya umarci Bilkisu Shehu Maimota, Babbar Sakatare a Sashen Gudanarwa da Ayyuka na Ofishin Majalisar Zartarwa, da ta riƙe mukamin Shugabar Ma’aikatan Jihar na riƙon ƙwarya har sai an naɗa wanda zai riƙe muƙamin na dindindin.

    An kuma umarci tsohon Shugabar Ma’aikatan Jihar da ya miƙa ragamar ofishin ga wadda aka naɗa riƙon ƙwarya kafin ranar Laraba, 11 ga Maris, 2026.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnati Ta San Sunaye Da Wuraren Da ‘Yan Ta’adda Suke — Sheikh Gumi

    [ad_1]

    Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce Gwamnatin Nijeriya ta san sunaye da kuma wuraren da ‘yan ta’adda ke ɓoye a ƙasar.

    Malamin ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da DRTV, inda yake mayar da martani kan zargin cewa yana da alaƙa da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

    • Ramadan: ‘Yansanda Sun Buƙaci A Sanya Ido A Kano A Goman Ƙarshe
    • Kamfanonin Kasa Da Kasa Sun Nuna Gamsuwa Da Dimbin Damarmakin Da Kasuwar Kasar Sin Ta Samar

    A cewarsa, gwamnati na da cikakken bayanai game da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

    “Gwamnati ta san kowane ɗan ta’adda da sunansa da kuma inda yake,” in ji Gumi.

    Ya kuma kare kansa kan ganawar da ya taɓa yi da ‘yan bindiga, yana mai cewa bai taɓa zuwa tattaunawa da su shi kaɗai ba.

    Ya ce yawanci yana zuwa ne tare da jami’an tsaro kamar ‘yansanda da sojoji, sannan a wasu lokuta tare da sarakuna.

    Gumi, wanda tsohon likita ne kuma tsohon kyaftin a rundunar sojojin Nijeriya, ya sha bayyana cewa tattaunawa da ‘yan bindiga na iya taimakawa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, maimakon dogaro da ƙarfin soji kawai.

    Har yanzu gwamnatin tarayya da jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba kan wannan iƙirari nasa.

    [ad_2]

    Source link

  • Gwamna Abba Ya Sauke Shugaban Ma’aikatan Kano Daga Muƙaminsa

    [ad_1]

    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin jihar, Abdullahi Musa, daga muƙaminsa.

    Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da yammacin ranar Talata.

    • Cinikin Kasar Sin a Watanni 2 Na Farkon Bana Ya Karu Da 18.3% Idan Aka Kwatanta Da Na Shekarar Da Ta Gabata
    • Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 5 A Jihar Zamfara

    Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na inganta aikin ma’aikatan gwamnati a jihar, domin ƙara inganci, bin doka da kuma kyautata ayyukan da suke yi wa jama’a.

    Gwamnan ya gode wa tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin bisa gudunmawar da ya bayar da kuma jajircewarsa wajen yi wa Jihar Kano hidima a lokacin da yake kan muƙaminsa.

    Haka kuma, gwamnan ya umarci Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, wadda ke riƙe da muƙamin Babbar Sakatare mai kula da harkokin gudanarwa da ayyuka a Ofishin Majalisar Zartarwa, da ta riƙe muƙamin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na riƙon ƙwarya har sai an naɗa wanda zai maye gurbin.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa an umarci Abdullahi Musa da ya miƙa ragamar ofishin ga mai riƙon muƙamin kafin ko a ranar Laraba, 11 ga watan Maris, 2026.

    [ad_2]

    Source link

  • DAGA LARABA: Yadda Sinadaran Dandanon Abinci Ke Yin Illa Ga Lafiya

    [ad_1]

    Ƙarin Podcasts



    A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu.

    Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsalolin lafiya.

    Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin abubuwan da idan aka tara su a jiki na dogon lokaci, na iya haifar da illa.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan irin matsalolin da amfani da sinadarin dafa abinci fiye da kima ke jawowa ga lafiyar mutane.

    Domin sauke shirin, latsa nan


    [ad_2]

    Source link

  • SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 22

    [ad_1]

    Fa’idar Sahur

    1. Yin sahur koyi ne da annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam), kuma malamai sun yi ijma’i a kan mustahabbi ne yinsa kamar yadda Ibnul Munzir da Imamu Annawawi suka naƙalto.

    2. Yin sahur saɓa wa Yahudu da Nasara ne, domin su ba sa yin sahur a azuminsu kamar yadda Muslim da Abu Dawud Tirmizi da Nasa’i suka ruwaito.

    • Darussa Daga Ramadan Na 9: Danne Fushi Da Nutsuwa A Ramalana
    • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 10

    3. Sahur albarka ne ga mai yinsa kamar yadda hadisi ya gabata.

    4. Sahur yana samar da karfi ga mai azumi wajen yin ibada, da kuma ƙaruwar nishadi, da kuma tunkuɗe mummunar dabi’a da yunwa take haifarwa. Kuma a lokacin yinsa sahur, mutum yana samun dama ya yi sadaƙa ga almajiri ko kuma su ci tare. kuma yana sa mutum ya yi zikiri da addu’a, domin lokacin ne da ake karbar addu’a… “kamar yadda Hafiz Ibnu Hajar ya bayyana a littafinsa Fathul Bari (4/496) da malaminsa Ibnu Mulaƙƙin a cikim  al’I’ilamu (5/187)

    5. Samun salati daga Allah da mala’ikunsa.

    Allah ya datar da mu ga koyi da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam) a cikin al’amuranmu baki daya.

    [ad_2]

    Source link