Rokar Smart Dragon-3 Ta Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan’adam Daga Teku
Rokar kasar Sin mai suna Smart Dragon-3 ta tashi a jiya Lahadi a lardin Shandong dake gabashin kasar Sin, inda ta aika rukunin taurarin dan’adam na CentiSpace 02 zuwa da’irar sararin saramaniya da aka tsara hawansu. Rokar ta tashi da karfe 11:49 na dare bisa agogon Beijing daga teku a kusa da birnin Haiyang. Cibiyar…