Zargin ɗaukar nauyin ta’addanci: Ba a samu makamai a gidana ba — Malami
[ad_1]
Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya musanta rahotannin da ke cewa an gano makamai a wasu gidaje da ake zargin mallakinsa ne.
A cikin wata sanarwa da hadiminsa kan yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya fitar a ranar Laraba, Malami ya ce labaran ba gaskiya ba ne.
Ya ce: “Muna musanta iƙirarin da ke cewa an gano makamai ko harsasai a dukkanin wani gida da ake alaƙnta da Abubakar Malami, SAN.”
Ya ce babu wata hukuma da ta sanar da shi, iyalansa ko lauyoyinsa cewa an samu makamai a gidansa.
Sanarwar ta zargi wasu kafafen yaɗa labarai da yaɗa jita-jita ba tare da yin bincike na gaskiya ba.
Ta jaddada cewa Malami ba a same shi da laifi ba, kuma doka ta tanadi a ɗauke shi a matsayin ba shi da laifi har sai kotu ta tabbatar da akasin haka.
Malami, ya kuma musanta duk wata alaƙa da ta’addanci ko ɗaukar nauyin ta’addanci, yana mai cewa an yi zargin ba tare da kawo suna, ƙungiya, ma’amala ko wata hujja mai inganci ba.
Ya kara da cewa: “Haka kuma muna yin watsi da duk wani zargi da ke danganta Abubakar Malami, SAN, da ta’addanci ko ɗaukar nauyin ta’addanci.
“Waɗannan iƙirari ba su da hujja, sun kasance jita-jita ne kawai kuma marasa tushe.”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa tun bayan kama Malami da Hukumar DSS ta yi a ranar Litinin, an hana shi ganin iyalansa da lauyoyinsa, wanda hakan ya saɓa da dokokin Najeriya.
Ta ƙara da cewa irin waɗannan labarai sun jefa iyalan Malami da abokan aikinsa cikin damuwa.
Sanarwar ta tunatar da cewa Malami jigo ne a jam’iyyar ADC kuma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Kebbi a 2027, inda ta bayyana cewa siyasa bai kamata a yi amfani da siyasa wajen hana sa cikar muradinsa ba.
A ƙarshe, Malami ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da suke bambance tsakanin zargi da gaskiya, tare da barin doka ta yi aikinta yadda ya dace.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link