Yadda Amurka Za Ta Iya Yin Tasiri A Zaɓen Nijeriya Na 2027 — Yakubu Dogara
[ad_1]
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya ce Amurka na iya yin tasirin gaske a zaɓen 2027 a Nijeriya saboda muhimmancin da ƙasar ke da shi a Afirka.
Da yake magana a gidan talabijin na Channels, Dogara ya ce tsarin siyasar duniya a yanzu ya raunana, kuma manyan ƙasashe na ƙoƙarin kare muradunsu ne kawai.
- Kasar Sin Ta Dade Tana Zama Aminiya Kuma ’Yar Uwa Ga Kasashen Afirka
- Ministocin Wajen Sin Da Nijeriya Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Diflomasiyya
Ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi hattara ba, za a iya yanke hukunci kan makomar Nijeriya ba tare da ita ba.
A cewarsa, Amurka da sauran manyan ƙasashe na damuwa da zaman lafiyar Nijeriya, domin duk wata matsala a nan na iya shafar ɗaukacin Afirka.
Wannan ne zai sa hankalinsu ya fi karkata ga zaɓen 2027 mai zuwa.
Dogara ya kuma yi tsokaci kan rahoton cewa gwamnatin Nijeriya ta biya dala miliyan 9 ga wani kamfani domin neman goyon baya a Amurka.
Ya ce neman goyon baya ba laifi ba ne a hulɗar ƙasa da ƙasa, amma idan har an biya wannan adadi, ya yi yawa.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan hulɗar dole ne su kasance a bayyane.
Ya jaddada cewa dole ne Nijeriya ta tsara manufofinta na harkokin waje cikin hikima, musamman a wannan lokaci da siyasar duniya ke cike da sauye-sauye.
[ad_2]
Source link