Shugaban Xi Ya Karbi Sabbin Jakadun Kasashen Waje A Kasar Sin


A yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karbi takardun sabbin jakadu 18 da aka turo kasar Sin.

Da yake jawabi ga jakadun, ya ce duniya a yanzu na fama da manyan sauye-sauye cikin sauri, irin wadanda ba kasafai ake gani ba, inda yanayin duniya ke kara fuskantar sauye-sauye da hargitsi da kalubale.

Ya kara da cewa rarrabuwar kawuna da fito-na-fito da cin nasara da faduwar wani bangare ba su da wata makoma, kuma dawo da amfani da karfi a duniya ba abu ne da jama’ar duniya ke son gani ba, yana mai cewa hadin kai da goyon bayan juna su ne kadai zabukan da suka dace. (FMM)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *