Kenya Ta Gudanar Da Taron Bita Domin Karfafa Amfani Da Fasahar Juncao Ta Kasar Sin A Fannin Abinci

[ad_1]

An bude wani taron bita kan karfafa amfani da fasahar Juncao ta kasar Sin a fannin abinci, da kawar da fatara, da daukan mataki kan sauyin yanayi jiya Talata a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, wanda ya samu halartar masu tsara manufofi, da masana kimiyya, da manoma da kuma ‘yan kasuwa.

Ma’aikatar bunkasa aikin gona da kiwo ta kasar Kenya, da sashen kula da shirin muradun ci gaba masu dorewa, watau SDGs, da ke karkashin sashen raya harkokin tattalin arziki da zamantakewa na MDD, watau UNDESA, da jami’ar aikin gona da gandun daji ta Fujian ta kasar Sin, watau FAFU ne suka shirya taron na kwanaki uku.

Da yake jawabi a taron, babban jami’in reshen kula da tsare-tsare na kasa da inganta kwazon aiki a bangaren shirin SDG na sashen UNDESA Amson Sibanda, ya ce da zarar an fara amfani da ita sosai, fasahar Juncao za ta bunkasa samar da wadatar abinci da juriyar sauyin yanayi tare da kawo kyakkyawan sauyi ga jin dadin rayuwa a Kenya. Ya ce fasahar Juncao wadda masana kimiyya na jami’ar FAFU suka kirkiro, ta zama abar koyi a hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *