Mazauna Borno da Yobe sun san waɗanda suka kai hare-haren Maiduguri — CDS

[ad_1]



Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya ce mazauna jihohin Borno da Yobe sun san waɗanda ke da hannu a hare-haren ƙunar baƙin wake da aka kai Maiduguri, kuma dole su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar ta’addanci.

Ya bayyana hakan ne a Maiduguri bayan shi da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, suka koma can bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.

Wannan na zuwa ne biyo bayan hare-hare a baya-bayan nan da suka yi sanadiyyar mutuwa da jikkata mutane.

Oluyede, ya ce yawancin maharan ’yan yankin ne kuma ana san su yayin da suke rayuwa cikin mutane.

Ya bayar da misalin wani hari a Kukawa inda aka gano cewa wasu daga cikin maharan daga garin suke.

Ya jaddada cewa kawo ƙarshen matsalar na buƙatar haɗin kan jama’a, yana mai kira ga mazauna yankunan su ɗauki alhakin taimaka wa jami’an tsaro.

Ya kuma ce ’yan ta’addan na amfani da jirage marasa matuƙa da sabbin fasahohi, amma sojoji na ƙara inganta kayan aikinsu domin tunkarar su.

Hare-haren Boko Haram sun yi ƙamari a baya-bayan nan, inda suke farmakar sojoji da kuma fararen hula.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *