Cutar Lassa: Mutum 44 Sun Kamu, 6 Sun Mutu A Nijeriya Cikin Mako 1

[ad_1]

NCDC, ta bayyana samun karuwar masu kamuwa da zazzabin Lassa a kasar, inda aka tabbatar da sabbin mutum 44 da suka kamu da cutar tare da mutuwar mutum shida a mako na biyar na shekarar 2026.

An samu sabbin masu kamuwa da cutar ne a jihohi bakwai: Bauchi, Ondo, Taraba, Edo, Filato, Benuwe da Ebonyi.

Rahoton halin da ake ciki ya nuna cewa daga mako na daya zuwa na biyar, Nijeriya ta samu jimillar mutuwar mutane 31, wanda ke nuna kason mace-mace (Case Fatality Rate – CFR) na kashi 18.8 cikin 100, kadan kasa da kashi 19.6 cikin 100 da aka samu a irin wannan lokaci a bara.

A jimlace, jihohi tara sun tabbatar da a kalla mutum guda da ya kamu da cutar a kananan hukumomi 33, lamarin da ke nuna yadda cutar ke ci gaba da yaduwa.

Rahoton ya kuma nuna cewa yawancin masu kamuwa da cutar sun fi yawa a jihohi biyar masu dauke da babban nauyi, wadanda suka hada da kashi 92 cikin 100 na dukkan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar: Bauchi kashi (47%), Ondo kashi (18%), Taraba kashi (14%), Edo kashi (8%) da Filato kashi (5%). Sauran kashi 8 cikin100 an same su ne daga wasu jihohi hudu.

Rahoton ya bayyana cewa manya masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 su ne suka fi kamuwa da cutar, yayin da shekarun masu dauke da cutar suka fara daga jarirai har zuwa tsofaffi masu shekaru 1 zuwa 74.

Duk da karuwar sabbin wadanda aka tabbatar sun kamu, NCDC ta ce an samu raguwar wadanda ake zargi da kuma wadanda aka tabbatar sun kamu idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekarar 2025. Sai dai an samu kamuwar ma’aikacin lafiya guda a mako na biyar, wanda ke nuna hadarin da ma’aikatan lafiya ke ci gaba da fuskanta.

A matsayin martani, NCDC ta ce an kulla tsarin hadin gwiwa na kasa kan zazzaBin Lassa wato (National Lassa FeBer multi-partner, multi-sectoral Incident Management System – IMS) domin inganta daidaituwa da karfafa matakan dakile cutar a dukkan matakan gwamnati.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *