Iraniyawa sun gudanar da sallar Idi duk da yaƙi ya tsananta a Gabas ta Tsakiya

[ad_1]



A yayin da yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da tsananta, dubban Musulmi a ƙasar Iran sun gudanar da idin salla ƙarama a ranar Asabar bayan kammala azumin watan Ramadan.

Gidajen talabijin na ƙasar sun nuna yadda aka gudanar da sallar a babban birnin Tehran, inda aka samu cunkoson masu ibada a masallaci da ma wajen harabar sa saboda ƙarancin fili, duk da barazanar hare-hare.

A bisa al’ada, jagoran addini na ƙasar ne ke jagorantar sallar Idi, amma sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, bai halarci sallar ba, kuma bai fito bainar jama’a ba tun bayan naɗa shi a farkon watan nan.

Sai dai shugaban sashen shari’a na ƙasar, Gholam Hossein Mohseni Ejei, shi ne ya halarci sallar a babban masallacin Imam Khomeini da ke tsakiyar birnin.

Ƙasar Iran, wadda galibin al’ummarta mabiya Shi’a ne, ta gudanar da Idin ne kwana ɗaya bayan yawancin ƙasashen Musulmi na Sunni sun gudanar da ta su a ranar Juma’a.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren bama-bamai ke ci gaba da aukuwa a sassa daban-daban na ƙasar, musamman a Tehran da kuma birnin Isfahan, tun bayan fara yaƙin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a ranar 28 ga watan Fabrairu.

Duk da haka, an kuma gudanar da sallar Idin a wasu biranen ƙasar kamar Arak, Zahedan da Abadan, inda jama’a suka fito domin gudanar da ibada duk da yanayin rashin tsaro.

Masu lura da al’amura na ganin cewa ci gaba da gudanar da ibada a irin wannan yanayi na nuna ƙarfin zuciya da jajircewar al’ummar ƙasar duk da ƙalubalen da suke fuskanta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *