Category: Latest News

  • Sallah: Sibil Difens ta jibge jami’anta 700 don tabbatar da tsaro a Gombe

    [ad_1]



    Hukumar Sibil Difens a Jihar Gombe, ta sanar da tura jami’anta guda 700 zuwa sassan jihar daban-daban, domin tabbatar da tsaro yayin bukukuwan salla ƙarama.

    Wannan matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Buhari Sa’ad, ya fitar a madadin kwamandan jihar, Jibrin Idris.

    Rundunar ta bayyana cewa an tsara aikin ne na musamman tsakanin ranakun 19 zuwa 21 ga watan Maris, 2026.

    Kwamandan ya bayyana cewa an riga an jibge jami’an a wuraren da ake ganin sun fi buƙatar kulawa, ciki har da filin Idi da hanyoyin da za a bi domin yin hawan salla.

    Ragowar wuraren sun haɗa da wuraren shaƙatawa, kasuwanni, tashoshin mota da manyan hanyoyin shige da fice na jihar.

    Baya ga kare rayukan jama’a, Jibrin Idris, ya jaddada cewa rundunar za ta sanya idanu kan kadarorin gwamnati da na jama’a domin daƙile masu son yin amfani da lokacin wajen yin ɓarna.

    Ya kuma tabbatar da cewa suna aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da doka da oda.

    Yayin da yake jan kunnen jami’an da aka tura su gudanar da aiki da gaskiya da ƙwarewa, kwamandan ya kuma taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.

    Ya ƙarƙare da yin kira ga mazauna jihar da su gudanar da bukukuwan cikin lumana, sannan su kasance masu sanya idanu tare da kai rahoton duk wani ga jami’an tsaro mafi kusa da su.


    [ad_2]

    Source link

  • Adadin Wutar Lantarki Da Xinjiang Ta Samar Ga Sauran Wurare Daga Makamashi Mai Tsafta Ya Wuce Biliyan 304 Kwh

    [ad_1]

    Rahotanni na cewa ya zuwa yau Laraba, adadin wutar lantarki da jihar Xinjiang ta aikawa sauran wurare a nan kasar Sin, bisa makamashi mai tsafta ya kai biliyan 304.36 kilowatt-hour, adadin da ya kai kusan kashi 30 cikin 100 na dukkan wutar lantarki da ta samarwa sauran wuraren kasar.

    Xinjiang, muhimmiyar tasha ce ta samarwa sauran wuraren kasar Sin wutar lantarki, a cikin tsarin jigilar wutar lantarki daga yamma zuwa gabas, da tsarin samarwa sauran wuraren wutar lantarki bisa makamashi mai tsabta.

    Ya zuwa karshen shekara ta 2025, Xinjiang ta gina manyan tasoshin samar da wutar lantarki bisa makamashi mai tsabta 6, masu karfin kilowatts miliyan 10, kuma karfin samar da wutar lantarki daga makamashi mai tsafta ya kai kilowatts miliyan 169, adadin da ya kai kashi 64 cikin 100 na jimillar karfin samar da wutar lantarki a Xinjiang. (Amina Xu)

    [ad_2]

    Source link

  • Eid-fitr: Gwamnatin Kano Ta Sanya Tsauraran Matakai Kan Hawan Sallah Saboda Tsaro

    [ad_1]

    Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da tsauraran matakai kan bukukuwan Hawan Sallah mai zuwa, sakamakon sahihan rahotannin sirri da Majalisar tsaro ta jihar ta samu da ke nuna yiwuwar tayar da tarzoma.

    Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa labarai, Ibrahim Wayya ya fitar ta bayyana cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ne zai jagoranci Hawan Idi daga Kofar Mata zuwa Kofar Fatalwa, inda da Hawan Nassarawa kuma za a yi shi a salo na musamman ba tare da hawa dowakai ba.

    • Mataimakin Gwamnan Kano Na Iya Yin Murabus Saboda Barazanar Tsige Shi
    • Trump Ya Ce Amurka Za Ta Ci Gaba Da Yaƙi Da Iran Ba Tare da Taimakon Kowa Ba

    Sanarwar ta ƙara da cewa, an dakatar da Hawan Daushe da Hawan Fanisau da kuma Hawan Dorayi, na ɗan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya.

    Gwamnatin ta ce duk da ƙudurin ta na kare al’adun Kano, za ta fifita kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da doka da oda.

    An umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da bin waɗannan matakai, tare da kira ga jama’a da su kasance masu natsuwa da bin doka tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a lokacin bukukuwan Sallar.

    [ad_2]

    Source link

  • HOTUNA: Yadda ziyarar Tinubu ke kasancewa a Birtaniya

    [ad_1]



    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da mai ɗakinsa, Oluremi Tinubu, sun samu kyakkyawar tarba a Birtaniya yayin wata muhimmiyar ziyara da suka kai.

    Sarki Charles III ne, ya tarbi Tinubu a Windsor Castle, wanda ya zama ziyara ta farko daga Najeriya cikin shekaru 37.

    A yayin ziyarar ta kwanaki biyu, manyan gidan sarautar Birtaniya sun tarbi Tinubu, ciki har da Sarauniya Camilla, Yarima William da Gimbiyar Catherine.

    Ziyarar ta ƙunshi al’adun sarauta kamar faretin sojoji, hawa keken doki da sauransu.

    An fara tarbar Tinubu da matarsa a Fairmont Windsor Park kafin daga bisani suka wuce Windsor Castle domin bikin tarbarsu a hukumance.

    A wajen bikin, an yi gaisuwar ban girma ta sojoji tare da rera taken Najeriya da na Birtaniya.

    A gefe guda Shugaba Tinubu ya duba jerin sojoji, yayin da Sarki Charles ke tsaye a bayansa, alamar kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.

    Ga hotunan:


    [ad_2]

    Source link

  • An gargaɗi jama’a su yi aiki tare da hukumomin tsaro a Yobe

    [ad_1]



    Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta nuna matuƙar tausayawa ga gwamnati da al’ummar Maiduguri, jihar Borno, bayan afkuwar fashewar bama-bamai da suka faru a ranar 16 ga Maris, 2026, da misalin ƙarfe 18:30 a wurare daban-daban a cikin Maiduguri.

    A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Dungus Abdulkareema a ranar Talata 17 ga Maris 2026 ya fitar ya ce, rundunar ta yi kira ga mazauna jihar Yobe da su kwantar da hankalinsu, su yi taka-tsantsan, kuma su kasance cikin tsaro, musamman a ciki da kewayen al’ummominsu, wuraren jama’a da sauran wurare masu cunkoso.

    Bayan taron majalisar tsaron Jiha da aka gudanar a fadar gwamnatin Jihar Yobe a ranar 16 ga Maris, 2026, wanda ya shafi dukkan hukumomin tsaro a jihar, an sanya tsauraran matakan tsaro a faɗin jihar kafin bukukuwan Sallah mai zuwa kamar yadda tun farko gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya bada umarni akan hakan.

    Kwamishinan ‘Yan Sanda, Emmanuel Ado, psc, fdc, ya umarci Kwamandojin yankuna, Jami’an ‘yan Sanda na Sashe, Sashen dabaru, da sashen leƙen asiri da su tabbatar da tsaro mai inganci a cibiyoyin ibada, wuraren shaƙatawa na jama’a, da sauran wurare masu muhimmanci kafin, lokacin da kuma bayan bukukuwan Sallah.

    Ana ƙarfafawa jama’a da su yi aiki tare da hukumomin tsaro ta hanyar samar da sahihan bayanai game da harkokin mutane, motoci ko babura da ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

    Ana kuma gargaɗin masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanya da su guji tuƙi ba tare da kulawa ba da kan haifar da haɗari a lokacin bukukuwan domin tabbatar da tsaron jama’a.


    [ad_2]

    Source link

  • Sarki Sanusi ne zai jagoranci Hawan Sallah — Gwamnatin Kano

    [ad_1]



    Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, shi ne zai jagoranci Hawan Sallar Idil-Fitr na wannan shekarar, yayin da ta fitar da tsauraran matakai domin hana ɓarkewar tarzoma a lokacin shagulgulan.

    Gwamnatin ta bayyana cewa, wannan shawara wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ita, ta biyo bayan rahotannin sirri ne da ke nuna yunƙurin wasu mutane na tada zaune tsaye a lokacin Sallar.

    A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar ranar Laraba, gwamnatin ta ce tana nan kan bakanta na kiyaye al’adun Kano, amma zaman lafiya da tsaro su ne a gaba.

    A cewar sanarwar, Sarki Sanusi zai gudanar da Hawan Idi tun daga filin Sallar Idi na Kofar Mata, ta hanyoyin da aka ware zuwa Gidan Shettima, sannan ya ƙarƙare a Kofar Fatalwa ta fadar Sarki.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, za a gudanar da Hawan Nasarawa ta wani salo na daban ba tare da jerin gwanon dawakai ba, yayin da aka dakatar da Hawan Daushe da Hawan Fanisau, da Hawan Dorayi a halin yanzu domin tabbatar da tsaron jama’a.

    Gwamnatin ta ce an umarci dukkan hukumomin tsaro da su tsananta sanya ido tare da tabbatar da ganin an bi waɗannan dokoki daki-daki kafin sallah, lokacin sallah da kuma bayan shagulgulan.

    Haka kuma, ta buƙaci mazauna jihar da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka, sannan su ba hukumomin tsaro haɗin kai, tare da yin gargaɗi kan yaɗa labaran da ba a tantance ba.


    [ad_2]

    Source link

  • Tawagar Gwamna ta gana da Sarki Sanusi II

    [ad_1]



    ’Yan sa’o’i kaɗan bayan karɓar baƙuncin manyan jami’an gwamnati a taron buɗe baki (Iftar) a fadarsa, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya gudanar da wata ganawar sirri da wata tawaga daga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

    Lamarin dai ya rura wutar hasashen matsayar jihar kan taƙaddamar sarautar da ake yi.

    Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya tabbatar da ganawar a wani saƙo da ya wallafa a Facebook da safiyar ranar Laraba, inda ya ce an gudanar da ganawar ne a fadar Gidan Rumfa.

    Ya bayyana cewa, waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Umar Ibrahim, Shugaban Ma’aikatan Gwamna, Sulaiman Wali Sani, da kuma shi kansa.

    Dawakin Tofa ya rubuta cewa: “Jim kaɗan bayan buɗe baki a Fadar Sarki, tawagar Gwamnan ta yi wata ganawar sirri da Mai Martaba.”

    Wannan na zuwa ne yayin da birnin Kano ke shirye-shiryen shagulgulan ƙaramar Sallah na Idil-Fitr da kuma gagarumin Hawan Sallah na tarihi.

    Hawan Sallar, wanda tsohon al’ada ne da aka daɗe ana yi, ya shiga yanayin rashin tabbas biyo bayan maganganu masu karo da juna daga jami’an gwamnati kan ko za a yi shi a wannan shekarar, ganin yadda har yanzu akwai taƙaddamar shari’a tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero da ba a warware ba.

    Duk da cewa Gwamna Yusuf ya mayar da Sanusi II kan mulki a shekarar 2024, Bayero na ci gaba da ƙalubalantar tsige shi a kotu, wanda hakan ya sa batun sarautar ke cikin ruɗani.


    [ad_2]

    Source link

  • Tinubu zai gana da Sarki Charles III

    [ad_1]



    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai gana da Sarki Charles III a yau Laraba domin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu da gano damar ƙarin zuba hannun jarin ’yan kasuwa.

    Bola Tinubu da matarsa, Oluremi Tinubu, sun isa filin jirgin saman Stansted ranar Talata inda Sarki Charles zai karɓi Tinubu a gidan sarauta na tarihi na Windsor Castle kafin ya shirya liyafar ƙasa da ƙasa da yamma.

    Birtaniya da Najeriya na da kyakkyawar alaƙa ta diflomasiyya, inda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniya ta haɗin kai a Nuwamba 2024 don ƙarfafa tattalin arziki da shige da fice da kuma tsaro kamar yadda majiyar BBC ta ruwaito.

    An kuma tsara cewa, ranar Alhamis, Tinubu zai gana da  sabon Firaiministan Birtaniya Keir Starmer da ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje.


    [ad_2]

    Source link

  • Mutum Ɗaya Ya Mutu A Faɗan Daba A Jihar Kano

    [ad_1]

    Mutum ɗaya ya rasu bayan wani rikici tsakanin ƙungiyoyin ’yan daba biyu ya ɓarke a Jihar Kano.

    Masanin harkokin tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

    • CAF Ta Soke Nasarar Senegal, Ta Ayyaṇa Morocco A Matsayin Zakarar AFCON Ta 2025
    • Tinubu Ya Bai Wa Masu Riƙe Da Muƙamai Da Ke Son Yin Takara Wa’adin Yin Murabus

    Rahoton ya ce rikicin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a yankin Ja’en Unguwar Lalle, bayan wani zaman sulhu tsakanin ɓangarorin biyu.

    Wani mazaunin yankin ne ya kira jami’an tsaro domin neman agaji, inda jami’an ’yansanda suka gaggauta zuwa wajen suka daƙile rikicin tare da dawo da zaman lafiya.

    ’Yansanda sun kama shugabannin ƙungiyoyin biyu da ake zargi: Abubakar Abdullahi mai shekaru 22 daga Sabuwar Madina, da Abubakar Bello wanda aka fi sani da Babuji, mai shekaru 18 daga Unguwar Lalle.

    Mutane uku sun samu munanan raunuka a rikicin, inda aka kai su Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad domin duba su.

    Ɗaya daga cikinsu, Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, wanda ya samu mummunan rauni a wuya, ya rasu daga baya, yayin da sauran biyu ke ci gaba da jinya.

    A wani samame da ’yansanda suka kai, sun sake kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a rikicin.

    An kuma ƙwato makamai kamar adda, takobi da kuma wasu kayan tsafe-tsafe a hannunsu.

    Jami’ai sun ce suna ci gaba da bincike, kuma za a fitar da ƙarin bayani nan gaba.

    [ad_2]

    Source link

  • Sojoji Sun Ƙwato Shanun Sata A Filato

    [ad_1]

    Sojojin Operation Safe Haven sun ƙwato wasu shanu da aka sace a Jihar Filato, bayan wani samame da suka gudanar a ƙaramar hukumar Riyom.

    Wannan na cikin wani saƙo da masanin harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X.

    • CAF Ta Soke Nasarar Senegal, Ta Ayyaṇa Morocco A Matsayin Zakarar AFCON Ta 2025
    • Madrid Da PSG Na Shirin Sayen Osimhen

    Rahoton ya ce sojojin Sashe na 6 da ke Makera sun samu sahihan bayanai da misalin ƙarfe 7:20 na safiyar ranar Litinin, game da motsin wasu shanu da ake zargin an sace su a kusa da ƙauyen Tahoos.

    Nan take sojojin suka kai samame yankin, inda suka gano shanu shida da ɓarayin suka bari bayan sun gudu da ganin jami’an tsaro.

    Daga baya an miƙa shanun ga mai su.

    Majiyoyin tsaro sun ce sojoji na ci gaba da sintiri a yankin domin hana sake faruwar irin wannan laifi da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

    [ad_2]

    Source link