Category: Latest News

  • Ba a ga jinjirin watan Shawwal a Najeriya ba — Sarkin Musulmi

    [ad_1]



    Majalisar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, tare da haɗin gwiwar Kwamitin Ƙasa na Ganin Wata, sun sanar da cewa ba su samu rahoton ganin jinjirin watan Shawwal ba a ko ina a Najeriya.

    Sakamakon haka, majalisar ta ayyana ranar Juma’a a matsayin 1 ga watan Shawwal na shekarar 1447 bayan hijira, wadda ta yi daidai da 20 ga watan Maris, 2026.

    Hakan na nufin ranar Juma’a za ta kasance ita ce ranar ƙaramar sallar bana.

    Haka kuma, Musulmi a faɗin Najeriya za su azumci ranar Alhamis domin cike azumin watan Ramadan zuwa 30, kasancewar ba a ga jinjirin watan Shawwal ba.

    Sarkin Musulmi, ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumi, tare da yin kira gare su da su ci gaba da yin ibada da ayyukan alheri.

    Ya ce: “A ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya da aminci da kwanciyar hankali, da kuma neman sauƙin halin da ake ciki.”

    Ya ƙara da cewa: “A riƙa yi wa shugabanni addu’a domin Allah Ya ɗora su a kan abin da zai zama maslaha da alheri ga wannan ƙasa.”


    [ad_2]

    Source link

  • An Kama Mutane Shida Da Ake Zargi Da Lalata Layin Dogo A Kano – NSCDC

    [ad_1]

    Hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya (NSCDC), reshen Jihar Kano, ta kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen cirewa da satar abin ƙulle layin dogo ba bisa ka’ida ba a Ƙaramar Hukumar Kiru ta jihar.

    Kwamandan NSCDC na jihar, Mohammed Agalama, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar a ranar Laraba.

    Ya ce, “Hukumar NSCDC reshen Jihar Kano na sanar da al’umma cewa ta kama wasu mutane shida da ake zargi da lalata tare da satar katakon layin dogo a Ƙaramar Hukumar Kiru ta Jihar Kano.”

    A cewarsa, jami’an hukumar masu lura da tsaro sun kama waɗanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma ci gaba da gudanar da aikin sa ido na musamman.

    [ad_2]

    Source link

  • Sibil Difens ta kama mutum 6 kan satar ƙarfen digar jirgin ƙasa a Kano

    [ad_1]



    Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Kano, ta kama mutum shida da ake zargi da satar ƙarfen digar jirgin ƙasa a Ƙaramar Hukumar Kiru.

    Kwamandan hukumar a jihar, Mohammed Hassan Agalama ne, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba.

    Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanai da kuma sa ido da jami’ai suka yi.

    Agalama, ya bayyana wannan aiki a matsayin lalata tattalin arziƙi da kuma barazana ga tsaron jama’a.

    Waɗanda aka kama, dukkaninsu ’yan asalin Jihar Kaduna ne, sun haɗa da Sulaiman Salisu mai shekaru 45, Musa Aliyu Harisu (22), Ishaq Alhassan (20), Isa Aminu (35), Sadiq Bala (20) da Mansur Idris (22).

    Kayan da aka ƙwato sun haɗa da ƙarfen jirgin ƙasa da aka lalata, ƙusoshi 60, da kayan aiki kamar tankunan gas da bututun roba da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.

    Bincike ya nuna cewa suna shirin sayar da kayan ne domin samun kuɗi.

    Kwamandan ya jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci lalata kadarorin gwamnati ba, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.


    [ad_2]

    Source link

  • Sin Ta Samun Gaggarumin Ci Gaban Ayyukan Taimakon Masu Bukata Ta Musamman

    [ad_1]

    Kwanan nan, aka rufe gasar wasannin Olympics ta masu bukata ta musamman ta lokacin hunturu karo na 14 a Italiya. Tawagar ‘yan wasa ta Sin ta samu lambobin yabo 44, ciki har da zinare 15, azurfa 13 da tagulla 16 a gasar, lamarin da ya sa ta zo ta farko a wajen yawan cin lambobin zinare da kuma lambobin yabo gaba daya, kuma hakan ya zama mafi kyawun sakamako a tarihin kasar wajen halartar gasar da aka shirya a ketare. Yayin da aka daga tutar kasar Sin sau da dama a wajen gasar, nasarorin da ‘yan wasan masu bukata ta musamman na Sin suka samu ba wai kawai nasarori na wasanni ba ne, a maimakon haka, shaida ce na bunkasar ayyukan taimakon masu bukata ta musamman a Sin. Daga wannan bangare, muna iya ganin yadda ake ta inganta ayyukan tabbatar da rayuwar masu bukata ta musamman da yawansu ya kai miliyan 85 a nan kasar Sin.

    Ta fannin tabbatar da rayuwar masu bukata ta musamman, ya zuwa watan Yuni na shekara ta 2025, kimanin masu bukata ta musamman da ke cikin wahala miliyan 11 da dubu 884 na samun tallafin kudade daga gwamnatin Sin, kuma yawan masu bukata ta musamman da ke fama da tsananin nakasa da suke samun tallafin kudi na musamman ya kai miliyan 16.4. Har wa yau, yawan masu bukata ta musamman da suka shiga inshorar ritaya ga mazauna birane da karkara da inshorar kiwon lafiya ya kai kashi 90% da kuma 95%. Wadannan alkaluma sun shaida cewa, Sin tana da ingantaccen tsari na ba da tabbaci ga rayuwar masu bukata ta musamman.

    Ilimi shi ne mabudi ga masu bukata ta musamman don su cimma darajar rayuwarsu. A cikin shekaru biyar da suka gabata (2021-2025), adadin yara masu bukata ta musamman da suka shiga makaranta a matakin ilimin tilas na shekaru 9 ya karu zuwa kashi 97%. Sai kuma a bangaren aikin yi, adadin masu bukata ta musamman da ke da aikin yi a fadin kasar ya kai miliyan 9.01, kuma karin masu bukata ta musamman da suka samu guraben aikin yi a birane da karkara ya wuce miliyan 2.31. A halin yanzu ana aiwatar da “shirin aiki na shekaru uku don inganta samar da aikin yi ga masu bukata ta musamman (2025-2027)” , kuma ana ci gaba da yi wa tsarin aikin yi ga masu bukata ta musamman na Sin kwaskwarima ta yadda za a samar musu aikin yi mai kyau da inganci.

    Kimiyya da fasaha na taimaka wa masu bukata ta musamman wajen cimma burinsu. Daga fasahar hada kwakwalwa da na’ura da na’urori masu tallafa wa masu bukata ta musamman, zuwa hannayen mutum-mutumi masu sarrafa kansu, ana gaggauta amfani da fasahohin zamani wajen amfanar masu bukata ta musamman a yau da kullum.

    An rubuta nasarorin da ‘yan wasa masu bukata ta musamman na kasar Sin suka cimma a kundin tarihi, sai dai abin lura shi ne: sama da kashi 90% na masu bukata ta musamman a kasar suna samun tabbacin rayuwarsu, kuma masu bukata ta musamman miliyan 9.01 suna da aikin yi, baya ga kashi 97% na yara masu bukata ta musamman a kasar sun samu damar shiga makaranta, har ma ra’ayin tallafa wa masu bukata ta musamman ya yadu daga birane zuwa karkara, daga kayan aiki zuwa manhajoji. A nan Sin, kowane mai bukata ta musamman yana da damar cimma nasara dogaro da karfinsa!(Mai zane da rubutu: MINA)

    [ad_2]

    Source link

  • Yadda ake fitar da Zakkar Kono

    [ad_1]



    A yayin da watan Ramadan ɗin wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali.

    Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.”

    Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abin da za su ci a lokacin Ƙaramar Sallah.

    Yadda ake fitarwa

    Mutum zai fitar wa kansa da kuma waɗanda yake ciyarwa kamar mata, ’ya’ya da ma’aikata da sauransu idan Musulmai ne.

    “Manzon Allah Ya wajabta fitar da zakkar kono ga babba da yaro, ’yantacce da bawa, daga cikin wadanda kuke ciyarwa,” kamar yadda Abdullahi bn Umar ya ruwaito a Hadisi.

    Mai fitar da zakkar zai fara ne da fitar wa kansa, sannan sauran mutanen gwargwadon wajibcin ciyar da su a kansa.

    Adadin da ake fitarwa

    Kowanne mutum ɗaya za a fitar masa da Sa’i ɗaya, wato Mudun Nabi hudu.

    Idan babu Sa’i ko Mudun Nabin awo, ana iya aunawa da tafin hannu.

    Malamai sun ce Mudun Nabi ɗaya daidai yake da cikin tafin hannu biyu na matsakaicin mutum.

    Abin da ake fitarwa

    Ana fitar da zakkar kono ce daga nau’in ɗanyen abincin mutanen garin.

    Ana fitarwa ne daga abin da ya ƙaru a kan abincin rana da yinin mai fitarwa da iyalansa a lokacin.

    Lokacin fitarwa

    Malamai sun bayyana cewa ya halatta a fitar da zakkar tun daga ranar 28 ga Ramadan.

    Hadisi ya nuna, “Abauullahi bn Abbas kan ba da ita da kwana ɗaya ko kwana biyu kafin ranar Sallah.”

    Amma tana wajaba ne daga safiyar ranar Ƙaramar Sallah, a kuma gama kafin Sallar Idi.

    “Wanda ya bayar kafin sallah to zakka ce karɓaɓɓiya, wanda ya bayar bayan sallah kuma to sadaka ya bayar kamar sauran sadakoki.”

    Malamai sun ce haramun ne a jinkirta fitar da da ita ba tare da uzuri ba.

    Waɗanda ake bai wa

    Hadisi ya nuna miskinai ake bai wa.

    Wasu malamai na ganin ana iya ba da ita ga sauran mutanen da ake ba wa zakkar farilla (bayi, matafiya, masu bashi a kansu, masu aikin karbar zakka, masu aikin fisabilillahi, wadanda ake kwadayin su musuluntar).

    Wanda aka ba wa zakkar shi ma zai fitar, idan har an samu ragowa.


    [ad_2]

    Source link

  • NYCN Ta Yi Allah-wadai Da Harin Bam A Maiduguri, Ta Buƙaci Ƙarfafa Matakan Tsaro

    [ad_1]

    Ƙungiyar Matasa ta Ƙasa (NYCN), ta yi Allah-wadai da hare-haren bam da suka afku a birnin Maiduguri na Jihar Borno, waɗanda suka yi sanadin asarar rayuka da lalata dukiyoyin al’umma da dama.

    Ƙungiyar ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, tana mai jaddada cewa bai kamata wani ɗan ƙasa ya rayu cikin fargaba a cikin al’ummarsa ba.

    • Mutum Ɗaya Ya Mutu A Faɗan Daba A Jihar Kano
    • Sojoji Sun Ƙwato Shanun Sata A Filato

    Ta yaba da gaggawar tura jami’an tsaro, tare da kira na a ɗauki matakai masu ɗorewa domin kiyaye sake afkuwar makamantan harin, ciki har da inganta tattara bayanan sirri da tsaron al’umma.

    NYCN ta kuma buƙaci gwamnati ta ƙara ƙaimi tare da ɗaukar matakai masu tsauri da haɗin gwuiwa domin magance matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar nan.

    Haka kuma ta roƙi matasa da su kasance masu natsuwa da sanya ido, da kuma mara wa hukumomin tsaro baya, tare da jaddada aniyarta na bunƙasa zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

    [ad_2]

    Source link

  • Kenya Ta Gudanar Da Taron Bita Domin Karfafa Amfani Da Fasahar Juncao Ta Kasar Sin A Fannin Abinci

    [ad_1]

    An bude wani taron bita kan karfafa amfani da fasahar Juncao ta kasar Sin a fannin abinci, da kawar da fatara, da daukan mataki kan sauyin yanayi jiya Talata a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, wanda ya samu halartar masu tsara manufofi, da masana kimiyya, da manoma da kuma ‘yan kasuwa.

    Ma’aikatar bunkasa aikin gona da kiwo ta kasar Kenya, da sashen kula da shirin muradun ci gaba masu dorewa, watau SDGs, da ke karkashin sashen raya harkokin tattalin arziki da zamantakewa na MDD, watau UNDESA, da jami’ar aikin gona da gandun daji ta Fujian ta kasar Sin, watau FAFU ne suka shirya taron na kwanaki uku.

    Da yake jawabi a taron, babban jami’in reshen kula da tsare-tsare na kasa da inganta kwazon aiki a bangaren shirin SDG na sashen UNDESA Amson Sibanda, ya ce da zarar an fara amfani da ita sosai, fasahar Juncao za ta bunkasa samar da wadatar abinci da juriyar sauyin yanayi tare da kawo kyakkyawan sauyi ga jin dadin rayuwa a Kenya. Ya ce fasahar Juncao wadda masana kimiyya na jami’ar FAFU suka kirkiro, ta zama abar koyi a hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • Mazauna Borno da Yobe sun san waɗanda suka kai hare-haren Maiduguri — CDS

    [ad_1]



    Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya ce mazauna jihohin Borno da Yobe sun san waɗanda ke da hannu a hare-haren ƙunar baƙin wake da aka kai Maiduguri, kuma dole su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar ta’addanci.

    Ya bayyana hakan ne a Maiduguri bayan shi da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, suka koma can bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.

    Wannan na zuwa ne biyo bayan hare-hare a baya-bayan nan da suka yi sanadiyyar mutuwa da jikkata mutane.

    Oluyede, ya ce yawancin maharan ’yan yankin ne kuma ana san su yayin da suke rayuwa cikin mutane.

    Ya bayar da misalin wani hari a Kukawa inda aka gano cewa wasu daga cikin maharan daga garin suke.

    Ya jaddada cewa kawo ƙarshen matsalar na buƙatar haɗin kan jama’a, yana mai kira ga mazauna yankunan su ɗauki alhakin taimaka wa jami’an tsaro.

    Ya kuma ce ’yan ta’addan na amfani da jirage marasa matuƙa da sabbin fasahohi, amma sojoji na ƙara inganta kayan aikinsu domin tunkarar su.

    Hare-haren Boko Haram sun yi ƙamari a baya-bayan nan, inda suke farmakar sojoji da kuma fararen hula.


    [ad_2]

    Source link

  • ‘Yan Wasa 23 Da Eric Chelle Ya Gayyata Domin Buga Wasannin Sada Zumunci

    [ad_1]

    Kocin Super Eagles, Eric Chelle ya gayyaci ‘yan wasa 23 wadanda za su wakilci Nijeriya a wasannin sada zumunta da kasar zata buga da kasashen Iran da Jordan. Kyaftin din tawagar Wilfred Ndidi, Alex Iwobi, da Ademola Lookman suna cikin jerin ‘yan wasan da suka taba wakiltar kasar da aka gayyata.

    Hakazalika Chelle ya kuma gayyaci sauran ‘yan wasa kamar Calvin Bassey, Semi Ajayi, Moses Simon, Samuel Chukwueze, da Akor Adams, daga cikin wadanda basu taba wakiltar kasar ba da aka gayyata akwai dan wasan baya na Rangers Emmanuel Fernandez, Philip Otele, da Yira Collins Sor.

    Masu tsaron raga da suka hada da Maduka Okoye, da Adebayo Adeleye na daga cikin wadanda suka shigo cikin tawagar bayan daukar tsawon lokaci ba tareda an gayyacesu ba, Super Eagles za ta fafata da kasar Iran a birnin Antalya na kasar Turkiyya a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris da misalin karfe 4 na yamma agogon Nijeriya, sannan za su fafata da kasar Jordan a ranar Talata, 31 ga watan na Maris da misalin karfe 8 na dare agogon Nijeriya.

    Ga Cikakken Jerin ‘Yan Wasan:

    Masu Tsaron Raga

    Maduka Okoye (Udinese FC, Italy)

    Adele Adebayo (Volos FC, Girka)

    Francis Uzoho (Omonia FC, Cyprus)

    Masu Tsaron Gida

    Calvin Bassey (Fulham FC, Ingila)

    Oluwasemilogo Ajayi (Hull City, Ingila)

    Bright Osayi-Samuel (Birmingham City, Ingila) Bruno Onyemaechi (Olympiakos, Girka)

    Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal)

    Igoh Ogbu (Slavia Prague, Jamhuriyar Czech)

    Emmanuel Fernandez (Glasgow Rangers, Scotland)

    ‘Yan Wasan Tsakiya

    Alex Iwobi (Fulham FC, Ingila)

    Frank Onyeka (Coventry FC, Ingila)

    Wilfred Ndidi (Besiktas FC, Turkey)

    Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium)

    Fisayo Dele-Bashiru (SS Lazio, Italy)

    ‘Yan Wasan Gaba

    Ademola Lookman (Atletico Madrid, Spain)

    Samuel Chukwueze (Fulham FC, Ingila)

    Simon Moses (Paris FC, Faransa)

    Chidera Ejuke (Sevilla FC, Spain)

    Paul Onuachu (Trabzonspor AS, Turkiyya)

    Akor Adams (Seville FC, Spain)

    Philip Otele (Hamburger SV, Jamus)

    Collins Yira Sor (KRC Genk, Belgium)

    [ad_2]

    Source link

  • Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya

    [ad_1]



    Hukumar Kula da Ganin Wata ta ƙasar Saudiyya, ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ƙasar.

    Hakan na nufin za a azumci ranar Alhamis, inda azumin watan Ramadan na bana za a cike ya zama 30 kenan.

    Don haka ranar Juma’a, 20 ga watan Maris, 2026 ce za ta yi daidai da 1 ga watan Shawwal na shekarar 1447 bayan hijira.

    A kan haka ne hukumar gudanarwar ƙasar Saudiyya, ta umarci jama’ar ƙasar da su cike azuminsu zuwa 30, sannan su yi idi a ranar Juma’a.

    Tun a ranar Talata ne dai wasu masana Ilimin Taurari da Sararin Samaniya suka yi hasashen cewar ba za a ga jinjirin watan Shawwal ba a ranar Laraba ba, har sai zuwa ranar Alhamis.

    Hukumar ta kuma ƙarfafa wa Musulmi gwiwa su yi amfani da sauran lokacin Ramadan wajen yin ibada da ayyukan alheri, tare da roƙon Allah Ya karɓi azuminsu da sauran ibadunsu.


    [ad_2]

    Source link