[ad_1]
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya yafewa fursunoni 12 da aka yankewa hukunci a wani mataki na jin ƙai a cikin watan Ramadan da kuma shirin bikin Sallah.
Sanarwar da Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Bello Fanini, ya fitar ta ce an dauki matakin ne bisa shawarwarin Kwamitin Ba da Afuwa na Jihar Jigawa, da kuma tanadin kundin tsarin mulki na shekarar 1999.
- Gwamnatin Jigawa Na Ƙoƙarin Ganin DSS Ta Saki Walida — Umar Namadi
- Zargi: Yadda Amarya Ta Kashe Mijinta Da Gubar Ɓera A Jigawa
Daga cikin waɗanda aka yi wa afuwar akwai Ibrahim Adamu Isa, Sa’idu Umar, Adamu Musa, Habibu Musa, Yusuf Ahmed, Shu’aibu Adamu, Abdullahi Ya’u, Yahaya Jana’u, Abdul Hamisu, Garba Miko, Salisu Isa da Aliyu Ibrahim.
Gwamnatin ta ce matakin na nuna ƙudirin ta na inganta zaman lafiya, sulhu da kuma haɗin kan al’umma, tare da bai wa waɗanda aka yafewa damar komawa cikin al’umma.
Haka kuma an buƙaci waɗanda aka yi wa afuwar su kasance masu halin kirki, su guji aikata laifi a nan gaba, yayin da aka roƙi al’umma su karɓe su tare da taimaka musu wajen farfaɗo da rayuwarsu.
[ad_2]
Source link