Category: Latest News

  • Sallar Bana: Yadda Al’umma Ke Bukukuwa Cikin Firgicin ‘Yan Ta’adda Da Tsadar Rayuwa A Arewa

    [ad_1]

    Al’ummar yankin Arewacin Nijeriya sun gudanar da bukukuwan Karamar Sallah a bana a cikin yanayi mai cike da kalubale, sakamakon tsananin tsadar rayuwa, firgicin ‘yan ta’adda da kuma fargabar hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi jama’a tare da hana masu bacci da idanu biyu.

    Duk da farin cikin da jama’a ke yi a yayin bukukuwan Sallah a kowace shekara, a wannan shekarar 2026, shagulgulan sun gudana ne cikin yanayi na kunci da takura ta yadda  iyalai da dama suka gudanar da sallah a cikin matsi kamar yadda wasu yankuna suka dakatar da wasu al’adu bisa ga tabarbarewar sha’anin tsaro.

    A lokacin da watan Ramadan na wannan shekarar ya fara a watan Fabrairu, shugabannin addini sun yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nemi taimakon ubangiji dangane da kalubalen tattalin arziki da tsaro da ke addabar kasar nan.

    Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na azumi wajen yin addu’o’i domin samun sauki daga matsalolin da kasa ke fuskanta, tare da rokon zaman lafiya ya wanzu a fadin kasar.

    Sako na nuni da yadda al’ummar Nijeriya da dama ke tunkarar bukukuwan Sallah a cikin yanayi na tsadar rayuwa, talauci da kuma rashin tsaro da ya ta’azzara a Arewa Maso- Gabas, Arewa Maso- Yamma da Arewa ta Tsakya.

    Haka kuma, kungiyoyin kwadago sun bayyana yadda matsin tattalin arziki ke kara tsananta da hana masu walwala kamar yadda kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya da aka fi sani da SSANU ta koka.

    Kungiyar ta nuna damuwa  kan yadda jinkirin biyan albashi ke kara tsananta wahalhalun ma’aikata a lokacin azumi. A cewar kungiyar, dubban ma’aikatan jami’o’i da iyalansu na fuskantar matsin kudi a daidai lokacin da da dama ke gudanar da ibadar azumin Ramadan mai alfarma.

    Wadannan matsaloli sun shafi yadda mutane da dama a Arewa zuwa Kudu suka gudanar da bukukuwan Sallah a karshen Ramadan, inda da dama suka yi bukin cikin sauki ba kamar yadda suka saba ba.

    A jihohin Kano, Katsina,, Zamfara, Katsina, Sakkwato, Kaduna, da Yobe, jama’a sun fito cikin natsuwa domin gudanar da ibada tare da rokon Allah ya kawo karshen matsalolin tsaro da tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

    Sai dai wasu daga cikin mazauna yankin Arewa sun bayyana cewa duk da farin cikin gudanar da Sallah karama, zukatansu na cike da damuwa saboda matsalolin da suka dabaibaye su.

    Daya daga cikin manyan kalubalen da al’umma suka fuskanta a wannan Sallah shi ne tsadar rayuwa. Rahotanni daga kasuwanni daban-daban a jihohin Arewa sun nuna yadda farashin kayayyaki ya yi sama kafin Sallah kamar kuma yadda teloli suka ci karen su ba babbaka.

    Hare- haren ‘yan ta’adda, tashin gwauron zabin man fetur, hauhawar farashin kudin mota daga wannan garin zuwa wancan da rashin tsayayyar wutar lantarki sun haifar da illa sosai wajen hanawa bukukuwan Sallah armashi.

    Kayan abinci kamar shinkafa, mai, nama, kayan miya da kayan marmari sun yi tsada sosai, abin da ya sa iyalai da dama suka kasa shirya liyafa ko hidimar Sallah kamar yadda suka saba a baya.

    A kasuwannin dabbobi kuwa, farashin dabbobi musamman shanu da ake yin watanda ya karu matuka saboda tsadar sufuri da kuma karancin dabbobin da ake kawowa daga wuraren kiyo. Haka ma farashin kaji ya yi tashin gwauron zabi sama sosai lamarin da ya sa iyalai da dama suka hakura da yanka yadda suka saba.

    LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar yadda tufafi suka yi tsada sosai iyalai da dama sun hakura da dinka sababbin tufafi a yayin da wasu suka kasa dinka tufafin yadda suka saba saboda hauhawar farashin tufafin da na kudin dinki.

    Garba Dan Tani ya bayyanawa wakilin mu cewar tsadar tufafi da kayan masarufi sun sa ya kasa sayen sabbin kaya ga ‘ya’yansa kamar yadda ya saba a lokutan Sallah.

    Wata uwa mai suna Hajiya Amina Modi ta ce duk da cewa ta yi kokarin ganin ‘ya’yanta sun kasance cikin farin cikin a yayin Sallah, amma ta yi hakan ne a yanayin takaitawa a abin da ta kira ba yabo ba fallasa.

    A baya, lokacin Sallah kan kasance lokaci na ziyartar ‘yan uwa da abokai a garuruwa da kauyuka daban-daban amma a yanzu, wasu iyalai sun zabi yin Sallah a gidajensu saboda tsoron hare-hare a hanyoyi ko kauyuka.

    Wani mazaunin jihar Zamfara ya ce matsalar tsaro ta sa mutane da yawa sun rage zirga-zirga. “Mutane suna tsoron tafiya saboda matsalar tsaro. A wasu hanyoyi a na jin labarin hare-hare ko satar mutane, don haka mutane sun fi son su zauna a wuraren da suke ganin sun fi samun aminci.”

    Duk da wadannan matsaloli, al’umma da dama sun bayyana cewa Sallah har yanzu lokaci ne na ibada, addu’a da karfafa zumunci. Wasu magidanta sun bayyana cewa duk da tsadar rayuwa, sun yi kokarin faranta ran iyalansu da kananan abubuwa domin su ji dadin wannan rana.

    A yayin da ake daf da Sallah a cikin wata mai tsalki sababbin hare- haren ta’addanci na kunar bakin wake sun tayar da hankalin al’umma a Borno da ke Arewa Maso- Gabas a inda rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 28 da mutane 108 da suka jikkata.

    Yadda ‘yan ta’adda a yankin Arewa suka zafafa ayyukan ta’addanci a cikin watan Ramadan ya kara tsorata jama’a da sanya shakku kan yadda gwamnati da hukumomin tsaro ke fuskantar kalubalen tsaro a kasar nan

    Mummunan harin ya faru ne a lokaci daya a ranar Litinin bayan buda- baki a wurare daban- daban da suka hada da babbar kasuwar Litinin da aka fi sani da “Monday Market” da ofishin aika sakonni na gidan waya da kuma a bakin asibitin koyarwa ta jami’ar Maiduguri.

    Hare- haren mayakan na Boko- Haram sun faru ne bayan da mayakan suka kai wasu munanan hare- hare a sansanonin sojoji da ke Ajari da Baga da kuma Damboa duka a jihar Borno a yayin da sojojin Nijeriya ke kara sabunta ayyukan yakar ‘yan ta’addan.

    Wani mazauni garin, Modu Bukar, wanda ya ga harin da idon sa ya bayyanawa kafafen yada labarai cewar suna zaune kawai suka ji karar fashewa suka kuma fara gudun tsira da rai.

    Haka ma daya daga cikin wadanda harin ya faru a kusa da wajen sa suka yi buda- baki ya bayyanawa manema labarai cewar bayan shan ruwa ne sai kwastam suka ji kara sosai a yayin da wasu mutane ke gudun fanfalaki a cikin jini a yayin da ya ce sun ga mutane da dama ba adadi a cikin jini.

    LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewar mayakan ISWAP sun kashe kwamandojin soja har guda uku a cikin sati daya a bisa ga munanan hare- haren da mayakan ‘yan ta’addan suka kai masu. Rahotanni sun nuna cewar, a yanzu adadin manyan kwamandojin soji bakwai ne suka mutu a sababbin asarar rayukan wadanda suka hada da Birgediya Janar daya da aka kashe watanni uku da suka gabata.

    A watannin baya dai sojoji sun tsananta zazzafan farmaki a wuraren ‘yan bindigar masu hadari da suka hada da dajin Sambisa, Timbuktu, Tuddan Mandara da kuma yankin tafkin Chadi. Sai dai rundunar sojoji ta bayyana cewar ta kashe daruruwan kwamandojin ‘yan ta’addan a yayin da ta matsa lamba wajen fatattakar su.

    Kafafen yada labarai sun bayyana cewar mafi yawan mace- macen sun faru ne a sansanonin sojoji da kuma hare- haren kwanton bauna da hatsabiban mayakan ke kaiwa sojojin da ke fafatukar kakkabe ayyukan ta’addanci a yankin.

    A bisa ga hare- haren Shugaban Nijeriya, Bola Ahmad Tinubu ya umurci manyan hafsoshin hukumomin tsaro da su koma birnin Maiduguri da zama domin fuskantar ayyukan mayakan gadan- gadan- ba tare da kakkautawa ba.

    Tinubu wanda ya yi Allah- wadai da lamarin a jawabin da ya sanyawa hannu a ranar Talata ya bayyana cewar gwamnatinsa ba za ta zuba idanu ta na kallon ‘yan ta’adda na cin karen su ba babbaka ba.

    Ya jaddada cewa hare-haren suna nuna alamun rashin karfi da kuma matsananciyar damuwa a tsakanin kungiyoyin ta’addancin, yana mai cewa ci- gaba da hare-haren sojoji ya raunana su matuka.

    A yayin tofa albarkacin bakinsa, jagoran ‘yan adawa a Nijeriya, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana alihini a kan sake ta’azzarar ayyukan ta’addanci a Borno tare da cewar ‘yan Najeriya ba su gamsuwa da kalaman Allah-wadai da gwamnati kan yi bayan an kai hari; abin da suke nema shi ne sakamako, domin sakamako ya fi duk wata magana karfi.

    Ya ce karuwar kashe-kashen sojoji da fararen hula da dan ta’adda ke yi yana dawo da yanayin abubuwan kunci da suka faru a shekarar 2014, lokacin da ayyukan Boko Haram suka fi kamari a Arewa- Maso- Gabas

    Atiku ya bayyana cewar a bayyane yake gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali wajen murkushe ’yan adawa maimakon bayar da kulawar musamman domin magance matsalar tsaro da ke ci-gaba da tsananta. A cewarsa duk da umarnin da aka bayar na murkushe ‘yan ta’addan har yanzu mayakan na ci-gaba da cin karen su ba babbaka.

    A bayyane yake cewa matsalar tsaro ta kara jefa al’umma cikin firgici, musamman bayan wasu sabbin hare-haren ta’addanci da suka faru a ‘yan watannin nan. A farkon shekarar nan, wasu ‘yan ta’adda sun kai munanan hare-hare a wasu kauyuka na jihar Kwara, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.

    Rahotanni sun nuna cewa daruruwan ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan kauyukan, inda suka kona gidaje tare da sace mutane da dama lamarin da ya sanya tsoro da zullimi ga mazauna yankin.

    Haka ma a karshen mako, kwana daya gabanin harin ta’addancin a Maiduguri sabbin hare-haren da ake dangantawa da mayakan Bello Turji sun yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu tare da tilastawa mazauna garin Bargaja da ke karamar hukumar Isa a jihar Sakkwato tserewa daga gidajensu.

    Wasu mazauna yankin da suka yi magana kan lamarin sun ce harin wanda ya faru a karshen mako, ya jefa al’umma cikin firgici, inda iyalai da dama musamman mata da yara suka nemi mafaka a wasu wuraren.

    A kodayaushe masu sharhi kan al’amuran tsaro kan bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen magance matsalar tsaro a yankin Arewa, sai dai har yanzu lamarin na ci-gaba da ta’azzara.

    A ra’ayin mabambantan jama’a, idan aka samu ingantaccen tsaro, manoma da makiyaya za su iya komawa gonakinsu da wuraren kiwo, wanda hakan zai taimaka wajen kara samar da abinci da rage tsadar kayayyaki

    Al’ummar yankin Arewa dai na ci- gaba da fatan ganin an samu zaman lafiya da saukin rayuwa domin bukukuwan Sallah su dawo cikin walwala da annashuwa kamar yadda aka saba a baya.

    [ad_2]

    Source link

  • Sai ranar Asabar za a yi Sallah a Iran

    [ad_1]



    Gwamnatin Iran ta sanar da cewa sai a gobe Asabar ce za a gudanar da Idin Sallah ƙarama a ƙasar da mafi rinjayen musulmanta mabiya shi’a ne.

    A cewar gidan talabijin na ƙasar, ofishin jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya bayyana cewa yau Juma’a ce za ta kasance rana ta 30 ga watan Ramadan bayan hukuncin da masu duban wata na ƙasar suka tabbatar.

    Sanarwar ta kuma yi daidai da ta ƙasar Iraƙi, inda babban malamin Shi’a, Ayatollah Ali al-Sistani, ya amince da Asabar a matsayin ranar sallah.

    A bana, ƙarshen watan Ramadan a ƙasar ya zo daidai da bikin Nowruz, wato sabuwar shekarar gargajiya da ake yi a Iran.

    Ana tantance ranar Sallah ne bisa ganin jinjirin wata kamar yadda tsarin kalandar Musulunci ya tanada, yayin da ake gudanar da azumi wanda ke daga cikin rukunan addinin Musulunci.


    [ad_2]

    Source link

  • Karamar Sallah: Sallar Idi A Wajen Musulmi…

    [ad_1]

    Da sunan Allah mai Rahama mai Jin ƙai. Yabo da godiya da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah Shi kaɗai. Yabon Allah da amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, shugaban na farko da na ƙarshe tare alayensa da sahabbansa baki ɗaya.

    Bayan haka; wannan rubutu ya ƙunshi bayani akan Sallar Idi a bisa fahimtar Mazhabar Malikiyya. Ga bayanin kamar haka.

    • Yadda Sheikh Musa Lukuwa Ya Jagoranci Sallar Idi A Sakkwato
    • Abubuwan Da Za Su Iya Kawo Cikas Ga Bukukuwan karamar Sallah

    1. Sallar Idi sunna ce mai ƙarfi ta wajibi.

    2. Liman da mamu za su tafi filin idi bayan rana ta fito, domin suna isa filin idi hantsi ya yi, sai a yi salla.

    3. Ana yin Sallar Idi a filin Idi ba a masallaci ba, sai dai idan akwai lalura, to za a iya yi a masallaci, haka nan waɗanda suke a garin Makka za su yi ta ne a Harami.

    4. Mustahabbi ne mutum ya yi wanka domin sallar Idi.

    5. Mustahabbi ne idan an yi wankan a tafi masallaci ba tare da ɓata lokaci ba.

    6. Mustahabbi ne a yi ado a sanya turare da sababbin tufafi ga wanda yake da iko.

    7. Za a tafi filin Idi ana kabarbari a bayyane har a je filin idi, idan an je ba a yin nafila, za a zauna a ci kaba da kabarbari har liman ya ƙaraso, sai a tsaya da kabarbari. Idan liman yana kabarbari , nan ma mamu za su yi kabarbari idan liman ya yi.

    TAMBIHI: Kabarbari aka fi buƙata sama da wa’azi kafin liman ya zo, don Allah a bar al’umma su raya kabarbarbari a Filin Idi.

    8. Sallar idi raka’a biyu ce , kuma ana yin karatu a bayya ne, a raka’a ta farko ana yin kabbara bakwai har da kabbarar harama sai liman ya fara karatu, a ta biyu kuma kabbara shida har da ta mikewa. Ana karanta Fatiha da Sabbi a rakar farko a ta biyu kuma Fatiha da Hal’ataka ko kuma makamantansu.

    9. Idan mutum bai riski wani abu tare da liman da bai kai raka’a ba, to, zai yi kabbara bakwai a raka’a ta farko kafin ya yi karatu, kuma zai kabbara shida a raka’a ta biyu kafin ya fara karatu kamar yadda liman ya yi.

    10. Ba a yin nafila bayan an gama sallar idi.

    11. Liman zai yi huɗuba guda biyu, kuma zai zauna a tsakaninsu, haka nan ana so ya yawaita kabarbari a huɗubarsa.

    12. Ana so a yi sallar layya da wuri akan ta sallar azubi, domin ana so a ci abinci kafin a tafi karamar salla, ita kuma ta layya sai bayan an dawo.

    13. Kabarbari da ake so a yi, laffuzansu suna da yawa kuma za a iya yin kowanne, daga ciki akwai: Allahu Akbar Allahu Akbar La’ilaha illallahu Allahu Akbar Allahu Akbar Walillahil Hamdu.

    14. Ana so a rinƙa kabarbari a bayan kowacce salla ta farilla sau uku bayan salla da kwana uku, kuma ana so a yawaita zikiri a cikinsu.

    15. Mustahabbi ne ga mata da yara idan ba za su je sallar idi ba, to su yi wanka da ado da sanya sababbun kaya idan da hali.

    16. Mata su guji caba ado da sanya turare idan za su idi saboda gudun fitina.

    17. Makruhi ne mutum ya ƙi yin ado da kwalliyya da gayu a ranar idi wai don gudun duniya, idan kuma ya ƙi yi da sunan addini, to ya zama ɗan bidi’a.

    18. Yara da mata za su iya yin wasanni a ranakun idi.

    19. Mustahabbi ne mutum ya sabunta hanya wajen dawo gida, watau ya sauya hanya.

    Allah ya karɓa mana ibadunmu ya gafarta mana. Amin.

    Manazarta:

    1~ Muwadda Maliki (shafi 87-90) bugun Mu’assatul Mukhtãr.
    2~ Almudauwanatul Kubra (1/223-231) ta Imam Malik Riwayatu Imam Sahnun, bugun Maktabatus Saƙãfati Addiniyyati.
    3~ Arrisãlatu (shafi na 71-72) na Abu Zaid Alƙairawãnī,bugun Dãrul Fadīlati.
    4~ Attalƙīnu (shafi na 115-116) na Abdulwahab Albagdadi, bugun Dãrul Fadīlati.
    5~ Alma’ūnatu (1/233-237) na Abdulwahab Albagdadi, bugun Dãrul Fadīlati.
    6~ Alkãfi (shafi na 128-129) na ibnu Abdilbarri, bugun Assahwatu.
    7~ Mukhtasul Khalil (shafi na 87) na Shehu Khalil, bugun Dãru Ibnil Jauzī.
    8~ Sharhul Iziyyati (shafi na 103-106) na Sharnūbi .
    9~ Fathu Rabbil Bariyyati (shafi n 558-566) na Farfesa Masur Sokoto, bugun Maktabatul Imamil Bukhari.
    10~ Sirãjus Sãliki (1/135-137) na Al’ujali, bugun Dãrul Fikr
    11~ Bulgatus Sãliki (1/175-177) na Ahmad Assãwi, bugun Dãrul Fikr
    13. Assharhu Assagir (1/652-660) na Ahmad Addardir, bugun Dãrul Fadīlati.
    14~ Takribul Murãdi (shafi na 124-128) na Sulaiman Zamfara, bugun Dãrul Ummati.
    15. Jawãhirul Iklil (1/101-104) na Saleh Abdussami’i, marubucin Sharikatul Kudsi.

    Nuhu Ubale Ibrahim
    Abu Razina Paki
    Zul-Hijjah 9.1444H

    [ad_2]

    Source link

  • Yara biyu sun mutu bayan an yi musu allurar rigakafi a Kebbi

    [ad_1]



    Gwamnatin Kebbi ta kafa wani kwamiti na musamman domin binciko musabbabin rasuwar wasu yara ƙanana biyu da aka yi wa allurar rigakafi a Babban Asibitin Zuru da ke jihar.

    Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jiha ya sanya wa hannu, wadda aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis, ta ce gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris, ne ya amince da kafa kwamitin.

    A cewar sanarwar, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jiha, Alhaji Yakubu Ahmed BK ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Kwamishinan Lafiya, Alhaji Sama’ila Augie da Kwamishina Manu Dogondaji za su kasance mambobi.

    Haka kuma, Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya, Dakta Zaki Abubakar Zaki, shi ne sakataren kwamitin.

    An ɗora wa kwamitin alhakin gano haƙiƙanin musabbabin mutuwar yaran, waɗanda ‘ya’yan mutum ɗaya ne, tare da bincike kan zargin da mahaifinsu ke yi na cewa sakacin likitoci ne ya janyo mutuwar bayan yi musu allurar rigakafin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an bai wa kwamitin wa’adin mako guda ya kammala aikinsa, tare da umarnin fara aiki nan take.

    A nasa ɓangaren, mahaifin yaran ya zargi likitocin asibitin da laifin mutuwar ‘ya’yansa, inda ya buƙaci gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci.

    A halin yanzu, ana jiran sakamakon binciken domin tantance gaskiyar zargin ko akasin haka.


    [ad_2]

    Source link

  • Peng Liyuan Ta Yi Kiran Daukan Matakin Kasashen Duniya Kan Yaki Da Cutar Tarin Fuka

    [ad_1]

    Uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, Peng Liyuan, kuma jakadiyar hukumar lafiya ta duniya (WHO) game da yaki da cutar tarin fuka da ta HIV/AIDS mai karya garkuwar jiki, ta yi kira ga kasashen duniya da su ba da goyon baya, da kuma shiga a dama da su wajen yaki da cutar tarin fuka a duniya.

    A cikin wata sanarwar da aka fitar a rubuce a wani taron da aka yi ta kafar bidiyo domin tunawa da ranar yaki da cutar tarin fuka ta duniya ta WHO a shekarar 2026, Peng ta ce yana da matukar muhimmanci da WHO ta dauki nauyin gudanar da taron ta kafar bidiyo don tattaunawa bisa taken “kasashe ke jagoranta, al’umma ke karfafawa,” domin zai taimaka wajen hada karfi da karfe tsakanin kasashen duniya kan yaki da cutar tarin fuka wadda ta kasance kalubale ga kiwon lafiyar jama’a.

    Peng ta kuma ce, bisa jajircewa wajen cimma kudurin kare lafiyar jama’a da cikar burin kawo karshen annobar tarin fuka, hukumar ta WHO ta yi gagarumin aiki mai inganci, tare da shawo kan karuwar bullar cutar tarin fuka da aka samu a baya-bayan nan a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • An Gudanar Da Dandalin Kafofin Watsa Labarai Na Sin Da Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo A Birnin Kinshasa

    [ad_1]

    An gudanar da dandalin kafofin watsa labarai na Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo a jiya Laraba a birnin Kinshasa, bisa taken “Zamanantarwar kasar Sin da turbar ciyar da janhuriyar dimokaradiyyar Congo gaba: Hada karfi wajen lalubo sabbin hanyoyin cimma gajiya tare, da hadin gwiwar cimma moriyar bai daya,” taron da ya hallara kimanin mutane 250, ciki har da ’yan siyasa, da wakilan kafofin watsa labarai, da jagororin ’yan kasuwa na kasashen biyu.

    Cikin sakonsa ta kafar bidiyo yayin bude dandalin, shugaban kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, Fu Hua, ya ce a bana ake cika shekaru 70 da kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da nahiyar Afirka, kana a banan ne ake bikin shekarar musaya tsakanin al’ummun Sin da na nahiyar Afirka.

    Fu Hua, ya kara da cewa Xinhua zai dauki wannan dandali a matsayin dama ta aiki tare da takwarori na kafofin watsa labarai dake janhuriyar dimokaradiyyar Congo, wajen zurfafa aiwatar da kudurori da shugabannin kasashen biyu suka zayyana.

    A nasa bangare kuwa, mataimakin firaministan janhuriyar dimokaradiyyar Congo, kana ministan ma’aikatar bunkasa tattalin arzikin kasar Daniel Mukoko Samba, cewa ya yi dadaddiyar alakar Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo ta ci gaba da bunkasa, bisa hadin gwiwa da abotar da suke rayawa. Kazalika, hadin gwiwa tsakanin nahiyar Afirka da Sin ta samar da muhimmin tallafi na bunkasa ci gaban nahiyar Afirka. Har ila yau, Mukoko ya ce kafofin watsa labarai suna taka rawar gani wajen cike gibin tuntubar juna, da taimakawa wajen bunkasa fahimtar juna tsakanin al’ummun kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwar Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo. (Saminu Alhassan)

    [ad_2]

    Source link

  • Binciken CGTN: Babban Layin Dogo Na Sin Da Turai Wani Sabon Kuzari Ne Ga Budadden Tattalin Arzikin Duniya

    [ad_1]

    A cikin watanni biyun farko na shekarar 2026, layin dogo na tsakanin Sin da Turai ya gudanar da ayyuka 3,501, tare da jigilar kwantenoni masu tsawon kafa 20, watau TEU guda 352,000, wanda ya nuna karuwar kashi 32 cikin 100 na ayyukan, da kashi 25 cikin 100 na yawan kwantenonin a mizanin shekara-shekara. Wani bincike na jin ra’ayoyin jama’a da tashar CGTN ta gudanar a tsakanin masu amfani da shafin intanet a duniya ya nuna cewa, kashi 88.8 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa layin dogo na tsakanin Sin da Turai ya nuna kwakkwaran kudurin kasar Sin na ci gaba da bude kofa a babban mataki na inganci ga kasashen waje, da kuma sa-kaimi ga bunkasar budadden tattalin arziki a duniya.

    A matsayin muhimmiyar gada ta gudanar da mu’amalar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Asiya da Turai, babban layin dogo na tsakanin Sin da Turai yana takaita tsawon lokacin jigilar kayayyaki zuwa kusan kashi daya bisa ukun na jigilar teku da kuma saukin farashi zuwa kusan kashi 1 bisa 5 a kan na jigilar jiragen sama.

    A cikin binciken, kashi 91.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyi sun yi amannar cewa, layin dogo na tsakanin Sin da Turai ya kara habaka ingancin jigilar kayayyaki ta kasa da kasa, tare da rage tsadar cinikayyar kasa da kasa. Kazalika, kashi 91.8 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyin sun ce, layin dogo na tsakanin Sin da Turai ya samar da wani sabon dandali na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Turai, kana kashi 82.7 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyin sun yi amannar cewa, layin dogon na tsakanin Sin da Turai na ci gaba da sanya wani kuzari mai dorewa ga farfadowar tattalin arzikin duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

    [ad_2]

    Source link

  • Gwamna Zulum Ya Sha Alwashin Kakkaɓe Masu Ba ‘Yan Ta’adda Bayanai

    [ad_1]

    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa mutane ko kungiyoyin da ke ba ‘yan ta’adda mafaka, ko nuna goyon baya, ko kuma ba su bayanai, makiyan jihar ne kuma abokan gaba ne. Ya ce, ƙarshensu ya zo, za a fara farautar su domin su fuskanci cikakken hukuncin doka.

    Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis yayin wani jawabi ga daukacin al’ummar jihar a Maiduguri, inda ya ce ayyukan makiya, zagon kasa ne ga zaman lafiyar da jihar ta samu, kuma ba za a lamunta da ayyukansu ba.

    Zulum ya yi Allah-wadai da sake ta’azzarar matsalar tsaro a wasu sassan jihar, yana mai cewa lamarin “yana da matuƙar tayar da hankali.”

    [ad_2]

    Source link

  • Ana Neman Hankada Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Mummunan Rami In Ji Wakilin Kasar Sin

    [ad_1]

    Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce Sin ta damu matuka da yadda ake neman jefa yankin gabas ta tsakiya cikin mummunan rami. Fu Cong, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin zaman kwamitin tsaron MDD dangane da batun kasar Syria, ya jaddada cewa bai dace a yi watsi da yiwuwar fadadar kalubalen da ake ciki a Syria zuwa sauran sassan yankin ba.

    Jami’in ya kara da cewa, wanzuwar tashin hankali a gabas ta tsakiya ba kawai zai ci gaba da illata rayuwar al’ummun yankin ba ne, har ma zai haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin shiyyar da ma duniya baki daya.

    Daga nan sai Fu ya yi kira da a gaggauta dakatar da bude wuta, da kuma aiwatar da matakan dakile bazuwar yakin, tare da hanzarta komawa teburin tattaunawa da shawarwari. Ya ce kasar Sin a shirye take da ta ci gaba da taka rawar gani, wajen lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya mai ma’ana a yankin. (Saminu Alhassan)

    [ad_2]

    Source link

  • Sallah: Gwamnan Gombe ya buƙaci Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya

    [ad_1]



    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya buƙaci Musulmi da duk ’yan Najeriya su ci gaba da yin addu’a da kuma riƙe darusan da suka koya a watan Ramadan yayin bikin ƙaramar Sallah.

    A sakon taya murna da ya fitar, gwamnan ya ce bai kamata a ɗauki Sallah a matsayin shagali kawai ba, ya buƙaci yi amfani da darusan da aka kowa a Ramadan a rayuwar yau da kullum.

    Ya ce halaye irin tsoron Allah, biyayya da sadaukar da kai ya kamata su ɗora a rayuwar jama’a.

    “Mu yi amfani da darusan Ramadan wajen inganta zaman lafiya, juriya da soyayya a tsakaninmu,” in ji shi.

    Gwamnan ya jaddada muhimmancin ci gaba da addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaban ƙasa, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubale.

    Ya kuma buƙaci ’yan kasa da kada su yanke ƙauna, su haɗa kai tare da ƙarfafa imaninsu.

    Gwamnan ya roƙi al’ummar Gombe da su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai, yana mai cewa zaman lafiya shi ne tushen ci gaba.

    Haka kuma, ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo tashin hankali ba.

    Har ila yau, gwamnan ya gode wa jama’a bisa goyon baya, ya kuma taya Musulmi murnar Sallah tare da yi musu fatan farin ciki da kwanciyar hankali.


    [ad_2]

    Source link