Category: Latest News

  • Abincin Sallah

    [ad_1]

    Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.

    A yau shafin na mu zai koya mana Fried Rice da Kaza da Zobo domin yin abincin Sallah:

    A lokutan bukukuwa kamar Sallah ko taron biki, mutane da yawa suna son shirya abinci mai da di da kuma abin sha mai sanyaya rai. Daga cikin abincin da ake yawan yi akwai Fried Rice da Nama ko Kaza da Zobo ku kunun Aya ko na zaki.

    Kayan hadin fried rice:

    Shinkafa, Karas, Wake koraye (green beans), Albasa, Mai, Gishiri, Kayan yaji kamar Kuri da tiyim, da maggi.

    Yadda ake hadawa:

    Da farko a wanke shinkafa a tafasa ta kadan da gishiri. Bayan haka a soya Albasa a cikin Mai, sai a zuba karas da wake koraye a juya. A zuba kori, Tiyim da Maggi, sannan a zuba shinkafar da aka tafasa a gaureya sosai har ta dadu.

    Yadda ake yin kaza:

    A wanke kaza a zuba Gishiri, Maggi, Kori, Tiyim da Albasa. A tafasa ta kadan, sannan a dora Mai a soya ta har ta soyu.

    Yadda ake yin zobo:

    A wanke ganyen zobo sosai sannan a tafasa shi da ruwa da citta da kanunfari da bawon Abarba tana kara kamshi, amma ba dole bane idan ba bu na ‘yan mintuna. Bayan haka a tace ruwan, a zuba sukari da dan Abarba ko Lemun Tsami domin kara dandano idan ana so za a iya sa Cola ko ire-iren su. A sa shi a firiji domin ya yi sanyi kafin a sha.

    [ad_2]

    Source link

  • Sallah: Sanusi II ya buƙaci Musulmi su ɗore kan kyawawan ɗabi’un da suka koya a Ramadan

    [ad_1]



    Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ɗore kan kyawawan ɗabi’un da suka koya a cikin watan Ramadan.

    Sarkin, ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, jim kaɗan bayan ya jagoranci dubun-dubatar al’umma sallar Idi a filin Idi na Ƙofar Mata da ke birnin Kano.

    A cikin huɗubarsa, Sanusi, ya bayyana cewa azumin watan Ramadan bai tsaya ga barin cin abinci da sha kaɗai ba; ya haɗa da koyar da darusan tausayi, haƙuri, da tallafa wa juna.

    Ya kuma ƙarfafi Musulmi da su ci gaba da kula da marasa galihu, musamman marayu da gajiyayyu.

    Haka kuma, Sarkin ya yi kiran a tsananta addu’o’in neman ɗorewar zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa zaman lafiya shi ne ƙashin bayan kowane irin ci gaba.

    Sarkin ya ƙara da yin addu’ar samun zaman lafiya a duniya da kuma roƙon Allah Ya kawo damina mai albarka, domin manoma su samu amfanin gona mai yawa.

    Daga ƙarshe, ya shawarci iyaye da su jajirce wajen lura da tarbiyyar yaransu, inda ya bayyana cewa ingantacciyar tarbiyya ita ce ginshiƙin gina al’umma ta gari.

    Manyan jami’an gwamnati, ciki har da Gwamnan Jihar Kano, suna daga cikin sahun farko na waɗanda suka halarci sallar.


    [ad_2]

    Source link

  • GORON JUMA’A

    [ad_1]

    Jama’a barkanmu da kasancewa a wannan rana ta juma’a, barkanmu da ibada, fatan kowa zai sha ruwa lafiya Allah ya karbi ibadunmu amin.    Kamar kowane mako shafin GORON JUMA’A shafi ne da ya saba karbar sakonnin gaishe-gaishenku zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa, da na nesa, har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba.    A yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishenku da kuka aiko mana kamar haka:

    Sako daga Aminu I.B daga Gezawa:

    Ina gaida mahaifina da mahaifiyata Karimatu, ina gaida kanne na Yusufu, isma’ilu, Lauratu, Aisha, Amina da yayana Zainuddin. Ina gaida abokaina na makarantar Malam  Kallamu me allo kamar su; Idirisu, Dahiru, Ubaidullahi, da dai saurans, fatan sun yi juma’a lafiya. Ina gaida ‘yan garinmu gabadaya, Allah kuma ya karbi ibadunmu, Amin.

    Sako daga Umar Lawan Jihar Katsina:

    Ina gaida masoyiyata abar kaunata, rabin raina Maryama, sako na gaba ina gaida Amir Yellow, da Hafiz a ci a zauna lafiya, ina gaida mainasara Kabeer dan fulani, ina gaida kannena da ‘yan’uwana da duk abokaina da suke ko’ina, duk ina gaishe su da fatan sun yi juma’a lafiya, da fatan kuma sun sha ruwa lafiya.

    Sako daga Alaja Habiba Abdulmajid Jihar Kano:

    Gaisuwar goron Juma’a zuwa ga mahaifiyata da kuma mahaifina, da fatan sun yi juma’a lafiya. Ina gaida kawayena kamar su; Mufida, takwarata Habiba, Zeenat, Munira, Amira, Fatima, Zainab Zeey Baby, Fa’iza, Amiran Mama, Zarah ‘Yar Chakaras, Salma Beauty, da dai sauransu da fatan kowacce ta yi juma’a lafiya.

    Sako daga Aminu Shu’aibu Gidan Kaji Jahun:

    Ina gaishe da yayana Buhari, Tijjani da Aisha da Zainab, Musa, da Yusuf, da abokina Audu. Ina gaida Awaisu, Abdulsalam, Yawale, da Kalis, da kanwata Shahida, da Baba Ado, da Baba Al’a, da Baba Sabo, da Halle, da Muzambilu, da Kamilu, da Gambo, da Baban kifi, da Sulaiman, Baban Yaya, da fatan sun yi juma’a lafiya, kuma za su sha ruwa lafiya.

    Sako daga Habib Ahmad, Jihar Kano Unguwar Goron Dutse:

    Ina gaishe da ‘Yan’uwana da ke garin Jos, irinsu Kalisat, Ummussalama, khadijatu, Auwal, Isuhu da sauransu. Sannan ina gaishe da Malamina Malam Muttaka da kuma Baballe abokina, ina gaishe da ‘Yan kungiyarmu ta ball, da fatan sun yi juma’a lafiya.

    Sako daga Usman Bello Dikko daga Jihar Katsina:

    Ina gaida Hajiyata, Mamana kenan Haj. Karima, kowa ya bar gida, gida ya barshi, sai mahaifina Alh. Bello, sai kannena da abokaina, irinsu, Yahaya ikon Allah, su Idris Shettima, Dan Maraya Musa, Lukman a zauna lafiya, ina gaida matata Hafsat Bebin bebi, ina gaida ‘Yan’uwanta da kannenta gabadaya, da fatan sun yi juma’a lafiya.

    Sako daga Al’amin Shehu Jihar Kaduna:

    Assalam. Ina gaida Mahaifana, ina gaida sauran ‘Yan’uwana, da abokan karatuna wadanda na jima ban gansu ba, da wadanda ma muke haduwa har yanzu, ina gaida Ummi da Mami, da Fati, ina gaida Abdulkareem, Idris dan baiwa, ina gaida, Alhaji Ali mazan duniya, ina gaida sauran al’umma gaba daya da fatan kowa yayi sallar juma’a lafiya.

    Sako daga Gimbiya Aishat Sa’id Jihar Bauchi:

    Gaisuwar goron juma’a zuwa ga ‘yan’uwa musulmi, da fatan sun yi juma’a lafiya. Ina gaida Zakiya da Haj.Mero, da Haj. Marka, da Haj. Sa’adatu me tuwon shinkafa, ina gaida Maryamu Isah, ina gaida Dijen Malan Aminu, da Hidayatu Ibrahim, ina gaida Abubakar Mustapha, Arabian kingboi, Muhd Kalgo, Mika’il Adam, da sauransu. Da fatan kowa ya yi Juma’a lafiya.

    [ad_2]

    Source link

  • Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin

    [ad_1]

    Alhamdulillahi… kamar yadda muka ga farkon watan Ramadan, Malamai suka yi ta fassara littafin Allah mai girma daidai gwargwadon fahimtarsu, wanda ya aiko fiyayyen Annabinsa, Annabi Muhammad SAW da shi zuwa ga bayinsa, don ya sanar da su ilimin farko da na karshe, ilimin sama da na kasa, ilimin abinda ya bayyana da wanda ya buya, ilimin sanin halittar ubangiji tun daga farkonta har zuwa karshenta, yau Allah ya nuna mana karshen watan lafiya, muna fata ya yafe mana kura-kuranmu, ya karbi addu’o’inmu, ya nuna mana na badin-badada.

    Wannan makon, shafin namu mai albarka, tsakuro mana wasu ilimai da fahimtoci na zamani ya yi, wanda ya dace al’ummar musulmi da kowa ma baki daya ya sani a wannan zamanin.

    Ga wasu da muka tsakuro muku:

    Duk Abin da ya zo A Alkur’ani, Ilimi Ne Mai Girma Ba Wasa Ba

    Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) ya yi kira ga al’ummar musulmi da su rungumi bincike acikin addini, sannan su yi watsi da rikicin akida.

    Duba da hakan, Mai Diwani ya lura cewa, Alkur’ani yana dauke da ayoyi fiye da 6,000 amma ayoyin shari’a (Muhkamatu), ba su wuce 200 da wani abu ba, sauran duk bayanin ilimai da halitta suke yi.

    Mu yi koyi da Annabi Ibrahim (AS) a bangaren neman ilimi, inda yake cewa, “rabbi arini kaifa tuhyil mauta – ya ubangiji, nuna min yadda kake raya halitta”, ma’ana, neman ilimi sai da tambaya.

    Alhamdulillahi, wannan itace dabi’ar Sufanci – Tambaya a ilimi don neman sani, amma tsarin Malaman baya dake cewa, yin tambaya a ilimi neman tayar da husuma ce, wannan ba daidai ba ne.

    Ubangiji tabaraka wata’ala, ya nemi Annabi SAW da ya roki karin ilimi, “wa kurrabi zidni ilma – kace, ya Ubangiji kara min ilimi”, sabida ilimin littafinsa yana da yawa da fadi, wani an fahimce shi a zamanin saukarsa, wani kuma za a cigaba da fahimtarsa ne da sauyawan zamani, don haka, duk abin da ya sauka a Alkur’ani sai ya tabbata, ko dai a zamanin Annabi SAW ko a bayansa, da fadin Ubangiji cewa, “la tuharrik bihi lisanaka lita’ajala bihi, inna alaina jam’ahu wa kur’anah”.

    Wasu sun bautawa shaidan don kwaikwayon halinsa don samun ilimi, kuma sun samu ilimin mai kyau da mara kyau, don haka, Mai Diwani ya yi kira ga kowa da kowa da ya yi kokari a kan hanyar Allah don samun ilimi mai zurfi.

    Kimiyya da fasahar zamani (Technology) ya wayar mana da kai, akan bin Alkur’aninmu.

    Tsarin duniya, yana sauyawa, misali a kusa-kusa, daga 2018/2019, zuwa 2025, sannan 2026 ta zo da nata sabon tsarin, duba da tsarukan da gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ke aiwatarwa, wanda ke shirin mayar da duniya tsarin jari hujja da barazanar karfin soji.

    Da wannan, ya dace mu koma sabon tsarin da za a tafi a kai, (Alkur’ani), tsarin karatun musulmi ba tafiyar su ba.

    Allah Ya Hore Wa Annabi SAW Ilimin Sama Da Na Kasa A Alkur’ani

    A rana ta uku, tafsirin ya ci gaba cikin tsari da zurfin ilimi kamar yadda aka fara tun ranar farko da ta biyu.

    Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) ya ci gaba da tafsiri a cikin Suratun-Naml, inda ya jaddada muhimmancin sabunta fahimtar addini daidai da zamani, yana mai cewa wannan sabuntawa ita ce hanyar da za ta kawo ci gaba ga duniya da kuma al’ummar Musulmi baki ɗaya.

    Girman Annabi SAW da Mu’ujizarsa,

    Shehun malamin ya yi bayani mai zurfi kan girman Annabi SAW zahiri da badini, inda ya kawo ilgazai da dalilai masu yawa kan bãdinin Annabi SAW. Ya bayyana cewa babbar Mu’ujizar Annabi SAW ita ce Alkur’ani, wanda Allah ya hore masa dukkan halitta da dukkan ilimin duniya—na kasa da na sama.

    Sheikh Mai Diwani ya yi kira ga masu bincike daga Turai da sauran al’umma da su zurfafa bincike domin gano kalimomin ilimin Allah da ke cikin Alkur’ani. A nan ne ya yi karin haske cewa, duk Mu’ujizozin Annabawa da suka gabata, duk da girmansu amma suna bayan Mu’ujizar Annabi SAW.

    Misalai daga Annabawa:

    Annabi Nuhu (AS): An kawo tarihinsa da Mu’ujizozinsa masu girma, amma an jaddada cewa duk suna bayan Annabi SAW.

    Annabi Ibrahim (AS): An bayyana cewa ya zo da ilimi a matsayin hujja; ya fara gano ilimai daban-daban, ya fahimci tafiyar duniya da amfanarta, Allah Ya sanar da shi Ilmul-Yakin, Ainul-Yakin da Hakkul-Yakin, har ya zama mai cikakken yakini. Duk da wannan matsayi, Annabi SAW shi ne jagoransa.

    Annabi Musa (AS): Allah Ya ba shi himma wajen tsarin noma da kiwo na zamani, da ’yanci daga Fir’auna—amma a iyakar mutanensa. Amma Annabi SAW ya ba Larabawa karfi, ’yanci da hadin kai, har suka mallaki duniya da kyakkyawar dabi’a—wadda ita ce babbar ni’ima da Allah Ya ba shi. Wannan dabi’ar ce Annabi SAW ya rayu da ita tsawon shekaru 40 kafin a aike shi zuwa ga halitta baki daya.

    Annabi Isa (AS): An yi bayani kan saukin shari’arsa, inda ya halatta wa mutanensa wasu abubuwa da aka haramta wa mutanen Annabi Musa (AS).

    A yin kira ga Sauki da Hikima, Mai Diwani ya yi kira ga Musulmi da su rika kira ga abubuwa masu sauki da tausasawa ga al’umma, inda ya ce,

    “Ba dole a addini.” Da kuma ayar da ke magana kan yaki har sai an yi imani—inda ya jaddada cewa a wannan zamani, Allah ne Mai rarrabewa, shi ne masani kuma Mai iko a kan komai, kuma hikima da adalci su ne mafita.

    Da Ilimin Lissafi Aka Bankado Gaibu Har Ta Zama A Bayyane, Komai Zai Yiwu

    Mai Diwani, ya cigaba da kwararo karatu, inda ya bayyana cewa, duk wanda ya san falsafa, dole ya yarda da Allah, domin akwai wani abu da ya fi karfin danAdam. Allah bai halicci danAdam domin ya boye masa komai daga gaibu ba. Ya kara da cewa, babbar surar da ta yi magana a kan gaibu, ita ce Suratul Jinn, inda Allah ya bayyana cewa yana sanar da wanda ya yarda da shi daga cikin manzanni domin su isar da sakonsa ga jama’a. Komai na Ubangiji a lissafe yake don shi ne mai kiyaye lissafin komai.

    Shehu Mai Diwani ya kawo misalai na wasu da Allah ya sanar da su wasu abubuwa na gaibu (boye), kamar masana kimiyya ko likitoci da kan gano abubuwan da suke a boye ba a bayyane ba, kuma daga baya hakan ya tabbata. Ya yi kira ga wadanda ba su fahimci ilimin gaibu ba da su guji magana a kan al’amuransa , domin komai yana cikin ilimin Allah, sai dai kaine baka sani ba.

    Shehin ya jaddada cewa, kowace kasa idan ta kula da bangaren ilimi da kimiyya da fasaha (science and technology), za ta samu ci gaba a fannoni da dama ciki har da noma da kasuwanci, har ta kai ga sayar da fasahar. Ya ambato maganar Shehu Ibrahim (RTA) cewa idan aka ce malami, ba wai malamin addini kadai ake nufi ba, domin malami shi ne duk wanda ya san wani ilimi daga ilimin Allah da zai kawo ci gaba da wayewa ga al’umma.

    Shehin ya kara da cewa, yawancin sauye-sauye da aka samu a fannin fikihu da tafiyar da addini, sun faru ne a zamanin daular Abbasiyya, wadanda suka hada mulki da addini, ba kamar yadda Umawiyawa suka yi ba, duk da cewa su ne suka fara kafa siyasa ta karfi.

    Ya bayyana cewa, duk ilimin turawa wani bangare ne dake cikin tulin ilimin Ummul Kitab. Don haka, Mai Diwani ya yi kira da a kawar da kabilanci da wariyar launin fata, wanda yace, Isr@’1la, itace kasar da tafi nuna wariya, don haka ta rasa kasa mallakin kanta, sai dai tsilla-tsilla.

    An kuma yi bayani cewa Annabi (SAW) shi ne ya rufe annabta bayan ya cika kyawawan dabi’u, ya kawo sauyi da ci gaba a rayuwar al’umma, ya yaki kabilanci, bokanci da karya. A yanzu babu wahayi sai dai ilhama ga wanda ya bi Allah da gaskiya.

    Sayyidina Ali (KRM) ya ce duk wata bidi’a yawanci daga malamai take fitowa ta hanyar kirkirar abubuwan da ba su da asali a addini.

    An bayyana cewa, Allah ya bai wa Annabi (SAW) Akalul A’ala, ya haskaka zuciyarsa ta hanyar zikiri, salla, tafakkuri da tadabburin Alkur’ani. Allah Ya zabi watan Ramadan domin saukar da Alkur’ani, ciki har da Suratul Fatiha wadda ita ce mabudin alheri da ni’ima.

    Shehu Mai Diwani ya kara da bayanin ma’anar “An’amta Alaihim” da “Maghdubi Alaihim” a cikin Suratul Fatiha, yana mai cewa “An’amta Alaihim” su ne masu kyawawan dabi’u, yayin da “Maghdubi Alaihim” su ne marasa kyawawan dabi’u. Ya jaddada cewa ba a takaita wannan ma’ana ga wata kabila ko addini kadai ba, sai dai halayen mutum ne suke zama mizani.

    [ad_2]

    Source link

  • HOTUNA: Yadda Musulmi ke gudanar da bikin Sallah Ƙarama

    [ad_1]



    A yau Juma’a, 20 ga watan Maris ne musulmi a sassan daban-daban na duniya ke gudanar da bikin sallah ƙarama ko kuma Idu-al-Fitr bayan kammala azumi 30 na watan Ramadan.

    Sai dai tun a jiya Alhamis, wasu ƙasashe da yankuna sun gudanar da tasu sallar bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal tun a ranar Laraba.

    Galibi akan samu banbancin ranakun gudanar da sallar daga ƙasa zuwa ƙasa ko kuma daga wani yanki zuwa wani, kamar yadda ya faru a bana, inda ko a Najeriya duk da sanarwar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ta rashin ganin jinjirin watan a ranar Laraba, wasu yankuna kamar a Jihar Sokoto sun gudanar da sallar Idi a jiya Alhamis.

    Kazalika, a Jamhuriyyar Nijar ma an gudanar da bikin sallar bayan ganin jinjirin watan Shawwal tun a ranar Laraba, kodayake akwai wasu tsiraru da sai a yau ne suka gudanar da nasu bikin sallar bayan saukowa daga Idi.

    Yadda aka yi Sallar Idi a Babban Masallacin reshen sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano.

    📸: Abubakar Muhammad


    Hotuna daga Masallacin Idin Apo da ke Abuja

    📸: Onyekachukwu Obi


    [ad_2]

    Source link

  • Siffofin Bahaushe A Shudadden Zamani Mai Nisa

    [ad_1]

    Idan ba a manta ba, a makonni biyu da suka gabata a wannan shafin, mun ga asalin Kalmar zamantakewa da yadda take a yanzu a kuma magance . Sannan mun ga ma’anar Kalmar zamantakewa, da iren-irenta, haka zalika, mun ga ina ake kira da kasar Hausa a yau? Da yadda tsarin zaman Hausawa yake kama ga bambanci ta fuskar rukuni ko matsayin a zuzuwan al’ummar Hausawa.

    Bahaushe A Jiya

    Idan aka ce jiya ta kasu gida biyu akwai jiya ta nesa da kuma jiya ta kusa . Jiya ta nesa ita ce Jiyan da Bahaushe yake zaune a matsayin maras addini saukakke daga Allah (S.W.A), sai dai addini irin na tsarin zaman ‘yar marina, wato kowa gabansa, ma’ana kowa yana bautar abin da ya ga ya cancanci ya bautawa. Amma a lokacin da addinin musulunci ya zo kasar Hausa da yawa daga cikin Hausawa suka rungume shi a matsayiin addini  sabanin tsarin da suka taso suka tsinci  kansu a ciki na bantar dodanni ko gumakansu.

    • Binciken CGTN: Babban Layin Dogo Na Sin Da Turai Wani Sabon Kuzari Ne Ga Budadden Tattalin Arzikin Duniya
    • Kasar Sin: Kashe Shugabanni Da Hare-Hare Kan Fararen Hula A Iran Abu Ne Da Ba Za A Lamunta Ba

    Don haka, wadansu daga cikin su suka guji addinin Musulnci, da wannan ne wadancan bangare da suka karbi Musulunci suke kiran daya bangaren da suna maguzawa a matsayin jam’I amma a daidai ku Bamaguje, wato wanda ya guji addinin musulunci.

    Amma idan muka ce nesa ta kusa ita ce, nesa da Bahaushe ya riga ya  ya karbi addinin musulunci, ya zama riga a gare shi wato, al-adunsa da dabi’unsa mafi akasari sun rikide sun zama na Musulunci.

    Don haka, a nan zamu kasa Hausawa da zamantakewarsu zuwa kashi uku, kamar haka:

    Lokacin zama bai daya

    Hausawa a zamanin Musulunci da maguzanci

    Hausawa a zamanin Musulunci da zamantakewa  da dai-dai kun Maguzawa.

    Hausawa a lokacin zama bai daya. A wancan lokacin zamantakewar Hausawa, Ita ake kira da zamantakewa bai daya tare da Hausawan dauri. A lokacin mutane ne wadanda suka fahimci zamaninsu, sannan suka san kansu. Mutane ne da suka riki  ababan bautarsu da gaskiya a wancan lokacin wanda tasirin hakan ya bayyana ta fuskar riko da addini a lokacin da Musulunci ya zo musu, sukai masa kyakkyawan riko. A wancan  lokacin akwai wadansu abubuwa wadanda Hausawa suka rike, a cikin tsarin zamantakewarsu wadanda su suka saya wa Bahaushe girma da daukaka a tsakanin makwabtansu da sauran kabilu abokan zamansu.

    Manufar  rayuwa ga Bahaushen dauri ita ce a yi rayuwa ingantacciya cikin daraja da kaunar juna da kishin juna da taimakon juna. Bahaushe a wancan lokacin ya rike wadansu abubuwa  muhimmai wadanda su ne gishirin zaman duniya wato a cikin abin da ya shafi al’amuran rayuwarsu.

    Wadannan abubuwan su suka sa rayuwar Bahaushe a da ta yi inganci. Bahaushen jiya mai nisa yana da tattali da  tsansteni da kulawa a al’amuransa na yau da kullum. Don haka ne ma yake  da wani a zancin Magana da yake    cewa kada-ran kada-han ma’ana kada-ka-ki-ci kada-ka cinye-duka, kuma komai zaka yi ka rinka sara-ka-na kallon bakin gatari. Bahaushe ya samu wannan falsafar ce domin shi kansa harshen Hausa a jiya mai nisa , harshe ne da yake cike da azanci da Karin Magana kuma azanci da  karin Magana, suna daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen auna  falsafar al’ummar duniya . Don haka za mu iya cewa, rayuwar Bahaushe a da cike take da falsafa wadda hakan ya kara taimaka masa cimma burace buracen rayuwa da ya sa a gaba.

    Wadannan abubuwan suna daya daga cikin abubuwan da suka taka rawa wajen samun gida ko iyali na gari a cikin zamantakewar Bahaushe a zamanin dauri.

    Siffofin Bahaushe A Zamanin Da Mai Nisa

    Mutum ne mai takatsantsan kamar yadda muka ambata a baya, wannan taka  tsantsan din nasa ya shiga cikin ko wane bangare na rayuwarsa kuma ga neman aure yakan yi tattali dan gudun kada ya shiga tsaka  mai wuya          hakazalika, yana da kulawa wajen harkar iyalinsa da aikinsa da sauran al’umuran yau da kullum. Wadansu daga cikin sifoffin da Bahaushen da ya siffantu da su sun hada: tsare gaskiya da amana a dukkan al’amuransa, da zumunci da kana’a ko dangana da hakuri  game da halin da ya tsinci kansa ko ya tsinci kansa a halin rayuwa. Hakazalika, Bahaushe a da yana kiyaye dukkan wani abin da al’adarsa ta haramta masa ya aikata da kuma kawatawa cikin dukkan abin da al’adarsa ta halatta masa ya aikata, a takaice, za mu iya cewa, Bahaushe mutum ne mai kiyaye shari’a, sannan yana daga cikin siffofin Bahaushen da su ne, da’a ga manya ko jagorori a cikin al’umma.

    Bahaushe mutum ne mai neman na kansa don haka nema yake da wata Karin Magana da take cewa a san mutum a san cinikinsa in ya bari a san ya  daina. Don haka nema Bahaushe yake da sana’o’in gargajiya kamar noma da kiwo da fatauci da kira da saka da jima  da dukanci da sasaka da kuma dori . A da ko ajiya musamman mai nisa za a tarar da Bahaushe  kwarare ne a kan sana’arsa.

    Wata fitacciyar siffa da aka san Bahaushen dauri yake da ita , ita ce jaruntaka . Bahaushen da jarumi ne kuma yana  son jaruntaka, don haka ne ma yake zaune a sarari ba a cikin duhuwa ba,  wanda hakan yana daga cikin siffa ta jarumin mutum don haka Bahaushe bai san lalaci ba, ko ragwanci ko kuma matuwar zuciya ba.

    [ad_2]

    Source link

  • Ministan Tsaron Nijeriya Ya Taya Al’ummar Musulmai Murnar Sallah

    [ad_1]

    Mai Girma Ministan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya taya al’ummar Musulmai murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya da bikin karamar Sallah.

    Ministan ya taya al’ummar Musulai murnar ne tare da jan hankalinsu su dukufa wajen addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar da sanya shugabanni cikin addu’o’insu, domin samun mafita da nasarori kan tarin kalubalan da kasar ke fuskanta.

    • Ana Neman Hankada Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Mummunan Rami In Ji Wakilin Kasar Sin
    • Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Sauya Fasalin Tsarin Tsaro A Yaki Da Ta’addanci

    Sannan ya bukaci su yi addu’oi na musamman kan zaben 2027, wajen samun lafiya a lokaci yi da kuma kammalawa.

    Haka kuma ministan ya jan hankalin al’ummar Musulmai da su yi amfani da darrusan da suka koya a watan Ramadan, kamar hakuri, juriya, kokarin ibadah, taimako, kyauta da sadaka, tausayin juna, jin kai, sadaukarwa da mika wuya ga umarnin Allah a rayuwarsu ta yau da kullum, domin samun nasarori a rayuwa da gamawa da duniya lafiya.

    Kamar yadda ya sha kira da jan hankalin al’ummah kan sha’anin tsaron dukiyoyi da rayukan ‘yan kasa wanda ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, ministan ya bukaci daukacin al’ummar Nijeriya da su yi mai yiwuwa da zage dantse wajen bayar da gudunmawa domin tabbatar da ingantaccen tsaro a kasar.

    A yayin da a nasa bangaren ya maida hankali da jajircewa wajen lalubo bakin zaren da dinke matsalolin tsaron kasar, ya bukaci al’ummar Musulmai da su ci gaba da sanya shi cikin addu’o’insu na yau da kullum, domin ya sami nasara a ayyukan da ya sa a gabansa na tsaron kasar

    Haka zalika, ministan ya yi wa Musulman Nijeriya da Kiristoci godiya kan irin soyayya da kauna da goyon baya da kulawa da addu’o’in da suke yi masa a kullum. Ya ce da yardar Allah zai ci gaba da aiki ba dare ba rana domin samar da tsaron da ake bukata a kasar.


    [ad_2]

    Source link

  • An kwantar da jarumin fina-finan Amurka Chuck Norris a asibiti

    [ad_1]



    Rahotanni na cewa an kwantar da fitaccen jarumin fina-finan faɗa a masana’antar Hollywood ta Amurka, Chuck Norris, a wani asibiti a Jihar Hawaii sakamakon rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

    Bayanai sun ce, an garzaya da jarumin zuwa asibiti ne a tsibirin Kauai cikin gaggawa, sai dai an ce yana cikin yanayi mai kyau duk da rashin lafiyar da yake fuskanta.

    Har yanzu wakilan Norris ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.

    Jarumin, wanda ya cika shekaru 86 a makon da ya gabata, ya yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa da wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda ya nuna yana dambe, yana mai cewa: “Ba na tsufa, sai dai na ƙara ƙarfi.”

    Chuck Norris ya shahara ne bayan soma fitowarsa a fina-finai tun shekarar 1968, sannan ya ƙara yin fice bayan fafatawarsa da fitaccen gwarzon kung-fu, Bruce Lee, a fim ɗin The Way of the Dragon.

    Ana kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jaruman fina-finan faɗa da suka yi tasiri a duniya.


    [ad_2]

    Source link

  • Aikin Zamantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya Zai Rage Wa Kasa Asasar Naira Tiriliyan Daya —Dantsoho

    [ad_1]

    Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta bayyana cewa, aikin zamanantar da Tashoshin Jiragen Ruwan kasar da a yanzu, ake ci gaba da yi da kuma wanzar da tsarin NSW, zai taimaka matuka, wajen rage asarar da kasar ke tabkawa, a duk shekara, wadda ta kai ta kimanin Naira tiriliyan daya, musamman saboda rashin da ake da shi, na kayan aiki na zamani.

    Kazalika, Hukumar ta sanar da cewa, idan wannan tsarin na NSW ya fara aiki  gadan-gadan, a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, zai kara habaka kara samar wa da kasar kudaden shiga, a duk shekara, da suka kai daga kaso 10 zuwa 20, wadanda za su kai ga samun Naira biliyan 600 zuwa Naira tirliyan 1.2.

    • Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Sauya Fasalin Tsarin Tsaro A Yaki Da Ta’addanci
    • Ana Neman Hankada Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Mummunan Rami In Ji Wakilin Kasar Sin

    Sama da samun karin kudaden shiga, tsarin ana kuma sa ran zai kara bunkasa hada-hadar kasuwanci da kuma rage jinjirin da ake samu na safarar kaya daga kaso 35 zuwa kaso 45 a cikin dari tare da kuma rage tsadar hada-hadar da kai ta kaso 25.

    Da yake yin tsokaci kan sauye-sauyen da aka samar a Hukuamr ta NPA, shugabanta na kasa Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana cewa, magance gibin da ake da shi, a bangaren fasahar zamani, a fannnin na sufurin Jiragen Ruwa na kasar, abu ne da ya kasance, banbban ginshiki, na sauye-sauyen da da ake da shi, musamman a karkashin ajandar gwamnatin  shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

    Dantsoho ya kara da cewa, shirin ya zamanantar da Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, hakan zai kara habaka hada-hadar kasuwanci a Tashoshin kasar da kuma yadda ake sauke kayan da aka yo jigilarsu, zuwa tashoshin kasar.

    A cewarsa, gwamnatin tarayya, ce ta kirkiro da aikin sabunta Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, musamman wajen bukatar samar da kayan aiki na zamani, a Tashoshin da ke a Apapa, Tin Can Island, Port Harcourt, Warri da kuma ta Calabar.

    “Babbar manufar shi ne, domin a samar da kayan aiki na zamani da Tashoshin da kuma kara fadada yadda za a rinka sauke kayan a Tashoshin, masu yawan gaske tare da kara bunkasa hada-hadar kasuwanci, a Tashoshin,”.

    Dantsoho ya kara da cewa, aikin zamanantar da Tashoshin, zai taimaka, wajen rage bata lokacin safarar kaya da rage tsadar hada-hadar tare da kuma samar da saukin yin kasuwanci, inda hakan za kara tabbatar da yin gasar kasuwanci, a fadin duniya.

    Shugaban ya bayyana cewa, alamu sun nuna cewa, tuni, aka fara samun ci gaba a fannin na sufurin Jiragen Ruwan kasar, musamman wajen shigo da kaya a zuwa cikin Tashoshin wadanda suka karu daga kaso tan miliyan 45.1 zuwa kaso tan miliyan 103.3, inda kuma saukar Jiragen Ruwa a Tashoshin, ya karu zuwa sama da  4,000.

    Kazalika, kwantainar da ake saukewa a Tashoshin, sun karu zuwa miliyan 1.74 wanda hakan ya nuna a zahiri, an samu karin hauhawan hada-hadar kasuwanci da kuma yawan Jiragen Ruwan da ke fitar da kaya, daga Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.

    Bugu da kari, Dantsoho ya sanar da cewa, yin amfani da kayan aiki wadanda ba na zamani ba, na rage yawan yadda ake gudanar da hada-hada, a Tashoshin, wanda hakan kuma, ke kara haifar da cunkoso, a Tashoshin da kuma kara bata lokacin jigilar Jiragen Ruwan.

    Sai dai, shugaban ya bayyana cewa, aikin na zamanantar da Tashishin, zai taimaka, wajen fadada gudanar ayyuka a Tashoshin da kuma rage bata lokaci.

    Dantsoho ya kara da cewa, kara ingnata kayan aiki da kuma kara habaka gudanar da ayyuka a Tashoshin, hakan zai rage tsada da kuma kara janyo hankali masu zuba jari daga kasashen waje.

    Ya ci gaba da cewa, aikin zamantar da Tashohin, zai kuma taima samar da gudanar da hada-hada, a tsakanin kasashen da ke makwataka da kasar nan kamar irin su,jamhuriyar Benin, Togo da kuma Ghana.

    Shugaban na hukumar ta NPA, ya kuma jaddada mahimmancin daga darajar Tashoshin, wanda ya sanar da cewa, hakan zai kara sanya gudanar da gasa a fannin na shurin Jiragen Ruwan kasar, musamman saboda sauye-sauyen na zamani, da hukumar ta samar.

    A cewarsa, tsarin na NSW an tsara shi ta hanyar yin amfani da kafar zamani, musamman domin a bayar da dama, ga ‘yan kasuwa, yadda za su rinka gabatar da takardunsu na son yin fitar da kaya zuwa waje, ta hanyar gabatar da bukatarsu, a cikin rumbun samun bayanai ba tare da wani bata lokacin jiran hukumomin gwamnatin tarayya ba.

    Dantsoho ya kara da cewa, tsarin na zamani na NSW zai kawar duk wani bata lokaci wajen yin hada-hadar kasuwanci da kuma tabbatar da ana bin ka’ida, wajen gudanar da ayyuka yadda suka kamata, a Tashoshin Jiragen Ruwan.

    Bugu da kari, shugaban ya sanar da cewa, tsarin na zamani zai dakile duk wani kutse na bil’adama da magance almundahar cin hanci da rashawa da kuma dode duk wata kafa, da kudaden shiga na  gwamnti, ke zurarewa.

    Shugaban hukumar ya kuma sanar da cewa,  hakan zai kuma  bayar da damar samun bayanai, a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin wanda hakan zai kara taimaka wa, wajen daukar matakai, a hukumance.

    Hakazalika,  sauye-sauyen, za su kara taimaka wa, wajen kara habaka kudaden shiga ga gwamnati da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasar.

    Dantsoho ya kara da cewa, aikin zamantar da Tashoshin, zai taimaka wajen janyo hankalin masu zuba hannun jari a fannnin tattalin aarzikin kasar, kai tsaye.

    Ya sanar da cewa, alfanun da tsarin na NSW da kuma aikin zamanantar da Tashoshin ke da shi, ya dara maganar kara bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.

    [ad_2]

    Source link

  • Isra’ila ta hana Sallar Idi a Masallacin Qudus karo na farko cikin shekaru 59

    [ad_1]



    A karon farko cikin shekaru 59, ba a ji kiran sallah ba a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke Jerusalem, bayan da hukumomin Isra’ila suka hana masu ibada gudanar da Sallar Eid al-Fitr.

    Rahotanni sun ce babu kowa a harabar masallacin, lamarin da ya saɓa wa yadda dubban masu ibada ke cika shi a irin wannan lokaci na ƙarshen watan Ramadan.

    Matakin ya biyo bayan rufe masallacin mai daɗɗeɗen tarihi a birnin Jerusalem tun daga ranar 28 ga Fabrairu, inda hukumomi suka danganta hakan da yanayin dokar ta-ɓaci sakamakon yaƙin da ke gudana tsakanin Iran da ƙawancen Amurka da Isra’ila.

    Rufewar dai ta shafi muhimman lokutan ibada na Musulmi kamar Juma’ar ƙarshe ta Ramadan da kuma Sallar Idin, haɗi da kwanaki goma na ƙarshen watan mai falala.

    Falasɗinawa sun bayyana damuwa kan hana su shiga masallacin, wanda shi ne al-Qibla ta farko a Musulunci, suna mai cewa an tauye musu ’yancin addini.

    Haka kuma, matakin ya shafi Kiristoci, inda aka dakatar da ibadu a Church of the Holy Sepulchre, ciki har da bukukuwan Easter, wanda ake sa ran dubban masu ibada za su halarta.

    Wannan lamari ya kawo cikas mai girma ga al’ummomin Musulmi da Kirista a Jerusalem, inda aka hana su gudanar da muhimman ibadunsu na shekara.


    [ad_2]

    Source link