Yara biyu sun mutu bayan an yi musu allurar rigakafi a Kebbi

[ad_1]



Gwamnatin Kebbi ta kafa wani kwamiti na musamman domin binciko musabbabin rasuwar wasu yara ƙanana biyu da aka yi wa allurar rigakafi a Babban Asibitin Zuru da ke jihar.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jiha ya sanya wa hannu, wadda aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis, ta ce gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris, ne ya amince da kafa kwamitin.

A cewar sanarwar, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jiha, Alhaji Yakubu Ahmed BK ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Kwamishinan Lafiya, Alhaji Sama’ila Augie da Kwamishina Manu Dogondaji za su kasance mambobi.

Haka kuma, Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya, Dakta Zaki Abubakar Zaki, shi ne sakataren kwamitin.

An ɗora wa kwamitin alhakin gano haƙiƙanin musabbabin mutuwar yaran, waɗanda ‘ya’yan mutum ɗaya ne, tare da bincike kan zargin da mahaifinsu ke yi na cewa sakacin likitoci ne ya janyo mutuwar bayan yi musu allurar rigakafin.

Sanarwar ta ƙara da cewa an bai wa kwamitin wa’adin mako guda ya kammala aikinsa, tare da umarnin fara aiki nan take.

A nasa ɓangaren, mahaifin yaran ya zargi likitocin asibitin da laifin mutuwar ‘ya’yansa, inda ya buƙaci gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci.

A halin yanzu, ana jiran sakamakon binciken domin tantance gaskiyar zargin ko akasin haka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *