Ba Zamu Lamunci Buƙatar Murabus Ɗin Mataimakin Gwamna Ba — Kwankwasiyya

[ad_1]

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta yi Allah-wadai da kiran da aka yi na a sauke Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, tana mai bayyana shi a matsayin abu mai tayar da hankali, da rashin godiya da kuma abin da ba bazu su yarda da shi ba.

Wannan matsaya na ƙungiyar na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Dr. Habibu Saleh Mailemo, ya fitar a ranar Alhamis, biyo bayan rahotannin da ke yawo kan cewa gwamnatin jihar ta buƙaci mataimakin gwamnan ya yi murabus ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida.

  • NNPP Ta Caccaki Gwamna Yusuf Kan Ficewa Daga Jam’iyyar, Ta Ce “Cin Amanar Kano Da Kwankwasiyya Ne”
  • Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Bayyana 23 Ga Janairu A Matsayin Ranar Cin Amana

Kwankwasiyya ta ce ta karɓi rahoton “da matuƙar damuwa,” tana mai cewa irin wannan kira ba shi da hujja kuma na iya barazana ga zaman lafiya da jituwa ta dimokuraɗiyya a jihar. “Wannan kira ba shi da tushe, yana iya tayar da hankali, kuma abin takaici ne ƙwarai. Yana ƙarfafa zargin da ke ƙara yaduwa a zuƙatan al’ummar Kano cewa gwamnatin yanzu ba ta da niyyar tabbatar da ɗorewar  zaman lafiyar siyasa jihar, daidaito na cikin gida da jure ra’ayoyi,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta zargi gwamnatin da yunƙurin warewa da wulaƙanta magoya bayan Jagoranta na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ta ce ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar gwamnatin mai ci. Ta jaddada cewa an zaɓi mataimakin gwamnan ne tare da gwamna a kan tikitin haɗin gwuiwa, don haka ba za a iya tilasta masa barin ofis bisa son rai na wasu mutane a cikin gwamnati ba.

Kwankwasiyya ta kuma ce idan gwamnatin na da wata fahimta ta adalcin siyasa, ya dace ta waiwayi abubuwan da suka faru a zaɓukan 2019 da 2023, inda Jagora Kwankwaso da miliyoyin magoya bayansa suka yi gagarumar sadaukarwa wajen samun nasarar da ta kai Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo zuwa Gidan Gwamnati. Ta ƙara da cewa ba za ta yi shiru ba a kan abin da ta kira cin amanar magoya baya, da tsoratarwa da wulakanta mambobinta masu biyayya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *