Kotu ta ba Yahaya Bello damar tafiya Umara a watan azumi

[ad_1]



Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, izinin tafiya Saudiyya domin yin Umrah a kwanaki 10 na watan Ramadan mai kamawa.

A yayin zaman kotun na ranar Alhamis, alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin a saki fasfo ɗin tafiya na tsohon gwamnan, wanda yake a hannun kotu, na ɗan lokaci domin ya yi tafiyar.

Bello yana fuskantar shari’a a gaban kotun bisa zargin karkatar da kuɗi da Hukumar EFCC ta shigar a kansa.

Buƙatar izinin tafiya Saudiyya domin yin ibada, wadda aka shigar a ranar 20 ga watan Janairu tare da rantsuwar shaidar da Bello ya rubuta da kansa mai sakin layi 24, lauya Joseph Daudu (SAN) ne ya gabatar da ita.

Daudu ya shaida wa kotu cewa buƙatar ta nufin bai wa wanda ake tuhuma damar tafiya Saudiyya domin yin Umrah a watan Ramadan.

Ya ƙara da cewa Bello bai je ƙasar mai tsarki ba fiye da shekaru takwas, kuma akwai buƙatar ya je yanzu domin roƙon Allah ya kubutar da shi daga tuhumar da EFCC ta ke masa.

Lauyan masu gabatar da ƙara, Kemi Pinheiro (SAN), ya ce ba za su yi adawa da buƙatar tafiyar ba, amma ba za su yarda a yi sauyi ga ranakun shari’a da kotu ta riga ta tsara ba.

Da yake yanke kwarya-kwaryar hukunci, Mai Shari’a Emeka Nwite ya amince da buƙatar, inda ya umarci Magatakardar kotun ya saki fasfo ɗin Bello domin ya yi tafiyar Umrah a watan azumin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *