Ba Ni Da Alaƙa Ko Hannu A Ta’addanci – Gwamnan Bauchi
[ad_1]
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana cewa ba ɗan ta’adda ba ne kuma ba shi da wata alaƙa da ta’addanci ko wani laifi.
Gwamnan ya faɗi hakan ne a ranar Laraba a Fadar Gwamnati da ke Bauchi, yayin da yake karɓar lambar yabo ta Award of Excellence a matsayin Jakadan Tsaro daga Cibiyar Tsaro ta Nijeriya (Safety Institute of Nigeria).
- Jam’iyyar NNPP Ta Yi Watsi Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Dungurawa A Kano
- Dubu 100 Aka Biya Ni Na Sanya Bam A Masallaci A Borno — Ɗan Ƙunar Baƙin Wake
Ya yi wannan jawabi ne domin mayar da martani ga rahotannin da ke danganta shi da ta’addanci, da kuma ci gaba da tsare Kwamishinan Kuɗi na jihar da Hukumar EFCC ke yi.
Yayin karɓar lambar yabon, Mohammed ya ce, “Na kasance jakadan tsaro. Ban san cewa abu ne mai girma haka ba sai da wannan mai gabatarwa ya yi bayani sosai. Ina matuƙar farin ciki da karɓar wannan lambar yabo a madadin mutanen Jihar Bauchi.”
Ya ƙara da cewa wannan girmamawa ba tasa ce shi kaɗai ba, illa ta mutanen Jihar Bauchi gaba ɗaya.
Gwamnan ya bayyana mamakinsa kan zarge-zargen da ake yi masa, inda ya ce, “Ina farkawa kawai na ga ana zargina da ta’addanci a matsayina na Gwamna.”
Ya kuma koka kan abin da ya kira rashin adalci daga hukumomin tarayya.
A cewarsa, “Ko da yake ina da kariya ta doka a matsayina na Gwamna, an ambaci sunana a wata kotu ta Nijeriya.”
Mohammed ya ce ya daɗe yana yin shiru ne domin tabbatar da zaman lafiya, amma yanzu ba zai ƙara yin shiru ba.
“Na yi shiru na tsawon lokaci. Na yi hakan ne saboda zaman lafiya da tsaro, amma ba matsoraci ba ne,” in ji shi.
Da yake magana kan tsaro da shugabanci, gwamnan ya ce Jihar Bauchi na ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali duk da matsalolin tsaro da ke addabar Arewacin ƙasar.
Ya ce, “Babu wata jiha a Arewa da ta fi Bauchi samun tsaro.”
Gwamnan ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin APC da amfani da hukumomin gwamnati wajen gallaza wa ‘yan adawa.
A cewarsa, “Gwamnatin tarayya ƙarƙashin APC na tunanin za ta iya amfani da kotuna da hukumomin gwamnati kamar EFCC domin muzguna wa ‘yan Nijeriya da ba sa cikin jam’iyyarsu.”
Ya yi gargaɗin cewa ba zai ci gaba da yin shiru ba.
“Ina tabbatar muku, ba za mu ƙara yin shiru ba. Ba zan yadda wani ya mayar da ni mai laifi saboda ban shiga APC ba, kuma ba zan shiga APC ba,” in ji Mohammed.
[ad_2]
Source link