An kama mutum 2 kan zargin shigar da ƙwaya a gidan yari
Jami’an Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da yunkurin safarar miyagun kwayoyi da kuma tabar wiwi a gidan yarin jihar.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da: Usman Khalid mai shekara 25 da Bello Musa Ahmed mai shekara 24 dukkan su maza ne kuma mazauna unguwar Tsamiya (a Breget) a cikin jihar Kano.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gidajen yarin jihar, CSC Musbahu Lawal Kofar-Nassarawa ya fitar, ya ce an kama mutanen ne a lokacin da suke ƙoƙarin shigar da miyagun ƙwayoyin zuwa cikin gidan yarin.
Ya ce, jami’an da ke cibiyar Hukumar a yankin Goron Dutse, Kano ne suka kama waɗanda ake zargin, a lokacin da suke ƙoƙarin shigar da tabar wiwi ga fursunonin a harabar gidan,” in ji shi.
Hukumar ta gargaɗi mutane kan yunkurin shiga cikin fursunoni, musamman lokacin zirga-zirga zuwa kotu, saboda irin barazanar tsaro da hakan ke tattare da shi, kuma yin hakan akwai hukunci mai tsauri.