Darasin Da Aka Koya Bayan Kammala Kofin Afirka A Morocco
Gasar cin kofin Nahiyar Afirka da aka kamala a wannan watan za ta kasance gasar da za a dade ana tattaunawa a kanta na tsawon lokaci saboda yadda aka kare gasar cikin wani yanayi na rashin jin dadi.
Hargitsin da aka samu a lokacin da aka kusa tashi daga wasan karshe, lokacin da bugun fenaritin da aka bai wa Moroko ya kai ga cewa ‘yan wasan Senegal sun fice daga filin wasa, zai kasance abin da za a jima ana magana a kai Kociyan tawagar Moroko, Walid Regragui ya bayyana lamarin a matsayin “abin kunya”, amma har yanzu hukumar kwallon kafa ta Afirka ba ta sanar da wani hukunci ba kan lamarin.
- Jakadan Sin: Cudanyar Al’adu Za Ta Taimaki Yunkurin Daidaita Hulda Tsakanin Sin Da Amurka
- Gwamnan Zamfara Ya Yaba Da Gudumawar Ɗan Majalisa Hon. Mai Palace A Bangaren Kiwon Lafiya
Amma kuma rikicin da aka samu a lokacin wasan na karshe bai kamata ya dauke hankulan al’umma daga abubuwa da dama da suka faru a gasar ba, wadda a lokacinta ne aka ci kwallaye mafi yawa.
Babu shakka kasar Moroko ta shirya gasa mai kayatarwa, filayen wasan masu kyau, inda filin wasa na Yarima Moulay Abdellah da ke babban birnin kasar ya zama abin kallo ga bakin da suka je kallon gasar
Karbar bakuncin wannan gasa ta AFCON wani bangare ne na shirye-shiryen kasar na karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2030, inda za ta yi hadin gwiwa da Spain da kuma Portugal. Morocco ta zuba jari sosai a baya-bayan nan tare da goyon bayan Sarki
Mohammed na BI, wanda ya ce kayan da kasar ta samar ya nuna “juriyarta da kuma kwarewa wajen shiri kamar kowace kasa a duniya.
Ana sa ran Morocco za ta kara inganta kayan da ta samar, inda yanzu haka ake shirin yin gyare-gyare ga filin wasa na Mohammed B da ke birnin Casablanca da wasu a biranen Fes da Marrakesh da Agadir – haka nan kuma ake ci gaba da aikin gina filin wasa na Benslimane mai daukar ‘yan kallo dubu dari da sha biyar (115,000).
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Kenya, Hussein Mohammed ya amince cewa Moroko ta “ciri tuta” a batun karbar bakuncin gasar, sannan ya ce Kenya na daukar matakan da suka dace domin samar da kayan aiki masu kyau a gasar 2027. Sai dai har yanzu ba a sanar da takamaiman lokacin da za a buga gasar da Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda za su dauki bakunci ba.
Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta ce kudin da take samu a lokacin gasar sun karu da kimanin kashi 90%, inda kudin tikitin kallon wasa ya taka muhimmiyar rawa, inda ya karu daga dala miliyan 11 a shekarar 2023 a kasar Ibory Coast zuwa dala miliyan 55 a Moroko. Haka nan an samu karin kamfanoni masu daukar nauyi zuwa 23, sannan kuma darajar gasar ta karu sanadiyyar tallata gasar a shafukan sada zumunta. A shekarar da ta gabata hukumar CAF ta yi hasashen samun karin kudaden shiga sama da dala miliyan 114 a lokacin gasar, daga dala miliyan 75 a shekaru biyu da suka gabata.
Daga abubuwa marasa dadi kuwa, an nuna damuwa lokaci zuwa lokaci kan hukunce-hukuncen da alkalan wasa suka zartar. Saboda kafin wasan kusa da na karshe da Nijeriya, ta kai ga cewa har sai da mai horas da Moroko, Walid Regragui ya yi kokarin yayyafa ruwa kan rade-radin da ke cewa alkalan wasa na taimaka wa Moroko.
Babban lamari game da irin wannan takaddama shi ne abin da ya faru a wasan karshe, inda alkalin wasa Jean-Jackues Ndala ya tafiyar da al’amura a tsanake, har sai a kusa da karshen wasan, inda lamurra suka tabarbare cikin kankanin lokaci.
Matakin da alkalin wasan ya dauka na bai wa Moroko bugun fenariti ya sanya wasu sun yi tunanin akwai rashin adalci, lamarin da ya kai ga cewa ‘yan wasa sun fita daga fili.
Amfani da fasahar BAR wajen taimaka wa alkalin wasa a baya-bayan nan ya zamo abu mai rudani, tun bayan amfani da shi da aka yi a 2023.
Sannan kasar Senegal ta nuna damuwa kan rashin tsaro a lokacin da ta isa birnin Rabat, gabanin wasan karshe, inda mutane suka takura su. Sai kuma hatsaniyar da aka samu a cikin filin wasa, inda magoya baya suka yi artabu da jami’an tsaro a lokacin da Moroko ta samu bugun fenariti.
Haka nan an zura ido a ga matakin da hukumar CAF za ta dauka kan abin da ya faru a lokacin da aka ga yaran da ke dakko kwallo a filin wasa na kokarin dauke kyallen mai tsaron raga na Senegal Edouard Mendy.
Sai dai wasu hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda magoya bayan Moroko ke murna lokacin da aka sace kyallen mai tsaron raga na Nijeriya har sau biyu a lokacin karawar kusa da karshe.
Har ila yau, akwai yiwuwar hukumar CAF ta duba yiwuwar sauya wasu dokokinta kan bayar da katin gargadi a matakin kifa-daya kwala.
Jimillar ‘yan wasa 20 ne suka rika taka-tsantsan a matakin wasan kusa da karshe saboda suna jin tsoron cewa da zarar suka samu katin gargadi, hakan zai hana su buga wasan karshe.
Misali shi ne, kyaftin din Senegal, Kalidou Koulibaly da dan wasan tsakiya Habib Diarra sun gaza buga wasan karshe, kuma irin wannan abu ya kusa faruwa da mai tsaron baya na Nijeriya Calbin Bassey da na Masar
Hossam Abdelmaguid, in da tawagoginsu sun kai wasan na karshe.
Sai dai duk da cewa akwai bukatar ganin an tabbatar da da’a a lokacin gasar, amma masu horarwa da ‘yan wasa da kuma magoya baya har ma da kafofin yada labarai za su ga cewa kwararrun ‘yan wasa sun taka rawa a manyan wasanni kuma nan gaba abubuwa masu kyau da aka gani a wannan gasar za su karu a gasar da za a buga a nan gaba.