Gwamna Yusuf Ya Amince Da Sabbin Naɗin Muƙamai Ga Wasu Jami’ai A Kano

[ad_1]

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗi da kuma ƙarin girma a wani mataki da nufin inganta shugabanci da kuma samar da ayyuka a manyan sassan jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

Waɗanda aka naɗa su ne kamar haka:

1. Hon. Abdulkadir Balarabe Kankarofi (Alhajij) – Mai Ba da Shawara Kan Harkokin Jinƙai, a ƙarƙashin ofishin Gwamna.

2. Hajia Aisha Tamburawa – Mai Ba da Shawara ta Musamman ga Gwamna kan al’amuran dattako.

3. Injiniya Mukhtar Yusuf – Shugabn kamfanin Albarkatun Ruwa da Gine-gine (WRECA).

4. Zakari Usman Balan – Mataimakin Shugaban WRECA.

5. Dr. Mukhtar Bello Maisudan – Babban Sakataren Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kano.

6. Injiniya Abba Kankarofi – Babban Daraktan Gudanarwa, Hukumar Kula da Hanyoyi ta jihar Kano (KARMA).

7. Hon. Musayyib Kawu Ungoggo, Manajan Darakta a gidan kula da namun daji (zoo) na Kano.

Gwamna Yusuf ya umarci sabbin jami’an da aka nada da wadanda aka kara wa girma da su yi aiki tukuru don sauke nauyin aikin da aka dora musu ta hanyar sadaukarwa, gaskiya, da jajircewa ga al’ummar Jihar Kano.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *